HIDDEN

1.5K 133 1
                                    

DABAIBAYI👄

©Khadija Ahmad (Kdeey😊)

®Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

                          (3)
“Ya ha..habibii”

Kanne mata ido yayi ” have I been missed?” yayi saki wata muguwar dariya “oya matsa daga gabana before na mangare ki” ya sake ta da sauri,
Sum sum sum taja jiki gefe har tana neman fad’uwa, Amir da shigowarsa kenan yaga duk abinda ya faru ya ja hannunta a fusace suka nufi mota.

Habibii ya bisu da muguwar harara, ya shige cikin gidan yana kwala wa umma Salamatu kira.

****
“Sam muje wasa?”

Girgiza kai tayi a hankali “um um sholey I can’t play now just go ahead “

“Why Sam ?” Yarinyar ta turo baki gaba alal dole ranta ya ‘baci ,
Mu’allim bello malamin islamic wanda yazo wucewa ya ji maganar tasu ya tsugunnawa

Yace “meya samu samira naga tana ‘bata fuska ta manta yau kun shiga secondary” ya ‘karashe maganar idonsa kan fuskarta

“Mu’allim tun safe haka take”

Jinjina kai yayi idonsa kan ta, yace “Samira kina tuna daddy ne?”

Kallonsa tayi idanunta cike da hawaye ya d’aga kai, “I miss him so much”

Bud’e baki yayi zeyi magana wani security ya iso da sauri “mu’allim that your bossy brother yazo nemanka”

“Ohhhhh, yanzu kuma” ya karashe da kallon agogon hannunsa kan ya juya ya nufi hanyar gate har yayi gaba ya waiwayo inda yaga idanunsu ‘kuri a kansa

  Yace” c’mon let’s go ”

Kallon juna sukayi kan su bishi a guje, daka d’an nesa yace su jira shi ya nufi motar dake parking lot ya shiga, ya jima cikin motar sannan ya fito.

Fuskar nan kadaran kadahan, har class ya raka su sannan ya koma office.

****
Umma salamatu ta d’ago a fusace bayan ta tabbatar da yaran sun tafi makaranta cikin d’aga murya tace

  “Kagani ko ka gani ko, yau kwana tara kenan Ina bin kanka a tura Sa’idu (qaninta)can turkey yabi sakaran yaran nan to ga irinta nan, yanzu how sure are you manager din baze cuce mu ba bare yaga ba idon mu, nifa Ina tsoron mutanen nan, dukiyar maraya fa!”

Ajiyar  zuciya Alhaji  kabiru ya sauke kan ya kalli habiibii yace “Kai na baka kwana biyu ka shirya ku koma tare da sa’idu, kaji dai abinda mahaifiyar ka ta fad’a “

Fuska a had’e ya amsa “naji Abba amma...”

“Amma me? uban naka zaka kawo wa qabali da ba’adi? Eyeh? Fice ka bani guri”

A fusace ya wuce, ta kalli Alhaji kabiru “nifa Abban yara inaga kaima se ka bisu kaje ka gano halin da ake ciki dan habibii yace wannan “Hidden” d’in sun aika musu da takarda kamar yacce suka tura wa ragowar kamfanonin”

A rud’e yace “what!?”

Ta kya’be baki “uhm duba ka gani”

Amsa yayi yana shafa velvet bag d’in da aka rubuta ‘HIDDEN da manyan ba’ki bud’e jakar yayi ya fiddo takaddar da akayi rubutu da silver ‘make sure kun Adana every details’,

“this is different from the others”

“And that’s why nake so mu iya takun mu, and again ina buqatar kud’i dan zan aika ma c.i.d d’ina this time around inaso ya samomin gamsassun bayanai a kan ‘HIDDEN’ I want them to know they are dealing with d wrong people,

Girgiza kai yayi ya wuce, ta bi bayansa da ido har ya fice ta d’auki wayarta ringing d’aya tayi aka d’aga “proceed as planned “ ta furta cikin kausashiyar murya

****
Bayan wasu watanni

Ta du’kufa sosai Amir yana koya mata maths dan gobe zasu zana jarabawar gama aji d’aya, “umma salamatu inaso ki tayani da addu’a gobe zamuyi maths” ta ‘karashe a shagwa’be,

Shafo saman kanta tayi, “Insha’Allah habibty, Allah ya bada sa’a I trust you,and you never disappoint”

Smiling tayi har beauty point dinta ya lotsa Amir ya zira biro ciki ta bige hannun tana dariya idonta kan umma salamatu wacce take kalla,

Tsugunnowa tayi ta bata peck a chubby cheeks d’inta tace “concentrate habibty”

Smiling tayi ta juya kan littafinta tana faman turo baki, sanin cewar dashi take ya ri’ko hannunta “am sorry baby sis ni ne ko bazan kuma ba kinji”

Kallonsa tayi tare da nuna masa ‘karamin yatsanta tace “promise?”
Ya sar’kafe cikin nashi “I promise”, suka cigaba da karatun su.

Washegari
Tafe suke zuwa office d’in mu’allim bello suna hirar yacce exams d’in tayi musu dad’i sunzo daidai sport center ball ta gangaro gabansu ‘Kiris ya rage sholey tayi tuntu’be Sam ta ri’kota, a fusace ta d’ago ta fara fad’a zabgegen yaron da ya zo d’aukan ball d’in ya tsaya yana huci fuskar nan a cusgune Sam da duk ta firgice ta hau Jan hannun sholey su tafi ‘ki’kam ta’ki tafiya ala dole ta saketa ta nufi office d’in mu’allim bello a guje daidai lokacin ya d’aga labule kanta ya bigi ‘kirjinsa ‘kamshin daya doki hancinta ne yasa tayi saurin d’ago kai idonta ya sauka kan...

©Kdeey😊

DABAIBAYI (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now