24

1.1K 97 0
                                    

DABAIBAYI 👄

©Khadija Ahmad (Kdeey)😊

®Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

_ina dad'a neman afuwa na jina shiru da kukayi hakan ya faru ne a bisa tafiya da nayi, nagode_

                 (24)
Tamkar sukar aradu muryar tata ta doki kunnuwansa, daqyar ta tattara courage dinta t angije shi gefe tare da fad'awa jikin ammi had'e da sakin wani marayan kuka, a kid'ime Ammi ta d'ago kanta ta shiga duba  ta tamkar me nemo wani abu, kan ta kada baki tace "maza share hawayenki yar albarka, ba abinda ze same ki kinji, makarantar da zaki ta qawata ce duk lokacin da kike kewata zansa a baku waya se mu rinqa jin lafiyar juna uhm?" Ta d'aga kai, "good, maza kuje nasa eliza tayi miki packing abincin cikin flask dan bazan so 'yata daga zuwa ta fara da abincin makaranta ba ko ya?" Nan ma kuma d'aga kai tayi , Ammi tasa thumbs d'inta biyu taja kumatunta, "oya give me that one in million dollar smile"

Murmusawa tayi, had'e da kuma shigewa jikin Ammi, "wuce ka d'auko kud'i kuje ka saya musu suturu kafin kayi dropping d'insu" Ammi ta furta ba tare da ta kalli sashin da yake ba,

Jiki a mace ya ja qafa tare da ra'bewa ya fita ta wani hanyar, saman sitiyari ya kwantar da kai, idanunsa a lumshe ya san cewa yana da yawan buqata amma be ta'ba expecting qaramar yarinya irin Sam zata iya jan ra'ayinsa har haka ba, shin meke faruwa ne?

The feeling is so weirdo that he can't even imagine yanda akayi har ya isa gareta ya kuma mallaka mata bakinsa da ko kimberly da take fad'i tashi wajen ganin ta samu matsayin sumbata ba tayi nasara ba se kwailar yarinyar da bata yi wata cikakkiyar balaga ba, fursar da iska yayi lokacin daya jiyo sautin taku

Dag can ya hangota kwance gefen kafad'ar Ammi munu na gefe suna murmusawa farinciki lullu'be da kowannen su, knocking da akayi bisa window yasa shi saurin sa hannu ya bud'e,

"Maza ka sauke su ka dawo" tace game da juyawa ta koma,

Forming line yayi da baki had'e da cije ha'koransa har ana iya hango yanda gefen goshinsa ke lo'bawa, shiru ne ya ratsa motar, munu dake a gaba tafi maida hankali wajen qarewa garin kallo yayin da Sam ke raku'be a kujerar baya,

Sosai yayi musu siyayya kan ya je ya damqa amanarsu a hannun miss chloe inda aka wuce dasu d'akin kwanan su direct me d'auke da gadaje biyu gefe da gefe

"Ya Allah" Sam ta furta ido waje munu kuma tace "Masha'Allah", rungume juna sukayi , idanunsu suka shiga roaming around d'akin bangon d'akin manne yake da stickers d'in sophia the first yayin da ko wani gado ke had'e da reading table se toilet madaidaici, kalar d'akin pink ne haka ma kalar curtains da carpet d'in duka, knocking da akayi bisa door ne yasa su dawo wa daga duniyar kallon da suke

"Yes" suka furta a tare, wata dattijuwar baturiya ce ta leqo d'akin with a smile plastered on her face,
"Wellcome to saint teresa college"

Nodding sukayi game da fad'in "thank you"

"I'm miss patricia, dafatan zakuji dad'in kasancewar ku a nan, ni ce shugabar d'akunan hostel d'inku hope you will cooperate with me"

"Sure" suka ce tayi musu thumbs up ta tafi had'e da rufe musu qofa"

"Saint teresa" munu ta furta cikin rolling eyes kan ta fad'a saman gado, dariya tayi ta juya ta nufi bathroom ta dauraye hannu ta fito gefen gadon ta zauna ta shiga bud'e flask dan kauda yinwar dake qwaqularta.

~
"Care to explain yourself?"

Hannu sa daya d'ora saman handle ya janye game da waiwayo zaune take medicated glass maqale saman idonta tana duba jarida, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kan ya taka ya isa gabanta

DABAIBAYI (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now