Shuru-shuru yai ta zaman jiran tsammanin kira daga Abba ko a kasuwa ko gida saboda yasan dai wannan mara kunyar ba za ta yi shuru da bakinta ba. Ga shi a wannan watan kayan da suka yi oda zai karaso kasar sa'annan in har Alhaji ya ɗaura shi akan wannan business ɗin, ba karamin matashin mai arziki zai zama ba domin akwai alheri sosai a harkar. Murmushi ya yi haɗe da shafa gemunsa da hannunsa na hagu sannan ya ce.
"Da kyau Abbas. Da kyau gaye kwakwalwarka tana ja kamar mayen karfe, wai yau ni ne na yi kuɗi ina sai manyan motoci 'yan yayi. Na gina babban gida irin na kasar misrah, na auri kyawawan 'yan mata guda huɗu sa'annan na rabu da 'yarsu sai in ga abin faɗi kuma dole a dawo karkashina ana neman taimako. Ni kuma a lokacin zan rama duk abin da suka min, shi kuma Shamsu da ya ba ni 'yarsa wai don ya birgeni to ni a gurina ba komai ya yi min ba sai nuna tsanarsa a gareni."
Ya ja tsaki haɗe da dunkule hannu tare da maushin dayan hannun.
Yau kwana uku kenan Bilkisu na jiran dukan Abbas amma shuru har wani soyayya yake nuna mata ta ƙarya. Kaya iri-iri na kwalliyar zamani 'yan yayi yake siyo mata ya kawo mata duk saboda ta canza a 'yan lokutan kuma Abba ya yarda da gaske yake kula da nuna mata soyayyarsa, sabon halayyar da Abbas ke nuna mata yabar ba ta mamaki musamman da ya zaunar da ita yana kuka ya ce."Nasani kuma nasan ni mai laifi ne Bilkisu don Allah ki dubi girma da zatin Allah ki yafe min. Wallahi na canza daga Abbas ɗin da kika sani wannan wani sabon Abbas ne mai sonki da ƙaunarki ke tsugune a gabanki."
Ya yi saurin riko hannunta da rawar murya ya ce."Don Allah ki yi min rai ki yafe min domin inhar baki yafe mij ba tabbas rayuwata tana cikin garari kuma wutar jahannama ce makomata."
Ya sassauta murya kasan zuciyarsa farin ciki ne fal domin tarkonsa fa fara kamawa don jikinta ya yi sanyi harda hawaye tsammaninta da gaske ɗin ya canza kuma rokon da yake mata daga zuciyarsa take fitowa ba iya fatar bakinsa ya tsaya ba. Da sassauciyar murya ya ce."Matata Bilkisu don Allah ki yi min rai! Ki taimaka ki yafe wa wannan azzalumin mijin na ki dake neman gafararki. Matata a yanzu rahama da gafarata tana nan duniyar suna hannunki in kin yafe Allah ma zai yafe min in kuma ba ki yafe min ba Allahn da ya halicceni zai cigaba da fushi da ni kuma ba zai taɓa yafe min ba.!"
Ya fashe da kuka har da bubbuga kansa a jikin kujera. Bilkisu kuka take yi da gaske murna ya cika mata zuciya da sauri ta kamo shi, sai ta ji wani iri ta yi saurin sakinsa da sanyin muryarta ta ce."Ka taimaka ka daina bubbuga kanka a jikin kujerar kar ta ji maka ciwo."
"Ni har mutuwa zan iyayi akanki matata muddin ba za ki yafe min ba."
Hawayen farin ciki na surnano mata ta ce."In dai don ta ni ce na yafe maka, kai ma ina rokon yafiyarka don Allah nasan ni ma mai laifi ce a gareka."
Saurin riko hannunta ya yi haɗe da zama a kujerar da take zaune. Matsawa ta yi daga yadda ya manne a cikinta, murmushi ya yi a zuciyarsa sa'annan ya ce."Ba ki yi min komai ba kuma in ma kin min bisa kuskure to ni na yafe miki duniya da lahira."
Duk yadda ya so ta sake jikinta abin ya faskara domin kallon sabon halitta take yi masa. Zuciya da gangar jikinta na faɗa mata wannan canjin ba har cikin zuciyarsa ba ne saboda yau sati biyu kenan da yake ce mata shi da ita har abada kuma jira yake ya samu yadda yake so ya saketa ya aure 'yan mata kyawawa masu dogayen kafa da wuya ya aura, saboda ita ba ra'ayinsa ba ce cucenta aka yi mai kuma har ya koma ga Allah ba zai taba sonta ba.
Da sauri ta kauda tunanin saboda babu yadda Allah bai yi da mutum a ko wani lokacin da ya so yakan canza mutum cikin ikonsa kuma ya canzu. Da wannan shawarar ta kau da tunanin da ɗayar zuciyarta ke mata, kuma ta ɗauki na wanda zuciyarta ke nuna mata iko da zatin Allah da haka rabin zuciyarta ta yarda da shi. Haka ya ci gaba da janta da hira amma ta kasa ganin ya taki sakin jiki ya sa ya koma ɗakinsa har ya buɗe kofar ya leko da kansa ya ce.
