'Yan uwan juna

1.2K 107 0
                                    

DABAIBAYI👄

©Khadija Ahmad (Kdeey😊)

®Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

                          (6)
Tayi saurin juyawa ta koma office d’inta,

GET WELL HOSPITAL, asibiti ne da babban d’an kasuwa Alhaji Ammani ya ginawa babban d’ansa Hasheem bayan dawowar sa daga UK inda ya karanci gynecology wato likitan mata, asibitin be tsaya anan kad’ai ba akwai ‘kwararrun likitoci daga ‘bangarori da dama dake aiki cinkinsa tsaftataccen asibiti ne wanda ya gaji da had’uwa ta fannoni da dama kama ga ma’aikatan kiwon lafiyar, masu gyare gyare, wadatattun magunguna da dai sauran su

Saboda sau’kin da asibitin ke da shi da kuma kwararrun likitoci ga kyakkyawar kulawa da ake baiwa majinyata yasa mutane ke tururuwa cikinsa. Wannan kenan,

Alhaji ammani abokin Alhaji Ibrahim ne sosai hakan yasa alhaji kabiru ya bud’e family file a GET WELL gashi basu da nisa sosai.

***
Tun kafin motar takai ya tsayawa ya dira yayi cikin gida direct d’aki ya shiga yana tattara kayan sa ya na tura su cikin akwati ya d’auko passport d’insa ya zira cikin Jakar dake goye a bayansa wayarsa dake hannunsa ya sa gaban aljihu ya nufi hanyar fita

“Yayana ya haka?”

“Abba zan wuce airport ne “

Ya kalli agogon hannunsa “airport by this time?”

“Abba remain 2hrs fa”

Umma tace “To ai ka jira abokin tafiyar taka yazo ko?”

“Ya sameni a can” yayi gaba

Baki, hanci, ido ta saki tana binshi dasu,

A tsawace Abba yace “Yayana haka ya kamata kayi wa mahaifiyar ka magana?! Tamkar wata sa’arka!, ka dawo nan ko kuwa!”

Cak ya tsaya, har seda Abba ya kuma cewa “ba da kai nake bane?”


Dawowa yayi yana faman hura hanci, daf dasu ya tsaya, “idan har ka tafi ba tare da ka bawa mahaifiyar ka ha’kuri ba kai fa Allah!”  Ya juya zuwa cikin gida.

***
Dr Hasheem ya kallesu murmushi bisa fuskar shi “gaskiya you are a lazy being Anwar”

Lumshe ido yayi kan ya bud’e su a kan hasheem “think whatever you want, bazan damu ba” ya cigaba da daddanna mini laptop d’in dake bisa stool,

Girgiza kai Bro B yayi sanin cewar d’an uwan nasa baze kuma furta wata kalmar ba, ya kalli Dr yace “Allah da ace bansan Bro A ba zan iya ko bin hanyar da yake ba talkless of na mishi magana, kaga fa da muka shiga d’akin can ko kusa da gadon qin zuwa yayi, kamar wanda yaga trash”

“Ai wallahi da zan samu uncle zance masa ne kai ya kamata kaje hutu shi ya zauna ya cigaba da aikin”

Wani kallon karka fasa ya watsawa hasheem, hasheem ya kwashe da dariya yana fad’in “Allah kuwa kai da qasar haihuwar ka amma kabi ka tsane ta,”

“Ka fad’awa wanda aka Haifa anan ba de Anwar ba!”

Bro B yace “naji d’in and I’m proud to be a Nigerian”

Harara daya watsa masa ne yasa shi saurin d’aga hannuwa “I’m sorry big Bro”

Wayar dr hasheem ce ta katse su inda tashiga qara alamun kira dannawa yayi muryar wata nurse ya doki kunnuwansu “Dr room no.18” katse wayar yayi suka mi’ke a tare banda Anwar dake cigaba da latse latsen system,

Hasheem ya kalli Bro B “ i think you should stay here gara naje naga halin da take ciki tukunna,”

Nodding yayi shi kuma ya fice xua d’akin.

Maida hankali yay kan d’an uwan nasa yace “Bro A do you think is a good idea ka tafi ka barni ni kad’ai anan?”

Murmusawa yayi “kar ka damu I’ll soon be back afterall kasan hankali na baze ta’ba kwanciya ba matsawar kana cikin mugayen mutanen nan, so chill dana kwana biyu zan juyo, kar ka manta you are my only family now”

Forming line yayi da baki, Bro A ya bashi assuring look tare da tapping kafad’ar shi , kiran dr hasheem ne ya shigo wayar Anwar, yace dasu suzo su same shi, tare suka jera zuwa d’akin

Bro B ne ya fara sallama ya shiga, tayi waal da ido
   “Mu...Mu’allim Bello”

Murmushi ya sakar mata sam ya jikin ki?”

Gaza ansa shi tayi, tayi waal tana bin Bro A da ido ‘O’ shape tayi forming da bakinta, “Mu’allim is he your brother?”

“Yeah...big brother”

“Hello Mu’allim’s bro” ta d’aga mishi hannu.

Blank look ya bata without saying a word ya maida hankalinsa kan waya.

©Kdeey😊

DABAIBAYI (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now