26

978 102 4
                                    

DABAIBAYI 👄

©Khadija Ahmad (Kdeey)😊

®Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

                 (26)

_pray for me please ,..i'm sick🥺_

*kano state prison*

   Gidan masu laifi, wasu mata ke ta aiki a saman duwatsu, yayin da wasu ke zaune cincirindo guda suna hira wacce kashi 30/100 batsa ce, can gefe guda kuma wasu  ke yashe a qasa irin wayanda idan suka jigata suka yanke jiki su fad'i saboda tsananin gajiya.

Bulala ce riqe a hannun wata daga cikin masu basu tsaro tana shad'ad'a ma wasu daga cikin wanda ke yashe a qasa dan a ganinta qarya suke aikin ne basa so,

   Gefe guda umma salamatu ke zaune duk ta fita a hayyacinta wannan jikin duk babu d'an hasken ma yanzu babu shi se baqi da kayan qasusuwa, hannayenta tallafe da fuskarta hawaye na zuba daga idanunta girgiza kai tayi game da ajiyar zuci a fili take fad'in "oh ni salamatu×2 mahaifina ya yafe ni cikin yaransa tun sa'ilin da nayi wa matarsa dukan tsiya yace na bata haquri naqiya, mahifiyata shekararta shabiyar a cikin qasa, danginta duk sunqi waiwayo ni tun bayan da naci musu mutunci a tunanina tunda mijina nada arziqi to zan iya taka wuyan kowa, mijina maji'bancin al'amurana son duniya irin tawa yasa shi datse igiyar auremu d'aya , yaro na Ameer na d'ora shi bisa muguwar hanyata gashi ya 'bige a firsun, a yanzu haka banson a duniyar da yarana suke  ba, ko hajiya maryam data yi ikirarin ganin bayan su taci nasarar hakan? Ko kuwa?, kaico na ni salamatu son duniya ya kai ni tashar dana sani"

Wata iyamurar mata irin masu kula da masu laifi d'innan ta kalle ta tana girgiza kai dan taji duk abinda take fad'a, ciki da tausayawa

Tace "dukkan ku da kike gani anan shed'an ke rinjayar ku, gara ma ke kinsan zaki fita, da yawa anan sede a fidda gawar su? Kinga meye ribar kenan? Ina me baki shawara duk da bansan kalar lefin ki ba, da ki amfani da lokacin ki anan ki nemi gafarar ubangiji dan rayuwa yanzu ba ta da tabbas, mutuwa kuma  bata neman shawara"

Kukan tane ya dad'u, cikin sanyin murya tace "nagode da shawara insha'Allah zanyi yadda kikace d'in", tun kan ta rufe baki aka shiga qwala kiran batch C grp dinsu kenan, kallon matar tayi had'e da miqewa ta nufi gurin aikin da Allah kad'ai yasan ranar gamawa.

***
Hannunta biyu tasa tana jijjiga qofar cell d'in ciki karaji take fad'in
  "Ku bud'e min qofa nace! Tun kafin ku gamu da fishina, shin ko kunsan ni d'in wacece..."

"Her excellency hajiya maryam jamilu mainasara..or let me just call you kidnapper..tsk tsk tsk uwardaba suits you best.."

Ido, hanci, baki duk ta saki cikin rawar murya tace..." your excellency dan girman..."

"...dakata maryam!! Wullahi tallahi bazan ta'ba yafe miki ba har gaban abada! Kuma ki sani bawai zan sawaqe miki bane i will keep you hostage sede ki sani le da dabba a wurina babu maraba! Ki shirya abinda zeje yazo" da fad'in haka ya juya ya fice cikin qunar rai, Allah kad'ai yasan meke zuciyar shi.

Bayan kwana biyu...

  "Ammi duba yanda duk kika fita a hayyacinki dan Allah ki kwantar da hankalin ki..."

"Ann...mariya...tana raye cikin qunci da wahalar da Allah kad'ai yasan adadinta for almost 13 to 14 years ya kake ganin halin da zamu same ta ciki..."

"Ammi bro B yace she's fine and fine means fine insha'Allah, so please muje ki zauna a motor na janyo trolley mu tafi kada muyi missing flight"

Cikin zubar hawaye ta girgiza kai, shi kuma ya koma ya janyo kayan, bayan yasa cikin booth ya  nausa motar bisa kwaltar dake shimfid'e cikin company d'in.

Hannu tasa ta d'auka wayarta dake vibrating mss patricia tagani nan da nan ta murmusa kan ta qaga a kunne had'e da sallama

"Ammina.." ta furta in a  shaky voice,

"Sam my daughter, how are you?"

"Good, ammi kina lafiya?"

"Same here, i'm on my way to the airport"

"Airport? Ammi ina zaki tafi ki barmu?"

Ido ta lumshe cikin kukan zuci a fili kuwa cewa tayi "nigeria sweetheart zanje ganin bello i will be back in 2days insha'Allah"

"Ammi kizo muyi sallama pls inaso na ganki"

Hannu tasa ta matse idonta had'e da jan hanci ta kalli Ann, "can we make it? Ina so mubi ta saint teresa"

Kai ya d'aga tare da juya akalar motar zuwa titin da ze kai ka makarantar,

  "Gamu nan zuwa"

Kai ta d'aga kamar tana gabanta, ajiye wayar keda wuya munu ta fad'o d'akin, kallon mamaki ta bita dashi ganin tana ta faman cleansing face d'inta fara'a kwance saman fuskarta , tamkar ba ita ce ta bari kwance magashiyan ko lectures ta kasa zuwa.

Kula da irin kallon da munu ke mata yasa ta juya qwayar ido tace "fine  naji sauqin jiki na ne, and yes ina goge face d'ina coz banson Ammi ta ganni wani iri"

Ido wide open munu tace "is she coming.."

Kan ta bata amsa wayarta tashiga ringing nuna mata screen d'in tayi game da cewa "yes ta qaraso" light yellow veil kalar atamfar jikinta ta yane kanta dashi, tasa hannu ta amshe littattafen hannun munu ta ajiye game da jan hannunta sukayi waje.

Tun daga nesa yake hango fararan hakwaranta garai garai tamkar qanqara, murmushi yayi me kamar ajiyar zuciya yayi crossing leg d'insa daga tsayen da yake kusa da kujerar Ammi ya rungume hannun hagunsa a qirji yayin da hannun damansa ke tallafe da fuskar sa yana tapping hancinsa da yatsa (manuniya),

Na mujiya ya zuba mata from head to toe ya shiga qare mata kallo, takalmi ne flat sanye a qafarta shi ba lemon green ba haka kuma ba yellow ba, skirt ne pencil wanda ya fallasa dukkan wani curve na jikinta, yayin da  idonsa ya sauka saman rigar jikinta kuwa taune lips d'insa ya shiga yi game da had'e rai, lips d'inta dake kyallin farin lipbalm kuwa seda ya sashi d'auke wuta na wani d'an lokaci, idanunta da sukayi d'an jaja-jaja ya qurawa ido ta rame shine abinda  yayi crossing mind d'inshi bata da lafiya ne? Ba amsa , gaza d'auke idonsa yayi daga kanta sema gyaran murya da yayi yashiga amsa gaisuwar da suke masa,

Rungume take jikin Ammi suna sallama, bayan ta d'agata karaf sukayi ido hud'u, tsintar kanta tayi da son kallanshi wanda hakan yayi mutuqar faranta ransa ko banza he will be able to look into those white and black balls she's the definition of beauty zuciyarsa ra fad'a masa hakan a tare suka d'auke kai,

Ammi ta d'anyi dariyarsu irin ta manya, idonta a kan munu da itama ta kula da kallon kallo da suke,

"Munu zo ki raka ni gurin mss chloe mu gaisa kada tace nazo ban leqata ba"

Kai ta d'aga tana satar kallonsu, "Ammi bari na b..."

"No kuje muna jiranku" yace his eyes still fix on her's,

Tura baki gaba tayi idonta akan hanyar da suka bi,

  Yatsa ya d'alla mata saman lips ta saki wata kasalalliyar qara , cikin kunnenta yace "kinci sa'a Ammi is around da se nayi punishing bakin rashin kunyar" ido ya lumshe lokacin da hancinsa ya shaqi qamshin gashin kanta har be san lokacin daya furta

"Wani irin turare ne wan..nan?"

Dad'a runtse tayi kanta setin qirjinsa cikin sarqewar murya tace...

©Kdeey 😊

DABAIBAYI (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now