Tun bayan fitar Ni'imah take tsugunne cikin fargabar abin da zai biyo bayan tijarar da Ni'imah ta yi masa. Tsintar kansa ya da kasa ci gaba da cin abinci ya yi zuciyarsa cike da fargabar kalamanta, zufa ke tsatstsafo masa ta ko wani kafar gashin jikinsa, balle maballin rigars yai haɗe da barin falon gaba ɗaya.
Bayan isarta gidan ne ta ci abinci haɗe da kwanciya tana tunanin halin da ta baro 'yar'uwarta a ciki da kuma fargabar tambayoyin Umman Ni'imah.'Allah ka tsare min ita daga mummunar kudirin Abbas akanta.'
Bubbugatan da Umma ta yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunaninta haɗe da neman guri ta zauna kusa da 'yarta . Da fargaba a zuciyarta ta ce."Don Allah Mamana ki daure ki faɗa min halinda kika bar 'yar'uwarki a ciki ko na samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciyata! Tun bayan da Alhaji ya faɗa mana zaki kwana biyu a gidan Bilkisu hankalina ya kasa kwanciya.!"
Ta riko hannun Ni'imah hawaye na tsurnanowa a idanuwanta ta ce."Mamana jikina da dukkan mafarkaina na faɗa min Bilkisu na cikin mummunar hali a gidan mijinta, har yanzu zuciyata taka amince min da Abbas. Fargabana a kullum kara karuwa yake yi akansa sannan jikina na bani cewa nan kusa komai zai zo karshe! Sai dai karshen ne ban san a yadda za ta zo min ba. Da zaki daure kuma ki taimaka 'yar'uwarki ta fito daga wan can gidan na kunci da kin gama yi min komai a duniyar nan don Allah.!"
Zuciyarta ke ƙuna wutar tsanar Abbas na daɗa ruruwa a ƙasan zuciyarta sa'annan ga shi a dalilin shi Umma take kuka. Daurewa zuciyarta ta yi tare da ƙara karfafa masa gwiwa ta ce."Ummata zuciyarki da jikinki suna faɗa miki ƙarya ne domin Aunty Bill tana cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali. Kuma abin da ya sani kwana biyu can saboda ta ce kaɗaici ya isheta kuma tana son na zauna da ita na kwana biyu, kuma muna shakkar Abba shi yasa muka yi masa karyar rashin lafiya amma lafiyarta kalau. Ummata a ɗan zaman da na yi na fuskanci Ya Abbas mutumin kirki ne kuma yana son Aunty Bill har wani kulawa ta musamman yake nuna mata akan idanuna, kuma Umma abin da zai baki mamaki shi ne ita Aunty Bill ce ke ɗaga hankalinta wai don ba ta haihu ba har yanzu. Sai Ya Abbas ya kwantar mata da hankali fa take hakura da kuka da sa damuwa a zuciyarta, don haka Ummata ki yi hakuri babu abin da zai faru in ma karshen kike son gani In Shaa Allahu mai kyauce, ni ma jikina na ba ni kyakkyawar karshe ne da shi yardan mai duka Azza Wa Jallah.!"
Murmushi kawai take yi amma zuciyar taki yarda ta amince da kalaman kwantar da hankalin da Ni'imah ke mata. Har yanzu zuciyarta na faɗa mata ƙarya ce kawai Ni'imah ke faɗi don dai kawai hankalinta ya kwanta ne, ɗaga hannu sama ta yi sannan ta ce."Rabbi Sarkin iko ka nuna min ikonka a cikin rayuwar Bilkisu! Allah ni ce na ɗauki cikin da ɗawainiyar wahalarta tun daga sati har shekara da wata ɗaya. Saboda tausayi irin na ka Allah kasa min doguwar naƙudar da sai da nai kwana uku ina wahalarta, ka samin salamar kin yarda da aiki a ciro baiwarka Bilkisu Ya Allah. Na haifota haɗe da matsalolin haihuwa kala-kala kuma na jure don kawai na tayaka kiwon baiwarka Ya Rabbi! Kasa ta zame min mai sauki gurin shayarwa saboda rashin kuka da karaniyar 'yan yara, ta girma ka haɗata aure da mutumin da kaso don shi ne abokin rayuwarta. Ban yi gardama ko kuma na tuhume ka na ce don me ka yi hakan ba kuma ba shishshigi zan yi a rayuwar aurensu ba Allah! Sai dai ina rokonka kamar yadda ka ce addu'ar mahaifiya karbabbiya ce kuma na tabbata za ka amsa addu'ata. Allah ka kawo karshen wannan auren da babu komai a cikinta sai ƙunci da muzgunawa, Allah ka shigo lamarin Bilkisu ko zuciyata za ta daina fargabar halin rayuwar da take fuskanta Ya Rabbi ka amsa min Ya Ƙadir.!"
Da kuka ta karashe maganar, da Amin Ni'imah ta amsa zuciyarta na kuka idanunta na zubar da hawaye masu ɗumi..
