Gudun Tsira...

23 3 0
                                    

Ilfar gudu yake akan dokinsa yayin da dakaru ke biye da shi don kamoshi, jefi-jefi kuma wasu suna shan gabansa don salwantar da rayuwarsa amma da yake gwarzone duk wanda yasha gabansa tofa sai dai a tarar da gawarsa.

Wani matsanancin gudu yake tamkar iska, kawo i yanzu ya sadu da bayan gari, sai dai har yanzu dakaru na biye da shi waƴanda tazararsa da su bai wuce taku biyu zuwa uku ba.

Dakarun suka himmatu wajen ganin sun kama Ilfar ko kuma sun hallakashi amma abu sai ya gagara, maharba a cikinsu suka rinƙa harba masa kibbau, amma duk kibiyar da ta daki jikinsa sai kaga ta kama da wuta ko kaga ta zama hayaƙi ta bace bat.

Yana tsakiyar gudu ne kawai yaja linzamin dokinsa yayi turjiya ya juyo ya fuskanchi dakarun da suke biye da shi ya daka musu tsawa gami da yin wani ƙaraji. Ai kuwa sai dawakansu suka tirje, suka rinƙa ja da baya cikin firgici...

“Hahaha, Ƙarya kuke yammatan dakaru” Ilfar ya ambata yana mai ɗaure fuska, “Babu wanda ya isa ya ƙwaci sarauniyata daga hannuna, ballantana har akai ga yankata ga abin bauta... Tabbas wannan karon abin bauta yayi kuskure...”

Gundas da yake cikin dakaru ya bazamo daga gaba-gaba ya dakawa Ilfar tsawa yace “Kai ƙaramin jarumi, ka gaggauta turo Dije izuwa gareni ko kuma yanzu ka tsinci kanka ya rabu da gangar jikinka”.

Kafin Ilfar ya bada amsa tuni sai ga Nasir ya sukwano ya shiga tsakanin Gundas da Ilfar, Ilfar ya ɗan ja da baya kaɗan yana mai ƙyalƙyala dariyar mugunta.

A sannan ne kuma ilahirin bayan garin yayi duhu, yayin da wata ƙaƙƙarfar iska ta taso gami da wata baƙar guguwa, guguwar ta nufi Ilfar ta kewaye shi da su Nasir da Gundas kafin suyi wani yunkuri wannan guguwar duk ta rikito dasu daga kan dawakansu, yayin da guguwar ta kewaye Dije ta ɓace da ita babu ita babu dalilinta...

Filin yayi tsit aka rinƙa kallon-kallo.

Jim kaɗan sai suka ji anyi wata tsawa mai rikitarwa, sai ga Boka Lahan ya bayyana riƙe da Dije a hannunsa a sararin samaniya. Ya kallesu tare da ƙyalƙyalewa da dariya.

“Kwana biyar suka rage in yankawa abin bauta abin yankarsa, kuma babu wanda ya isa ya kawo min tangarɗa a abin da muka zartar ni da abin bauta.”
Boka Lahan ya ambata yana mai zazzare ido gami da sake bushewa da dariya.

Cikin wata zuciya ta dakiya Nasir ya kalli Boka Lahan wanda yake sararin samaniya sa'annan yace “Babu wanda ya isa ya shayar da wannan jini mai tsarki mai daraja ga ƙazamin abin bautar da kake ambata, kuma muna nan sai mun ceto rayuwarta daga hannunku, bama ita kaɗai ba, wannan al'ada ta yanka mutane tazo karshe...”

“Kaiiii!” Boka Lahan ya dakawa Nasir tsawa yayin da ya murtuke fuska wannan karon ko dariya baya yi, yaci gaba da cewa. “Zan ajiyeta tare da ni a dajin Bahaguwar Fahimta, idan akwai wanda ya isa sai ya shigo dajin a kasa da kwana biyar don ya cetota, ina mai yi muku rantsuwa da ubangijin ababen bauta babu wanda zai dawo da numfashi a cikinku...”

Yana gama furta hakan ya bace ɓat, yayin da a hankali hasken garin ya fara dawowa cikin ƙanƙanin lokaci sai komai ya dawo dai dai.

Gundas, Nasir da Ilfar sukai kallon kallo babu wanda yace wani abu, yayin da su kuma dakaru suka himmatu wajen dibar gawarwakin da Ilfar ya kashe.

Zamu dakata anan, sai kuma a rubutu na gaba.

Kada a manta da batun votes da kuma comments, shin friends ɗinka masu cancanci ka gayyacesu don karanta wannan ƙayataccen labari ba?

Shin Nasir, Ilfar da Gundas zasu iya zuwa dajin Bahaguwar Fahimta don ceto rayuwar Dije?

ƘARFIN SOYAYYA (Completed, 2020)Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora