GABATARWA

175 12 2
                                    

Da Sunan Allah Mai Rahma Da Tausayi da Jin K'ai. Dukkan Yabo da Jinjina da Godiya Su Kara Tabbata Ga Masoyina, Madubina, Abin Alfaharina Manzon Allah Tsira Da Aminci Da Wasila Da Fadila Su Dauwama Tabbatatta Ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam. Yarda Da Tsira Da Aminci Su Tabbata Ga Ahalin Gidansa Da Sahabbansa Da Tabi'un Tabi'una Ila Yaumiddin. Amin

Wannan Labarin Gajerar Labari Ne (SHORT STORY) Daya Faru A Gaske ( TRUE LIFE STORY) Kuma A Cikin Garin Kano Wannan Labarin Ya Faru, Ban Yarda Na D'aura Alkalamin Rubutuna Kan Wannan Labarin Ba Sai Dana Yarda Da Inganci Da Gaskiyar Lamarin Kafin Na Yarda Zan Rubuta.

Kuma Ban Yarda Wani Ko Wata, Kungiya Ko Masana'anta Su Jiya Min Labari Ko Ta Wani Siga Ba, In Anyi Rashin Sa'a Labarin Yazo Iri D'aya Da Halinka/ Ki, To A Yi Hakuri Ni Dai Wannan Labarin Ba Kirkirarsa Na Yi Ba. Labari Ne Daya Faru A Gaske. Don Haka A Kiyaye!.

Na Canza Suna da Unguwar Da Abin Ya Faru Ne Saboda Kare Mutunci Had'e Da Martabar Ahalin Gidan, Amma Ba Zan Canza Garin Da Abin Ya Faru Ba Saboda Haka Na Tsara Labarin. Sa'annan Akwai Abubuwa Da Yawa Da Zan 'Boye Kuma Akwai Abubuwa Da Ni Marubuciyar Zan Rubuta Don Na Gyara Rubutun Kuma Na Kiyaye Martaba Da Mutumcin Gidan Da Abin Ya Faru, Amma Ku Sani Da Yawan Abubuwan Da Nake Rubutawa Tabbas Hakan Aka Yi, Kawai Ina Dan Kwata Labarin Ne Yadda Zai Zo Muku Da Dadin Karatu Da Kuma Saukin Karantawa.

Labarin Ya Kumshi Gidaje Guda Uku.
GIDAN ALHAJI SHAMSU
GIDAN BILKISU DA ABBAS
TSANGAYAR MALAM MAMMAN

Ina Fatan Zaku Biyo Ni Sannu A Hankali Don Ganin Wani Darasi Ne Ke Dauke Da Wannan Labarin.

ALHAJI SHAMSU: Uba Ne Ga Bilkisu. Wanda Kuma Ya Dauki Son Duniya Ya Daura Mata, Saboda Rashin Fad'arta Da Hayaniyar Yara 'Yan'uwanta. Yana Da Mata Biyu Da 'Ya'ya Biyar Kuma Bilkisu Ita ce Bubba Duk Cikin 'Ya'yan, Sannan Maza Uku. Hassan, Hussai Da Sani, Sai 'Yar Autarsu Halima. Gida Ne da Kawunan Matan Gidan A Had'e Yake, Hajiya Basira Ita ce Mace Ta Farko Kuma Tana Da Yara Hudu. Bilkisu, Hassan, Hussai, Sani (Gambo).
Sai Hajiya Rukayya Na Da 'Ya D'aya. Halima (Ni'imah)

BILKISU: 'Ya Ce Ga Alhaji Shamsu Sa'annan Mace Ce Mara Surutu Da Hayaniya, Ko Cikin 'Yan'Uwa Magana Ba Ta Dameta Ba Balle Hayaniya Irin Na 'Yan Mata.

Tana Da Karen Da Tun Yarantarta Suke Tare Har Girma Mai Suna Samba. Samba Kare Ne Da Tun Yana Yaro Bilkisu Ke Daukar Dawainiyar Ci Da Shansa, Haka Shi Ma Samba Yake Girmama Uwargijiyarsa Bilkisu. Tun Yana Karami Yake Jin Maganarta, Ko Da Laifi Ya Yi Da Ta Fara Fad'a Zai Sadda Kai Kasa Wannan Halamu Ne Na Ban Hakuri.

ABBAS: Almajiri Ne Daya Taso Gidan Almajiran Malam Mamman, Bai San Kowa Nasa Ba Sai Gidan Almajiran Malam Mamman. Abbas Yaro Ne Mai Kwazo Da Kaifin Basira Wannan Dalilin Yasa Tun Farkon Auren Alhaji Shamsu Da Basira, Ya Je Gidan Almajiran Dake Bayan Layinsu Don A Ba shi Almajirin Da Zai Dinga Taimaka Mata Da Aikace-Aikacen Gida Saboda Fama Da Laulayin Da Take Yi. Malam Mamman Kuma Ya Ba Shi Abbas Saboda Nutsuwa Da Hankalinsa, Tun Yana Zuwa Ya Dawo Har Dai Alhaji Shamsu Ya Roka Ya Dawo Gidan Gaba D'aya Kuma Ya Amince. Wannan Shi Ne Dalilin Dawowarsa Cikin Gidan Kuma Ya Zama Kamar D'an Gida. Sun inganta rayuwarsa da hasken ilimin addini da western gaba d'aya shi yasa bai ta shi cikin duhun jahilci ba.

Sun D'auke Shi Kamar D'an Da Suka Haifa A Cikinsu Domin Ba Sa Banbanta Shi Da Bilkisu, Sai Dai Kuma Shi A Can Kasan Zuciyarsa Tsana Da Hantarar Bilkisu Ne A Ciki, Domin Acewarsa Tun Bayan Haihuwarta Ne Suka Rage Soyayyarsa Kashi Tamanin Acikin D'ari 80% /100% Da Suke Mai. Amma Bai Taba Nunawa Ba Sai Dai In An Bar Mai Rainonta Ya Yi Ta Duka Da Tsungulinta, Rashin Hayaniya Da Rashin Maganarta Yasa Babu wanda Yasan Da Hakan.

Bai Taba Son Bilkisu Na Sakwan D'aya Ba Balle Minti D'aya, Sai A Gaban Iyayen Yana Nuna Ko Su Basu Kai Shi Sonta Da Nuna Mata Kulawa Ba, Har Aka Haifi Halima (Ni'imah) Kuma Da Ita Ce Kad'ai Bilkisu Ke Iya Zama Ta Fad'a Mata Damuwar Da Take Ciki Kuma Ta Gargad'eta Da Karta Fad'awa Kowa.

Soyayyar Da Yake Nunawa Yasa Alhaji Shamsu D'aura Musu Aure Domin A Tunaninsu Har Cikin Jini Da Bargon Jikinsa Yake Sonta, Kuma Ya Daura Shi Akan Sana'arsa Na Saro Kaya Daga Waje Zuwa Kasarmu Najeriya, Duk Abokan Karatunsa Ya Watsar Da Su Saboda Ya Yi Kud'i Ba Kamar Yadda Suke Ba Su A Yanzu Da Hannu Ke Dukan Cinya, Juya Kud'i Yake Yi Kamar Uban Shi Domin Alhaji Ya Sake Masa Ragamar Kasuwancin Shi Yasa Ya Daura Musu Aure. Sai Dai Tun Auren Ba Ta Da Kwanciyar hankali Har Kawo Yanzu Da Nake Gabatar Muku Da Su.

TSANGAYA: TSANGAYAR MALAM MAMMAN Gida Ne Dake Cike Da Yara Kanana Da Ma Masu Matsakaitar Shekaru. Abbas Na D'aya Daga Cikin Yara Masu Karamin Shekaru A Tsangayar Kuma Shi Ne Attajirin Mutumin Da Duk Shekara Sai Ya Kawo Musu Zakkar Hatsi, Wannan Yasa Ko Da Ya Ne Mi A Ba Shi Yaron Da Zai Taimakawa Matarsa Basira Da Aiki Malam Mamman Bai Yi Kasa A Gwiwa Ba Gurin Aika Masa Da Abbas, Saboda Nutsuwa Da Hankalinsa Kuma Da Rashin Sanin Iyayensa Na Asali Har Yanzu. Shi Yasa Tausayi Yasa Malam Mamman Turashi Gidan Don Yasan Za'a Rike Shi Da Gaskiya Da Amana.

Ina Fatan Duk Kun Fahimci Inda Alkalamin Basira Sabo Nadabo Ya Dosa Ko?

Na Yi Wannan Gabatarwar Ne Had'e Da Labarin Cast D'in Saboda Bana Bukatar Na Yi Gaba Kuma Na Dawo Baya.

Kuma Karku Manta Wannan Labarin Da Gaske Ya Faru A Cikin Jahar Ta Kano.

Basira Sabo Nadabo Ce

Wattpad: Basira_Nadabo
Facebook: Basira Sabo Nadabo
Snapchat: basirasabo
IG: Basira Sabo Nadabo
Email: basirasabo@gmail.com

DAN'ADAM (BUTULU)Where stories live. Discover now