17

911 92 1
                                    

DABAIBAYI👄

©Khadija Ahmad (Kdeey😊)
WATTPAD @Deejaht ahmad

®Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

                          (17)
Tun daga nesa ya hango motar rannan a qofar gida,  daga can baya ya tsayar da motar had’e da sauke wani gauron numfashi , “ya dai?” Bello ya tambaye shi, “ku sauka ku bi ta gate d’in baya” bello ya maida idonsa inda yaga Anwar d’in na kallo, wata baqar mota ya gani a qofar gidan wani mutumi jingine jikinta bayansa a juye, jikinsa ne ya bashi cewa ba lafiya ba, “su waye wad’ancan?” Ya furta a hankali, “abinda nake son sani kenan, har yanzu ba wani feedback daga wurin bashari ne ?”, “a a  nasan da ya kira” girgiza kai Anwar yayi ya kalli su Sam ta cikin mirror had’e da sauke ajiyar zuciya a hankali yace “shiga dasu, zan bi bayan motar can” d’aga kai bello yayi ya juya baya “gwaggo bismillah muje mun iso ”

Hanci taja, ta kama hannuwansu suka bi bayansa, tsawon mintuna sha biyar sannan mutumin ya matsa ya shige gida, motar taja.

Ta wata kwana ya bi ya cimma motar a hankali yake binsu har zuwa commissioner road cikin wani tafkeken gida aka shiga, waige waige yayi unguwar shiru ba’a ji komai se kukan tsuntsaye, daga can baya kad’an ya hango wani me trader zaune yana quqqulla leda, parking yayi ya sauka zuwa wurin mutumin,

Sallama yayi had’e da fad’in “Washh Allah baya na, na gaji” buzun dattijo ya d’ago da kanshi da hausa shi da bata fita dakyau yace “sannu bawan Allah”

“Yawwa baba, dan Allah taimaka min da ruwa mana tun safiyar yau bansa komai a ciki na ba”

“Kash se de fa kayi sa’a duk masu zafi ne “ ya miqa masa sachet d’in pure water

Dariya Anwar yayi “nagode, amma baba daman talaka na samun abu me sanyi ne, rabo na da ganin ko qanqara na manta”

Kallon sama da qasa mutumin ya mishi, “kai kuwa daga ina kake haka dan shigar ka da kamanninka sun nuna kai d’in babban mutum ne”

Baki ya bud’e har da riqe ha’ba “wa d’in ni, tab lallai kace oga yayi aiki”

“Kamar yaya ban fahimce ka ba”

Gyara zama yayi, “ni sunana lawali nazo ne daga qaramar hukumar ajingi”

“To to ko kai ne sabon direban hajiya”

Jimm yayi zuwa can yace”..eh nine”

Kallon da tsohon ya masa yasa shi shan ruwan jikinsa,  “...amma..”

“Uhm...riqe maganar ka inde gidannan ne wata biyu na baka zaka gudu kaima da qafarka”

Ido ya waro waje “ko zan san meyasa kace haka?”

“..kaje ka gani..” ya miqe tsaye bari na kewaya

Binsa yayi da ido yana juya maganar, tashi yayi da zummar barin wurin ya hango wani ya leqo daga cikin gidan da motar nan ta shiga , bayan wata bishiyar darbejiya ya la’be, bisa mamaki sa se ganin wannan tsohon yayi ya fito shima yana waige waige har yana d’aga wa mutumin hannu

Cikin d’aga murya mutumin yace “ina yake?”

Dattijon dake leqe leqen neman Anwar yace “yanzu na barshi anan fa, wataqila gudu yayi”

Cikin d’aga murya mutumin yace “dalla ware, ni dama nasan duk qarya ka shirya son shigowa kake, To hajiya tace ka cire wannan tsimman ka shigo ciki”

Cikin d’aga murya dattijon yace “Kai dalla malam kasan yacce zaka rinqa min magana, ni ba sa’an ka bane” ya ja tsaki, hannu yasa ya cisge farin gashin bakin sa da na jikin gashin girar sa,

DABAIBAYI (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now