Artabu

13 3 0
                                    

Wayannan gwarangwal masu jikin wuta suka rinka shawagi a sararin samaniya suna kyalkyale dariya suna kuma harbo musu da kibiyoyi babu kakkautawa.

Tun suna kaucewa cikin karfin jiki da kuzari har ya zamana sai sunyi da gaske suke iya kaucewa...

Suna cikin wannan yanayi ne dabara ta zowa Ilfar, ai kuwa saiya daga garkuwarsa sama ya fara karanta wasu dalasumin tsafi iyakar karfinsa yana karaji, jijiyoyinsa suka tashi sukai burdin burdin idanunsa suka kada sukai jajur... Yaci gaba da karanto dalasumin tsafin aikuwa sai wannan garkuwa ta hannunsa ta fara budewa tana qara girma da fadi, saboda girma da nauyi saida ya durkushe, ita kuwa wannan garkuwa a wannan lokaci ta rufesu duka da shi da gundas harma da nasir, wanda hakan ya sanya suka tsira daga harbin da wayannan kwarangwal suke musu domin wannan garkuwa ta kare su tayi musu shinge daga wayannan kibiyu, saidai duk da suna karkashin wannan garkuwa amma hakan bai hanasu jin dariyar kwaramgwal din nan ba, karar harbin kibiyoyin da kuma karar dirar kibiyoyin akan wannan garkuwa.

Cikin kankanin lokaci sai wannan garkuwa ta fara daukar zafi har wasu sassa na jikinta suka fara rikidewa zuwa launin ja, alamar wuta. A dai dai wannan lokaci kuwa tayi nauyin da ta rinjayi Ilfar. Gundas da Nasir suka yunkura donsu hada karfi wajen daga wannan garkuwa, amma sai Ilfar ya dakatar dasu da daya hannun nasa wanda ya dafe kasa dashi.

Kamar wanda aka tsikara sai kawai sukaga ya zabura ya takarkare yana karanto wasu dalasuman tsafi da wata murya tamkar zaiyi aman kayan cikinsa, idanuwansa suka fara fitar da wani haske mai kama da hasken farar fatila, gashin kansa ya mimmike, jijiyoyinsa suka taso sama suna rawa gami da sauya launi zuwa jar kala, lebbansa suka rinka kakkarwa kamar ba jikin mutum ba. Lokaci guda ya fara kumbura yana kara girma, har saida ya zamana ya ninka girmansa na asali sau uku. Daga nan sai wata kakkarfar iska ta rinka fita daga jikin garkuwar tana zuko wayannan gwarangwal din... Har saidai ta zukosu duka daf da ita.

Duk da haka basu sarara wajen harba kibbau zuwa ga wannan garkuwar ba.

Ilfar ya kara dagewa wajen karanta wasu dalasuman tsafin, a wannan karon kuwa muryarsa bata fita sosai saboda disashewa. Ai kuwa sai wata iska mai matsanancin sanyi ta rinka fita daga jikin wannan garkuwa tana daskarar da kwaramgwal din. Hannun Ilfar ma a wannan lokaci ya fara daskarewa, ya kwarara ihu saboda wani zugi da yaji kamar ana kwankwatsa kasusuwansa.

Bayan wani lokaci gaba daya gwarangwal din nan sun gama zama kankara, shi kuwa ilfar tun daga kan yatsunsa har zuwa damtsensa na hannun hagu wanda dashine ya rike garkuwa ya daskere kamar yadda itama garkuwar ta gama daskarewa.

Ilfar kamar ba shine wanda muryarsa ta dusashe ba, sai sukaji ya kara kwalla ihu yana karanto wasu sabbin dalasuman yana gamawa wayannan kwarangwal duk suka tarwatse. Gundas da Nasiru cikin murna suka tafa, domin sun tsira daga hallaka, sun manta cewa gabansu shine mafi girman hatsarin da wani mahaluki zai iya fuskanta a rayuwa.

Bisa ga mamakinsu sai sukaga shi Ilfar kuka yake, kafin su tambayeshi dalili sai sukaga itama garkuwarsa data zama kankara ta tarwatse... Ilfar ya daga hannunsa wanda ya daskare yana mai zubar da hawaye yana girgiza kai cikin bakin ciki, aikuwa sai wannan hannu nasa ya tarwatse. Take ya fadi kasa sumamme.

ƘARFIN SOYAYYA (Completed, 2020)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora