Shirin Ceto...

17 2 0
                                    

Dakaru suka kama Ilfar suka nufi gidan sarautar dashi, tare da Nasir.

Shi Ilfar shine babban mai laifi, shi kuwa Nasir tare da cewa shine mai karamin laifi amma laifinsa yafi girma a wajensu domin yayi cece-kuce da boka Lahan, wanda hakan ba karamin lahani zai janyowa gaba daya alkaryar ba.

Saboda fushi, sarki mahaifin Gundas ko bukatar ganinsu Nasir bai yi ba. Ana tabbatar masa da an kamasu sai yace kawai aje a ajiyesu kurkuku.

Cikin dare Gundas yaje wannan kurkukun ya bukaci da'a bude su Ilfar. Amma sai dakaru masu tsaron kurkukun sukai masa taurin kai, cikin lumana yayi musu magiya amma suka nuna masa cewa umarnin mahaifinsa suke bi ba nasa ba.

Ai kuwa take Gundas ya fusata cikin wani yanayi na harzuka ya zare takobinsa ya sare kan shugaban dakarun sannan ya tirsasawa ragowar dakarun suka bude masa su ilfar da Nasir. Cikin kankanin lokaci yasa aka shirya dawakai guda uku kowannensu ya hau guda ba tare da yace musu uffan ba kawai ya saki linzamin dokinsa ya sukwaneshi... Ai kuwa sai Ilfar ya mara masa baya. Jim kadan Nasir ya tsaya yana tunani, sai kawai ya yanke shawarar shima bari yabi bayansu. Ai kuwa ya sukwani dokinsa yabi bayansu.

Haka suka wanzo suna gudu da dawakai cikin dare har suka fita daga gari. Suka sake daukar hanya suka nausa cikin daji, dukkaninsu suna masu bin bayan Gundas, saidai suka shude sa'a guda suna tafiya sannan Gundas yaja linzamin dokinsa ya tsaya, domin yayi wata tirjiya yayi haniniya ya daga kafafuwansa ya buga a kasa. Kamar hadin baki dokin Nasir da Ilfar suma sai suka tsaya.

Gundas ya kalli Nasir da Ilfar daga bisani yayi wani murmushi wanda bazaka iya tantancewa murmushin menene ba. Daga bisani ya fara da cewa “Dukkaninmu muna son mutum daya, kuma rayuwarta tana cikin hatsari wanda salwantar ranta shine yafi komai sauki......” yayi shiru yana mai nazarin fuskar abokanan takarar tasa.

Yaci gaba da cewa “Idan har mun cika masoya dole mu kwato mata yancinta, mu ceto rayuwarta daga wannan kangi da take ciki.....”

Nasir ya gyada kai alamar ya gamsu yayinda shi kumaa Ilfar yake wasa da linzamin dokinsa......

“Don haka nake ganin kamata yayi mu ukun mu hadu waje guda don hada karfi da karfe wajen ceto rayuwarta, idan yaso bayan mun tseratar da ita wanda yayi saura a cikinmu sai ya zama abokin rayuwarta, domin shiga dajin bahaguwar fahimta ba karamin aiki bane, ta iya yiwuwa mu rasa rayuwarmu baki daya” Gundas ne ya fadi hakan.

“Shawarace mai kyau” Nasir ya fada yana mai murmushi.

“Bana bukatar taimakonku ko kadan” Ilfar ya ambata, “ni kadai zan iya zuwa in ceto rayuwarta”.

“Munsan zaka iya” Nasir ya ambata yana mai kallon Ilfar cike da mamaki sannan ya cigaba da cewa “abinda muke bukata yanzu shine hadin kanmu, don kuwa hadin kanmu zai bamu damar yakar Lahan cikin sauki”.

“Bana tunanin ko gawata akwai abinda malalacin namiji irinka zai iya taimakonta dashi” Ilfar ya fada yana mai murmushin keta ga Nasir. “amma zan tafi tare daku domin a tafiyar zaku gane bambanci tsakanin ni da ku”

Kawo i wannan lokaci Gundas kawai kallon ilfar yake yana mai cike da mamaki.

Daga nan suka ci gaba da magana akan tafiyar tasu. Inda a karshe suka dauki alkawarin taimakawa juna komai ruwa komai rintsi. Duk da dai sunsha wahala kafin Ilfar ya yarda da taimakekeniya tsakaninsu.

“Muyi maza mu bar wajen nan don nasan za a biyo bayan mu” Nasir ya ambata.

“Dakaru ba zasu biyo muba har sai sun nemi izini daga mahaifina” Gundas ya fada “kuma a dokar mahaifina ba'a shiga wajensa da daddare komai girman abu kuwa, domin ana katse masa ayyukansa a halwar tsafinsa.”

Nan suka cigaba da shirya yanda zasuyi tafiyar har bacci ya daukesu. Bayan sunci abincin guzurin dake dauke a dawakansu.

Zamu dakata anan, me kuke tunani?
Muje zuwa a rubutu na gaba.

ƘARFIN SOYAYYA (Completed, 2020)Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu