5

1.3K 120 1
                                    

DABAIBAYI👄

©Khadija Ahmad (Kdeey😊)

®Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

                          (5)
Bayan wasu kwanaki...

Firgigit ta tashi jin yadda ake buga ‘kofar d’akinta kamar za’a ‘balle, a iya ‘kiyasinta yanzu sha biyun dare ta wuce tabbacin kowa na gidan ya jima da kwanciya to wane haka? Ko de horror ne yazo cinye ni tunanin daya kuma rud’ata kenan har takai ga zubda hawaye jiki na makyarkyata, can ‘kuryar gado ta ma’kure kanta kira take
“Daddy...wayyo umma na...um...” kan ta’karasa aka banko ‘kofar tun ‘karfi wanda yayi daidai da d’aukewar numfashin ta.

Washegari
Kwala mata kira ta ke tun ‘karfi amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa,  “kai yarinyar nan kuwa Anya lafiya?

Baffa ya sauke jaridar dake hannunsa yace “kinsan fa yau saturday qila bata farka ba”

“Haba Abban yara sha d’aya fa ta gota ri’ke min yarinyar nan kaga bara na dubo ta”

Fad’owa yayi d’akin kamar wanda aka wurgo kallon sama da ‘kasa ta masa
“Kai lafiya naganka a firgice?”

Sana’ar tasa yayi ta susar kai yace “ko d’aya uwarmu kawai de...”

“Kawai de me?, kai gafara da Allah naje gun d’iyata” fuu ta wuce sa, fuska a cakud’e ya isa gaban Abba ya zauna yana faman kukkumbura “ya dai yayana?”

“Abba wai meyasa umma kullum take son min fad’a ni idan batason ganina ne ba se nayi komawa ta ba”

Murmushinsu irin na manya yayi kan ya Kada baki yace “yayana kenan ka ta’bajin inda uwa ta guji d’anta?...”

“To amma Abba baka ganin kullum kullum...”

“Kayi haquri kasan umman taku gidan gargajiya ta taso har da kunya irin ta d’an fari yasa take maka haka bawai intentionaly bane,um?”

“Abba shekarar ta nawa a birni nazata duk qauyencin mutum idan ya shekara arba’in ze dena amma...”

A tsawace Abba yace “kai da Allah can banson sakarci mahaifiyar taka kake fad’ar haka a kanta, To lallai yau na kuma tabbatar da kanka yana da matsala dole mahaifiyarka take complain a kanka tashi ka bani wuri” ya ja tsaki rai a ‘bace, cikin tafiyar bouncing ya nufi hanyar waje

“Ka kintsa dan jirgin ‘karfi biyar zaku bi”

Wani qululu ya tokare mishi wuya a zuciye ya nufi waje dede lokacin da ihun umma Salamatu ya iske kunnansu

A kusan tare suka fad’a d’akin, Amir ya tsugunna gabanta yana jijjiga ta “Sam Sam ki tashi! Sam wake up please”

Umma salamatu dake a firgice ta nufi kawu “Abban yara Sam..Sam bata motsi” rasa abinyi yay kawai ya ciro hular kansa yana firfitu dan duk da AC dake d’akin d’igar gumi yake.

Amir ne ya shiga girgiza sa “Abba muje hospital, Abba banson wani abu ya samu Sam”

Aljihu ya shiga laluba fad’i yake “ina kake ina na ajiye “ ya d’ago kai yana kallon habibii “kai maza d’auko key “ ya cicci’be ta suka nufi parking lots inns salamatu na sa’be da safiyya kafad’a .

*one hour later*
Likita ya kalli Alhaji kabiru a fusace “malam anya kuwa yarinyar nan ‘yar kace kamar yanda ka fad’a yarinya qarama ace tana d’auke da hawan jini?”

Murya na rawa umma salamatu tace “Ha..w..an jini likita?” Tare da dafe qirji

“Kwarai kuwa hajiya, am sorry to say amma a gaskiya ku kiyaye dan bugun zuciyarta am ba daidai yake ba, ko zaku iya tuna wani abu daya faru da ita jiyan?”

DABAIBAYI (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now