FARKO

78 5 3
                                    

Kakkarfar iska ce take kaɗawa tare da wani sauti mai mutukar tsoratarwa da gigita mai sauraro, fili ne fetal babu komai a kan dandaryar kasa inka ɗauke wasu dogayen bishiyu wayanda ƙarfin iskar ya sabbaba musu yin rawa da rangaji kamar zasu fadi...

Bayan kananun ciyayi wayanda basu wuce zira'i biyu zuwa uku da suke ta faman fincike kawunansu daga kasa saboda kakkarfar iskar, baza kaga komai ba sai tsirarun mutane wayanda dukkaninsu suke a tsaitsaye kikam kamar gumaka, a tsakiyar wannan fili. Zakaji mamaki idan kaga cewa kewayen inda suke a tsaye ko kadan babu wannan iska, amma yamma kudu da arewa duk iskar ce mai mutuqar razanarwa.

Kamar da bakin kwarya akai wata tsawa gami da walƙiya yayin da lokaci guda kuma duhun dake ilahirin filin ya yaye, a hankali iskar ta fara lafawa yayin da ruwan sama yaci gaba da zuba.

Kamar haɗin baki sai wayannan tsirarun mutanen suka daga hannaye sama suna masu fadin "amsawarka ya cikamakin bokaye...."

"Hahaha" wata katuwar murya ta bayyana a dai dai lokacinda kasar wajen ta fara tsagewa, a hankali kuma sai duhun daya yaye ya ƙara dawowa, bayan wani lokaci sai dariya ta cika filin wadda ana jiyota daga kowane ɓangare na dajin. Bayan duhun ya yaye ne kuma saiga wani jibgegen mutum ya bayyana, babu sitira a jikinsa idan ka dauke wata fata wadda ta kare al'aurarsa.

Fuskarsa buzu-buzu  da gashi, gashin  bakinsa kuwa ya kusa karasowa zuwa kafadarsa.

Baƙi ne, mai tsayi da faɗi jikinsa a mummurɗe yake, idan ka tambayi wanda ya ganshi cewa da shi da giwa wanene yafi girma to tabbas ba zai iya banbance maka ba.

Bayyanarsa keda wuya, wayannan mutane suka zube kasa suna masu sujjada yayin da jikinsu yake kyarma, kai da ka gansu kasan a tsorace suke.

"Hahaha," mutumin ya bushe da dariya, "An gaishe da amintattun bayi, nasan abin da ke tafe daku. Kunzo tambayar wanda za a yanka idan lokacin yanka yazo ko?"

Cikin hanzari dukansu suka dago daga sujjadar da sukai suna masu gyaɗa kawunansu alamun sun yarda da abin da yace.

Filin yayi tsit, aka rasa wanda zaice wani abu, daga nan wannan jibgegen mutum ya kara kyalkyalewa da dariya. Daga bisani ya fara da yiwa kansa kirari

Nine Boka Lahan uban matsiyata..
Gugan karfe sha kwaramniya ta mazaje
Boka nake, dan boka jikan boka kuma uban boka.....
Daga nan, boka lahan ya sake bushewa da dariya mai kama da tsawa ko rugugin aradu..

Sannan yayi shiru, daga bisani yace "Akwai wani dattijo a bayan alkaryar Sirnas nesa kaɗan da al'umma, ya dogara ga noma da kiwo. Akwai yarsa mai suna Dije, wannan karon abin bauta ita yake bukatar a shayar da shi jininta....... kuyi sani cewa rashin cika umarnin abin bauta zai haifar muku da tashin hankalin da saikun gwammace ku yanka yayanku da dukkanin dabbobin da kuka mallaka.......", yana zuwa nan a zancensa ya bushe da dariya gami da bacewa bat.

Ko gezau babu wanda yayi suna tsaye kamar daga sama sukaji an kara daka musu tsawa...... "Kaiiii me kuke jira ne? Mun sallameku kuma mun baku nan da wata daya don bijiro da ita a yankata....."

Ƙaƙa ƙara ƙaƙa, ana wata ga wata...
Don jin wannan ƙayataccen labari sai a kasance tare da mu.
Shin za a yanka wannan abin yanka ga abin bauta? Ko kuwa akwai hanyar tsira?

Karku damu abu biyu kawai muke buƙata, comments da kuma vote.

ƘARFIN SOYAYYA (Completed, 2020)Where stories live. Discover now