Karfin Soyayya...

32 4 9
                                    

Ilfar da Nasir suka ci gaba da fuskantar Boka Lahan da matsanancin gudu zuciyarsu kuwa cike da fushi da bakin cikin ganin irin kisan gillar da yayiwa dan'uwansu.

Har a wannan lokaci kan Boka Lahan kan zaki ne, tsaye yake a waje guda yana wulwula takobinsa mai walkiya.

Kafin su karaso inda yake sai kawai ya ɗaga takobin tasa ya sari ƙasa da ita, waji haske yabi dandanyar kasa, kafin suyi wani yunkuri hasken ya riskesu, yana zuwa dai-dai inda suke sai kawai yayi wata kara, wata iska mai tsananin karfi tayi wurgi dasu.

Lahan ya sake kyalkyalewa da dariya cikin wani sauti mai mutukar tsoratarwa. A wannan lokaci kuwa dije tana gefe daure cikin sarƙar tsafi.

Cikin jigata Ilfar da Nasir suka mike kowannensu da jini a sassan jikinsa, tufafinsu sun yayyage, sannan duk sun kukkuje jikkunansu.

Nasir ya durkusa ya dauki takobinsa ya gyara tsayuwarsa, tabbas yasan ba karfinsa bane, wannan karfin soyayyar da yake yiwa dije ne. Hakanan shima ilfar a wannan lokacin ya gama mikewa, wannan karon wani gatari irin na mayakan zamanin da' ya rike, mai tsananin kaifi da tsini a karshen kowanne kaifi.

Ilfar yayi tafi, sai gashi kusa da Nasir, cikin yanayi na murmushi ya kalli Nasir cikin raɗa yace "Zanyi amfani da dukkanin tsafin dana mallaka daga wajen babana da kakana, wannan itace hanya daya da zan iya kashe wannan hatsabibin bokan, nasan kodai muyi ragas dashi, ko kuma bayan na kasheshi nima in rasa rayuwata, domin babu wani matsafi da yakai matakin tsafi irin nawa daya taba amfani da dukkan tsafinsa lokaci guda kuma ya rayu. Idan na kasheshi zan ƙoƙari zan kwance maka dije, ka tafi da ita, tabbas na sadaukar da ita gareka, kuma wannan shine gudummuwata a aurenku kaida ita." Ilfar ya juya ya kalli Boka Lahan wanda yake kara kusantosu, sannan yaci gaba da cewa "Idan ka koma cikin gari, ka nemi gafarar mutanen alkaryar mu, duk wanda na cutar kace ina neman yafiyarsa, domin ina tsoron haduwata da ubangijin ababen bauta... Nasan zakaji mamaki, to tabbas babu mamaki, domin nasan addininka shine addinin gaskiya, saidai bani da damar dazan karbe shi....."

Wani sara daya sauka akan gundulminsa ne ya dakatar dashi daga maganar da yake gami da kwalla wani ihu mai rikitarwa.

Kafin nasir yayi wani yunkuri tuni ilfar ya cakumi Lahan sun fara kokawa sunata kici-kici kowa yana kokarin cutar da ɗan'uwansa.

A wannan lokaci ne ilfar yayi nasarar yin jifa da Lahan, duk girman Lahan sai gashi anyi wurgi dashi gefe guda, yaje yaci karo da wata bishiya, dashi da bishiyar suka fadi kasa rikicaaa...

Kafin Lahan ya taso, sai kawai Ilfar ya durkusa ya damki kasa da dukkan hannunsa wani zazzafen bakin ruwa yana fitowa daga idanunsa, yana furta wasu kalamai wayanda mai sauraro baya gane kalaman, take aka fara wata tsawa da walkiya mai tsanani. Kasar dajin ta kama girgiza... Wata kara tamkar ana bude katowar kofar bakin karfe ta cike wajen... Daga nan kawai sai ilfar ya rikida ya zama wani katon goggon biri yana dukan kirjinsa da hannayensa guda biyu.

Wannan lokaci Lahan ya mike amma maimakon ya tsorata sai kawai ya kyalkyale da dariya, a daidai wannan lokaci kuma kan zakin ya juye izuwa kansa na ainihi.

Ilfar daya juye zuwa goggon biri ya nufoshi da tsananin guda, ai kuwa sai Ilfar shima ya nufoshi, suka hadu wani tartsatsin wuta ya tashi tamkar ƙarfe da ƙarfe ne suka hadu.

Nan fa suka wanzu cikin kaiwa juna duka hannu da kafa, Nasir da Dije wadda take daure cikin sarka suna kallon abinda ke faruwa cikin fargaba da rashin sanin wanda zaiyi nasara.

Goggon biri Ilfar ya kama kan Lahan yana kokarin murde masa wuya, Lahan yayi kokarin kwacewa amma sai abu ya gagara, zuwa can kawai saiya rikide ya zama wuta, babu shiri ilfar ya sakeshi, a wannan lokaci hannun ilfar ya kone, kafin ilfar yayi wani yunkuri Lahan yayi tsalle sama a cikin wutar daya zama ya daki ilfar a kirji. Ilfar yayi baya taga-taga kamar zai fadi amma saiya cije. Yayi girgiza ya daga hannayensa sama, ya daki kasa dasu, wata bakar guguwa ta tashi taje ta daga Lahan sama, amma kafin tayi nisa dashi sai kawai yayi tafi da hannayensa, take ta dauke. Ya diro kasa da kafafuwansa.

ƘARFIN SOYAYYA (Completed, 2020)Where stories live. Discover now