Bahaguwar Fahimta

21 2 0
                                    

Tun bayan da Ilfar ya fadi ya suma, bai tsinci kansa ba, shidai kawai ya farka ya ganshi a kwance Nasir yana yi masa fifita, yayinda shi kuma Gundas yake gefe yana sanya magani a inda kibiya ta harbe shi lokacin da yake yunkurin cetar rayuwar Nasir.

Bayan sun nutsu ne daya bayan daya bacci ya dauke su, duk da kuwa cikinsu babu wanda yayi shirin bacci domin sanin hatsarin inda suke.

Washe garin ranar, rana ta fito cikin tsananin zafi, wannan zafin shine yasa dukkaninsu suka farka daga baccin daya sacesu a daren jiya.

Bayan sun dan taba abinda ya samu na abinci sai suka fara shawarar yadda zasu shiga dajin bahaguwar fahimta.

"Mu zauna mu huta domin na tabbata idan muka shiga wannan daji da wayannan raunukan a jikinmu babu wanda zai tsira da rayuwarsa, hasalima dai boka lahan cikin sauki zai karasa kaimu barzahu.” Jarumi Gundas ne ya fadi hakan lokacin da yake sanya garin magani a inda kibiya ta soke shi.

“Nikam ina ganin mu afka cikin wannan daji,” Nasir ne ya fadi hakan lokacin da yake kokarin mikewa “domin kunsan a yammacin yaune zai yanka masoyiyarmu ga kazantaccen gunkinsa.” a dai dai wannan lokaci nasir ya kammala mikewa tsaye.

Ilfar ya gyada kai ba tare da yace komai ba shima ya mike tsaye yana mai karkade kurar da take jikin rigarsa da hannunsa na dama, daya hannun nasa kuwa baida wani amfani domin dusar kankararsa har yanzu tana dandaryar kasa a zube, yayinda bigiren hannun a jikinsa ya koma gundulmi kawai.

Cikin gaggawa dukkaninsu suka kimtsa tsaf, amma bisa ga mamakinsu sai suka nemi dawakansu suka rasa, sukai duk wata alama da suka sani don kiran dawakan amma babu alamarsu.

“Hahaha” sukaji wata babbar murya daga kowace kusarwa, “dabbobinku sunsan bala'in dake gabansu shiyasa suka gudu suka barku, ina mai baku shawarar cewa ku juya ko koma cikin biranenku, zan muku alfarma guda daya, zan barku ku koma kowannenku ya bada wasiyya a wuni guda daya, bayan nan kuma zan dauki rayuwarku ta hanyar rabaku da rayuwar duniya baki daya......”

“Kai boka,” Ilfar mai hannu daya ne ya daka masa tsaya lokacin da yake huci kamar yaci babu. “Kayi sani cewa babu abinda zai sanya mu juya baya mu kyaleka kaci zarafin masoyiyarmu, tabbas tafi karfin ka shayar da jininta ga wani abin bauta mara tabbas....”

“Haaa!” Sautin boka lahan ya fada cikin wata murya mai kama da izgilanchi, “Au a cikin masu tunanin jayayya dani harda mai hannu daya?”

Kafin wani ya sake magana Nasir ya daka tsawa daga inda yake tsaye, tabbas a wannan lokaci ya tabbatar da cewa ko duka rundunar duniya ce a gabansa zai iya tunkararta, cikin karfin hali yace “Fada da buya ai tsoro ne, idan har ka isa ka qaraso inda muke mana, nayi rantsuwa da girman Allah, saina kaskantar da kai kaskanchi mafi muni......”

Wannan karon ko amsar bai bayar ba. Tsit sukaji, tsawon dakiku babu alamar sautin. Sai kawai suka nufi dajin bahaguwar fahimta. Suna jere su ukun kowanne ji yake a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa don ceto rayuwar dije masoyiyarsa.

Cike yake da duhuwa, da kwazazzabai gami da manyan duwatsu amma haka suka rinka tafiya suna cin karo da kananun halittu masu hatsari amma cikin kiyayewar Allah babu wanda yayi nasarar cutar dasu.

Ilahirin samaniyar dajin bakikkirin ne, baka ganin komai sai duhu, wasu dogayen bishiyu dama da haunin dajin sune iyakar ganin mutum, daga tsakanin ganyayyakinsu ne haske yake saukowa zuwa dandaryar kasar dajin.

Suna cikin tafiya, kwatsam saiga wani bajikin zaki ya nufatosu a guji, Nasir ya zabura zai zare takobi, ilfar yayi maza ya rike masa hannu yace “Muddin ka kula dashi zai samu galaba a kanka. A cikin dajin bahaguwar fahimta duk abinda ka gani ka kula dashi, idan kaga alamar duhun inuwa a tattare dashi to tabbas na gaske ne, idan kuma kaga babu alamar inuwa a tattare dashi to tabbas na karya ne, kuma wannan na karyar yafi hatsari domin kuwa muddin ka kula shi to tabbas zai hallakaka domin babu makamin da zaiyi tasiri a kansa... Wannan ne yasa ake kiran dajin da sunan bahaguwar fahimta.”

ƘARFIN SOYAYYA (Completed, 2020)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora