14

815 82 0
                                    

DABAIBAYI👄

©Khadija Ahmad (Kdeey😊)
WATTPAD @Deejaht ahmad

®Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

                          (14)

*NOT EDITED *

Tunda security man ya sanar da ita saqon mu’allim bello gabanta ke fad’uwa, tare suka taho da sholey har ta isa jikin motar sannan su kayi sallama, knocking window tayi jin qofar a rufe, shiru ba’a bud’e ba kuma qwanqwasawa tayi jin ba’a bud’e d’in ba yasa ta kara fuskar ta jikin window wai ko zata gano ciki, wur wur take da ido, jiki na rawa jin wani mugun fitsari  daya cika mata mara gashi bata son shiga toilet d’in makaranta idonta ya cika da kwalla jin yana neman zubowa , kallon motar ta kuma yi gata dai se huci take amma ba alamun mutum cikin ta, juya wa tayi da niyyar nufar waje dan neman abun hawa, taku biyu zuwa uku taji ance “ke!” Banza tayi dan a tunaninta mazan makarantar ne jin ana ta cewa ke! har sau ba adadi had’e dayin horn yasa ta waiwayo a fusace tana faman matse ‘kafafu

Wani irin bugu qirjinta yayi bazata ta’ba mance wannan fuskar ba ko da cikin mafarki wani nannauyan yawu ta had’iye a qafule ta watsa masa daradaran idanunta dake ta tsiyayar hawaye, komawa yayi cikin motar ya zauna yana qare mata kallo ta side mirrow badan tanaso ba se dan taimakon kanta kar tayi fitsarin wando yasa tayi saurin zuwa ta shiga tun kan ta qarasa rufe qofar ya figi motar su gateman da tsalle aka sha.

Ido ta runtse tun qarfi hannunta bisa handle d’in qofa ta ruqunqume duk tabi ta firgita jin yacce yake manna gudu bisa shimfid’ed’iyar kwaltar sokoto road, qafar nan tata gam take dan qiris take jira fitsarin ya zubo, wani irin giya yaja aiko sam ta qwala qara tun qarfi tare da fad’owa jikinsa ta ruqunqume shi, ita duk a tunanin ta accident su kayi, a hankali ta shiga bud’e ido jin shiru ba ko motsi

Idanunta suka fad’a cikin nashi hancinta dake bisa nashi ta janye da sauri kanta a qasa, “d’agani”

Sassanyar muryarsa ta doki kunnenta, saurin kallon kanta tayi cikin zare idanu ta koma bisa seat d’inta,

“Ke!!!! Fitsari kikayi min!!!!!”

Wani irin bugu qirjinta yayi tamkar ze ‘ballo waje ta shiga kuka wiwi tana sheshsheqa tabbas fitsari tayi kuma a jikin sa innalillahi wa innalillahir raji’un, yau kam tasan wannan mutumin se ya kusan kasheta,

Ji tayi ya ja motar ya kuma tsaya lokaci qanqani ta rikice ganin da tayi sun shigo wani gida murya na rawa tace “dan girman Allah kayi haquri kar kayi min komai wullahi zanyi duk abinda kace” kula da rud’ewar da tayi yasa shi sassauta abinda yayi niyyar yi mata, bud’e qofa yayi ya fita tare da fad’in “biyo ni”

Ciki ba qwari ta bi shi a baya har zuwa wani tafkeken falo me d’auke da kujeru seti biyu, wata qofa ya nuna May da yatsa “shiga ki gyara jikin ki, akwai aerial cikin toilet yanzu zan kawo miki kayannan ki wanke min tass!”

“Uhum”

Yaja tsaki “dirty human being”

~~~~
2 hours later

Parking Bello yayi suka fito se fara’a suke shida uncle, “kaga abinda nake fad’a maka ko?”

“Sosai uncle, nifa abin nan ya d’auren kai kana ganin zata yarda da maganar mu kuwa duba da ta manta abinda ya faru shekara ashirin baya?”

Dariya uncle yayi “yaro yaro ne kai dai zuba ido ka gani,”

“Su kuma su alhaji kabiru fa?...”

Murmushi yayi “they are trapped”

“Ban fahimce ka ba...”

Shigowarsu falon ke da wuya wayar bello tayi qara “gwaggon samira ce” ya furta idonsa bisa uncle,

“‘Daga muji”

Answer wa yayi, suka gaisa tace “dama nace yau ko su sam nayin wani abu ne a school shiru bata dawo ba”

Saurin kallon juna sukayi da uncle, cikin dabur dabur yace “ahh..ahh” uncle ya d’aga masa kai yace “eh nace ta jira na gama aiki ne se nayi dropping d’inta”

“Ayya to shikenan, na yarda da kai bazaka ta’ba barin wani abu ya kusance ta ba”

Girgiza kai yayi hannu a ka yace “insha’Allah nama gama yanzu zan kawo ta”

“Allah ya kawo ku lafiya” ta ajiye, a fusace ya juya zuwa window yaga ali driver na wankin mota, d’akin Anwar suka nufa se de daidai shiga d’akin suka ji an yi atishawa cak suka tsaya, kuma yi akayi har sau uku, da sauri suka fad’a d’akin da suke kyautata zaton anan ne.

Me zasu gani?
Sam!!! Suka furta a tare, “mu...muallimmm sanyiiii” ta fashe da wani irin kuka me cin rai, juyawa yayi ya d’auko bargo cikin wardrobe ya lullu’beta fad’i yake

“Shii shiii, babu abinda ze same ki kinji, trust me Sam, open your eyes please, ya kalli uncle, uncle kar ka bari ta rufe ido pls pls pls Sam say something,” tallafo ta yayi jikinsa yaji taja wani dogon numfashi har sau uku jikinta ya saki

‘Dora ta saman gado, wayar hasheem ya kira yana d’agawa ya fad’a masa tare da ce masa maza yazo yanzu.

©Kdeey😊

DABAIBAYI (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now