ALHINI

3.5K 188 2
                                    

DABAIBAYI👄

©Khadija Ahmad (Kdeey😊)

®Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

                            (1)
“Alhaji kabiru ga d’iyata nan samira kulawar ta na gareka yanzu, ka kula min da ita idan ta samu miji wanda yayi daidai da addini ka aura mata, kwanaki na basu da tsayi”

Ya juya kan barrister usman “inason duk wills dina ka adana wa samira har se ta mallaki hankalinta kuma kaci gaba da juya kadarori na, na aminta da kai na kuma baka dukkan yarda ta” tarin daya si’ke shi ne ya kasa ‘karasa magana nan falon ya hautsine masu koke koke na yi masu addu’a na yi samira da dawo warta kenan daga skul ta fad’o falon a firgice daidai kansa ta tsugunne tare da sakin marayan kuka tana fad’in

    “Daddy um um daddy karka tafi ka barni, daddy idan ka tafi ka barni nima binka zanyi, kaga bani da kowa se ku gashi mummy ma ta tafi ta barni...”

Hannun ta ya jawo dakyar ya d’ora kan na Alhaji kabiru maganar sa na fita dakyar yace “d....a..ga ya..u sh..ine daddy ki, Allah yay..i mi..ki albarka, ya shafo kanta yana salati, lokaci daya jikin sa ya saki idonsa a kanta rai yayi halinsa, gwaggo haulatu ta janyo samira jikinta tana sakin wani irin kuka me cin rai nan samira ta zube sumammiyya.

Wani private hospital dake kusa dasu aka nufa da ita inda aka shiga bata taimakon gaggawa, yayin da a can gida kuma aka shiga shirya gawar Alhaji dan ‘kasa dan kaishi makwancin sa.

Alhaji ibrahim d’an ‘kasa shahararren mutum ne wanda yayi suna ciki da wajen Nigeria, sana’arsa itace siyarda auduga se yan kananun abubuwa daya bud’e irin su kamfanin da ake yin designer jeans da ke carlifornia se gida je wanda yake bada haya a wurare da dama da kuma sauran kadarori wanda Allah yayi musu yawa, sai gonar nakin auduga masu yawan gaske.

Asalin su mutanen mambila ne dake jihar adamawa su uku ne wajen mahaifansu wanda suka rasu tun suna matasa, gwaggo haulatu ce babba se daddy sannan alhaji kabiru, daidai gwargwado suna da rufin asiri dan mahaifinsu manomi ne ya bar musu dukiya me dama.

Alhaji d’an ‘kasa yana da mata d’aya hajiya mariya da yarinyar sa d’aya samira wacce yanzu haka take shekara takwas a duniya, yarinya ce ta taso cikin gata cike da kulawar mahaifan ta duk wani jin dad’in duniya tana samu musamman da take ita kad’ai Allah ya mallaka musu.

Dukiya irinta Alhaji d’an ‘kasa, da kuma ‘kafa da yake da ita a government yasa ake bashi tsaro har ita samiran dan ko makatanta zata se da securities su jira har ta tashi su dawo da ita.

Samira na shekara bakwai hajiya mariya ta ‘bata a wata asabar ta shirya zuwa mahaifar ta bichi, kamar yacce ta Saba duk karshen wata, ita da amintaccen driver din alhaji me suna namadi har ila yau ba labarin su tun ana sa ran dawowar su har an fidda tun daga ranar Alhaji mai ‘kasa ya fara samun health deficiency wanda daga ‘karshe likitoci suka tabbatar da cewa yana da damuwa wacce yayi silar zuciyarsa ta samu matsala.

***
“Mami na, mami na”
Bud’e ido tayi ta kuma saurin rufewa ganin wani irin haske daya dabaibaye wurin, lalubar wurin ta shiga yi da hannu har tayi nasarar ri’ko wani lallausan hannu shima ya ri’ke ta gam, tsinto muryar daddy tayi yana cewa

  “Kar ki ta’ba bari ya kufce miki no matter what kar ki bari kiyi nesa dashi”

Juyawa tayi dan ganin me hannun amma blank se wannan hasken murza idonta tayi wai ko ze washe but still hasken na nan, a hankali ta kuma lalubawa gabanta tana cewa

  “Daddy wanene wannan d’in da bana gani? Ku..ma kuma kai ma kana ina?” Ta ‘karasa with a shaking voice

Dariyarsa taji, “mami na shi d’in haske ne *dabaibaye* da ke, don’t ever leave his sight”

“Um..to kai fa??” Hawaye suka fara zubo mata

Daga can nesa ta tsinkayo muryar shi “sai wata rana mami na, ki kasance me hakuri a duk yadda rayuwa tazo miki, Allah yayi miki albarka”

Cikin lalube ta tashi zata bi hanyar da take yaqinin yabi taji an janyo ta da ‘karfi ta fad’a cikin wani faffad’an ‘kirji dake fidda wani sihirtaccen ‘kamshi wanda yabi ta hancinta ya shiga cancikin ‘kwa’kwalwarta ya zauna, ‘ko’kararin ‘kwacewa take bakinta na kwala kiran Daddy Daddy...tun ‘karfi.

Girgizata suka shiga yi daga gwaggon har matashiyar yarinyar da baza ta wuce agemate din samira ba wani yin’kurawa ta kuma yi daidai lokacin ta bud’e ido

Seda ta ‘kare musu kallo sannan ta fashe da wani sabon kukan, hannun gwaggo ta ri’ko “gwaggo na ki kaini wurin daddy na tun kafin yayi nisa kinji”

Rungumeta tayi a jikinta tana share kwalla batare da ta bari ta gani ba, zuciyar ta cike da tausayin marainiyar Allah, kuka take bil hakki har se da likita ya zagayo ya mata allura.

A hankali matashiyar yarinyar ta isa gaban gadon da yar uwarta ke kwance tana shafa mata gashinta dake barbaje bisa pillow idonta ya d’uru da ruwan hawaye ta d’ago kanta tana kallon gwaggo tace

“Gwaggo yanzu haka Sam zata cigaba da kwanciya anan without us doing anything???, look how helpless she is, gwaggo dan Allah mu tafi da ita gidan mu se muke yin wasa tare tunda daddyn ta da mummyn ta basanan kinji” ta ‘karashe maganarta cikin kuka,

“Aa mubina Samira wurin mu zata zauna ko daddy?”

Juyawa sukayi dan basu ji shigowa ba, d’an lukutin yaron dake ri’ke da hannun alhaji kabiru yana washe hakwara ya watsa wa mubina harara

Yace “kar na kuma jin kince gidan ku zata je that your tiny little home hahaha”

Hura hanci tashiga yi ta taso a fusace tayo kansa gwaggo ta daka musu tsawa nan da nan suka kame kansu mubina da baki baya mutuwa a hankali tace “elephant kawai can’t you even say salam, ba wanda yaji abinda ta fad’a se yaron dan alhaji kabiru zama yayi suna gaisawa da gwaggo

Hura hanci yayi yana kukkumbura ita kuma ta kuma sakar masa gwalo ai kuwa yayo kanta tana dariya ta shiga zagayen gadon da Sam ke kwance,

Gwaggo ta kira sunan ta cike da warning duk suka kama kansu.

Alhaji kabiru yayi gyaran murya
 
yace “yaya inaga ya kamata kije gida ki huta yau haka”

“To kabiru wane ze zauna da yarinyar?”

“Um dama salamatu se tazo tunda likita yace ta farfad’o ‘kila zuwa gobe a bamu sallama”

“Au to Masha’Allah, amma tunda gobe ake tunanin sallamar gara na zauna, ita salamatu me tsohon ciki Ina zata iya?”

Ya jinjina kai “haka ne, Allah ya bata lafiya” ledojin daya shigo dasu ya ajiye gabanta “ga wannan fruits din zuwa dare zan dawo”

“Allah ya kaimu, ka shirya wurin da zata zauna d’in?”

“Eh! Na gyara mata d’akin kusa da nasu Amir har kayan ta duka an kai mata”

“To madallah a ri’ke amana dan Allah”

“Insha’Allahu yaya”

Ta kalli yaron “kai ubana Ina zaka kai tsokar nan taka, ka samma mubina da Sam mana gasu nan kamar a bushe “

“Ba mubina tana tsokana na ba ni ba zan sammata ba se de Sam”

“Kayi min daidai kuwa, kaga kwa rin’ka zauneta ai”

“Eh mana murin’ka yi mata John cena”

“Ni kuma nayi muku shoulder face”

Dariya gwaggo tayi ta kalli alhaji kabiru
Tana share kwalla tace “har na tuna yarintar ku da Ibrahim ke zaune ka”

“Kai kai haba yaya dan Allah a bar tuno baya, ni kinga tafiyata ma”

Tabishi tana ‘yar dariya, Amir na gaba yana baya suna fita ya waiwaya ya kalli d’akin yana me jinjina kai....

©Kdeey😊

DABAIBAYI (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now