35-40: GABA DA GABANTA....

57 8 4
                                    

Zaman Ni'imah a gidan ya mugun koyawa Abbas hankali kaɗan. Saboda duk wani mugun abin da yake wa Bilkisu ya ragu domin Ni'imah ba ta barinsa da ya ce kule za ta amsa masa kamar naƙuda, yanzu ma ya dawo ne daga jogging tun daga kofar falo yake kwala ma Bilkisu kira da sauri ta fito tana mutstsika ido haɗe da hamma. Tsayawa ya yi yana kallonta kamar ya ga sabon halitta.

'Lallai yarinyar nan ta samu guri har da barcin safe don tsabar iskanci har da kiba ta yi. To wallahi ba zai yuwu ba dole ta dawo kan duties dinta dole.'
         Da harara ya rakata da maganar zuci sannan ya ce.

"Ina 'yar iskar kanwarki.?"
      Da hannu ta nuna mai kitchen. Ita kuma Ni'imah ta yi tsaye a kofar kitchen ɗin cikin tsiwa ta ce.

"Wani ɗan iskar da bai gaji tarbiyya da albarka a gurin tsinannun iyayensa da suka yi zinarsa kuma suka jefar don suna gudun abin kunya. Wani bawan Allah ya dauke shi saboda tausayinsa da son 'ya'yan wasu kuma ya martaba shi haɗe da bai da shi mutum, bai tsaya nan ba har ya dauki mafi soyuwar 'yarsa ya ba sa don kawai nuna masa ƙauna amma yasa kafa ya yi fatali da shi. Abbas gani nan ko kana da abin yi ne da ni.?"
           Ba Bilkisu ba hatta Abbas sake baki ya yi yana kallonta domin rashin kunyarta ya wuce yadda yake tunani. Gurin Bilkisu ya koma ya hauta da faɗa.

"Wallahi ba zai yuwu a cikin gidana 'yar karamar yarinyar da na haifa a cikina ta dinga faɗa min magana son ranta ba. Dole Bilkisu ki zaba ita ko ni ko kuma na je na haɗaku da Abba tunda ni kun rainani kun mayar da ni ɗan iska wanda bai da ta cewa a cikin gidansa to ba zai taɓa saɓuwa ba dole ki zaba a yanzu, sa'annan kuma ki sani dolen dole ki dauki hukuncin rashin kunyar 'yar iskar kanwarki domin ba zai tashi a banza ba shegu 'ya'yan shegu."
          Ya shige ɗakinsa da sauri don yana gudun bakar maganar da zai fito a bakin Ni'imah. Gurin da Bilkisu ke durkushe tana kuka ta karasa haɗe da rikota tana rarrashinta da tsigar rarrashi ta ce.

"Ki yi hakuri Aunty wallahi duk mai hakuri yana dafa dutse har watarana yasha romarsa. Kuma ina mai tabbatar miki da izinin Allah komai ya kusan zuwa karshe, sai na maye gurbin kukanki da dariya, da yardan Allah kukan da za ki yi nan gaba na farin ciki ne amma ba bakin ciki da kuncin rayuwa. Aunty Bill rauninki yasa Abbas ke rainaki da wulakanta martaba da nasabarki, nasani da wuya tsoron Abbas yabar zuciyarki amma da sannu tsanarsa zai samu mazauni a ciki. Aunty Bill don Allah ki bar kukan nan ki buɗe baki kimin magana ko zan ji daɗi hankalina ya kwanta kin ji.?"
            Jin ihun Abbas ne yasa Samba ya shigo falon direct gurin uwargijiyarsa ya nufa ya karkaɗa bindinsa.

"Kin ga Samba shi ma hakuri yake baki. Aunty Bill kibar kukan nan mana.!"
           Allah bai yi Ni'imah mace mai saurin kuka ba domin da tana da yawan kuka kamar Bilkisu to da tuni Abbas ya samu lagonta amma tana da juriya.

"Ni'imah don Allah ki taimaka min ki koma gida yau ina gudun dukan da Abbas zai min.!"

"Ki yi hakuri zan koma gida amma ba yau ba koma me zai miki ya yi mana tare don ba zan iya barinki a cikin wannan halin ba."

"Ke fa kanwata ce kuma autar gidanmu yanzu shikenan don ba ni da girma a idanunki sai kika yi fatali da rokon da na yi miki ko? Na gode Ni'imah."
       Da tausayi Ni'imah ta bita saboda tasan tabbas wannan maganar daga fatar bakinta ya fito amma ba a zuciyarta ba, zuciyarta ce ta yi mata nauyi don ba ta so wannan yaƙin ya tsaya iya nan ba, tafi bukatar kafin tabar gidan sai ta gyara mai zama kuma ta samarwa da 'yar'uwarta farin cikin da ta rasa a gidan aure. Kitchen ta koma don karasa abincin da ta daura sannan ta dafawa Samba abincinsa haɗe da zuba masa madararsa ta kai masa abincin ɗakinsa sannan ta dawo ta ci na ta ta koma ta tarar da Bilkisu zaune ta haɗa kai da gwiwa. Tana jin Ni'imah ta shigo ta yi saurin daga kanta tana kallon Ni'imah, ita kuwa ɗauke kanta ta yi ko kallon inda Bilkisu take ba ta yi ba ta faɗa toilet ta yi wanka ta fito ta shirya, kayanta da ta zo da shi ta mayar jikinta sannan ta ce.

DAN'ADAM (BUTULU)Where stories live. Discover now