Kwanakin fargaba

30 3 0
                                    

Tun bayan faɗuwar Dije sakamakon jin ambatar sunanta da akai a matsayin abin yanka ga abin bauta, bata tsince kanta a ko ina ba sai a ɗakin mahaifiyarta wadda take kanta a zaune tana mata fifita.

“Baba, ki gayawa babana mu tattara kayanmu mubar wannan A
alƙarya...”  Dije ta faɗa cikin sanyin murya, tana mai share hawayen da yake zubowa daga idanunta.

“Dije, bamu da wani zaɓi” mahaifiyarta ta ambata tana mai murmushin ƙarfin hali “Kinsan yanzu idanuwan al'umma duka yana kanmu, musamman kuma kowa yaga yadda kika nuna ba kya so a fili, abin da ya kamata shi ne mu roƙi Allah da ya kawo mana ɗauki.” mahaifiyarta ta cike maganar tata tana mai share ƙwallar da ta fara gangarowa daga idanunta.

Dije ta gyara daga kwance zuwa zaune fararen idanuwanta suna fuskantar mahaifiyarta daga nan ta kawar da kai tana cewa “To wai baba me zai hana mu fito fili mu gaya musu cewa mu bama bautawa kowa sai Allah, wataƙila su sauya tunani su zaɓi wani su yanka tunda suna ƙyamatarmu mu musulmai.....”

“Tabbas yin hakan shine mafi girman kuskuren da zamuyi” mahaifiyarta ta ambata yayin da take shafa gashin kan Dije.

Haka Lami, mahaifiyar Dije tayi ta kokarin rarrashinta da nuna mata cewa abin da Allah ya hukunta babu makawa shi zai faru, a haka har bacci ya sake kwashe Dije. Inda bayan ta fara baccin ne kuma mahaifiyarta ta fashe da kuka tana tunanin irin halin da yarta zata shiga...

★             ★            ★

Tun lokacin da aka ambaci sunan Dije a matsayin wadda za a yanka don a shayar da jininta ga abin bauta, sai aka baza dakaru a wannan alƙarya tasu wato alƙarya Sirnas, don su kula da kai kawonta. Sannan aka haramta mata ɗebo ruwa. Dama duk wani abu da zai sanyata tayi nesa da gida.

Wani abin mamaki shine maimakon al'ummar wannan alkarya su yiwa iyayen dije jaje, saidai suzo suna taya su murna. Wasu harma suna kawo kayayyakin ci da sha don a bawa dije duk don neman tabarrukin abin bauta...

A wani ɓangaren kuwa masu yin musulunci a ɓoye waƴanda mahaifin Dije jigo ne a cikinsu sukanzo suyiwa mahaifan nata jaje. Amma a ɓoye domin mutukar aka samu bayani a kansu cewar suna bautawa wani abin bauta dabam, ko kuma basa goyan bayan abin da abin bauta ya zartar, tofa hukuncin kisa ne.

Nasir, masoyin Dije kuwa ba zaka iya ayyana wani mutum wanda ya fishi shiga tashin hankali ba, domin kana ganinsa ba sai an gaya maka halin da yake ciki ba, duk da dai ya ƙuduri aniyar cewa mutukar yana numfashi babu wanda ya isa ya yanka masoyiyarsa ga wani abin bauta wanda shi kansa bai san kansa ba.

Ilfar, hamshakin jarumi ne, wanda yake son Dije, kuma ƙungurmin matsafi ne, shi ne babban bokan wannan alƙarya tasu tun bayan rasuwar mahaifinsa. Tabbas Ilfar yasha ganawa Nasir azaba akan ya daina kula ko shiga harkar Dije, amma Nasir yayi kunnen uwar shegu..... Banda Dije tayiwa Ilfar kashedin cewa kada ya sake ya hallaka Nasir, da tuni ya daɗe da hallakashi.

Gundas, kuwa shi ne babban ɗan sarkin wannan alkaryar kuma shima yana son Dije, don haka tun lokacin da aka ambaceta a matsayin abar yankawa Gundas ya fara tattaunawa da dakarunsa na sirri akan yadda zasu sace Dije don tseratar da ita daga sharrin abin bauta da kuma boka Lahan.

Duk wannan abu da yake faruwa tuni shaiɗanun ifritai sun sanar da boka Lahan.

★            ★            ★

Bayan kwana biyu da ambatar Dije a matsayin abar yankawa, sai Ilfar yaje gidansu, cikin tashin hankali mahaifinta ya fito don jin meke tafe da shi.

Ilfar ya risina ya gaida mahaifinta, abin da bai taɓa yi ba kenan ga wani a rayuwarsa inka ɗauke Dije wadda har sujjada yasha yi mata.

Bayan gaisuwa ilfar yace da mahaifin Dije to shifa ya zo ne ya ɗauketa don guduwa da ita zuwa wani yanki na wannan nahiyar domin bazai iya bari rayuwarta ta salwanta, idan ma mahaifanta sun yarda bayan ya kaita zai zo ya ɗaukesu suma ya kaisu inda ya kaita.

Mahaifin Dije ya tubure yace bai yarda ba, domin shi a wajensa bokaye ba ababen yarda bane. Bai kai karshen maganarsa ba Ilfar ya mangareshi. Take Sanda mahaifin Dije ya faɗi ƙasa sumamme. Shi kuma Ilfar ya kutsa kai gidansu Dije. Ya tadda ita zaune tare da mahaifiyarta duk sun tafka tagumi. kafin suyi wani yunƙuri yasa hannu ya mangare mahaifiyarta wadda karfin bugun yasa ta gwaru da bango kanta ya fashe jini yayi tsartuwa a fuskar Dije.

Dije a firgice ta miƙe ta kaiwa Ilfar raruma, amma sai kawai ya cafeta ya azata bisa kafaɗarsa yayi waje da ita. Ita kuwa ta taƙarƙare tanata dukansa iyakar ƙarfinta, amma inaaa ba ji yake ba.

Yana fita da ita ya haye kan ingarman dokinsa ya sukwane shi ya nufi hanyar barin gari. ai kuwa take dakaru masu kula da Dije suka fara tururuwa ta kowane yanki don kamashi.

Gundas da yake zaune cikin gidan sarauta take labari yazo masa, ai kuwa cikin ƙanƙanin lokaci yayi shigar yaƙi ya hau bisa ingarman doki da dakarunsa ya tafi don tarar Ilfar ya kwace Dije daga hannunsa, in yaso shi kuma zai san yadda zai yi ya kuɓutar da ita.

Nasir kuwa yana kwance yana tunane-tunane kala kala, kawai sai ganin tawagar dakaru yayi suna ta nufar hanyar barin gari.

“Lafiya?” Nasir ya tambayi wani magidanci a cikinsu.

“Ilfar ne ya sace Dije zai gudu da ita......”

Nasir bai tsaya wannan dattijo ya gama jawabi ba, sai kawai ya finciko shi daga kan dokin nan, sa'annan ya haye kan dokin ya sukwani dokin cikin dakarun nan don zuwa ceto rayuwar Dije.

Me kake tunanin zai faru?
Shin Ilfar zai iya guduwa da Dije ko kuwa masoyanta Gundas da Nasir zasu kwatota?
Idan sun kwatota shin zasu iya kareta daga sharrin abin bauta?
Idan kuma Ilfar ya gudu da ita shin yaya makomar rayuwarta zata kasance?

ƘARFIN SOYAYYA (Completed, 2020)Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu