Da murna ya koma gida domin haƙonsa ta cinma ruwa kuma ya zura Abba cikin duhun kogo mai cike da kunamu da macizai jiran kururuwan ihunsa da neman agaji, Shi kuma a lokacin zai juya masa baya sa'annan ya sa marufi ya rufe kogon ramin. Don babu taimakon da zai yi masa domin shi ma da yana sonsa da bai yi wa Bilkisu soyayyar da yake mata ba da har bai iya ɓoye soyayyarta ko a gaban waye, tabbas shi ma zai yi amfani da ita don cinma burinsa da sannu zai gane waye shi kamar yadda Ni'imah ta ce za'a yi kuma za a ganshi to shi kafin a ganshi zai rigasu ganinsu. Da wannan tunanin ya karasa gidan tana zaune ta yi kwalliya abin da ba ta taɓa yinsa don birge mijinta, atampa tana mai ruwan bula da ruwan kai sai ratsin fin kala a jiki, ɗaurin Zara Buhari ta yi fuskar nan ta yi kwalliya babu laifi na fito jinin fulanin usul, cakulati kala ce tana da manyan idanu da dogon hanci har baka sannan gashin idanuwanta masu tsawo tare da ɗan rankwafawa sun taimaka matuƙa gaya gurin ƙa wa ta kyawun fuskarta. Bakinta fin kala ne ɗan ƙarami madaidaici da ɗaukar hankali, dogon wuyanta ya yi daidai da faɗin kirjinta da ya cika da arzikin fulani, cikinta da bayanta kusan a haɗe suke don babu tasawa ko halamun tunbin da zai ta da rigarta, kugunta mai faɗi ne daidai da jikinta sa'annan tana da mazauna masu ɗaukar hankalin maza. Sannan santala-santalan kafafuwarta a tsaye suke wanda a turance ake cewa straight legs, fatar jikinta mai kyau da ɗaukar hankali banbancinta da Ni'imah kaɗan ne ita fara ce sa'annan doguwa ce mai yawaltaccen gashi don tafi Bilkisu dogon gashi mai mai silki, sannan ta fi Bilkisu wayewa da masifa kuma ta fita gogewa a bokonce don ita yanzu haka masters take haɗawa a BUK tana karantar tattalin arziki Economics, yayinda Bilkisu kuma iyakarta Degree a har kar kasuwanci wato Business Administration. Kuma dukkan su Alhaji Shamsu suka ɗauko musamman Bilkisu da kamaninsu kamar an tsaga kara da shi sai dai jikin ne ta ɗauka na Hajiya Basira shi kuma Alhaji Shamsu kana ganinsa ka bafulatinin usul saboda rashin jiki da tsawo sa'annan ga wadataccen arziki. In taƙaita muku dai gaskiya a kyawawa ne su.
Da sallama ya shigo gidan hannunsa ɗauke da bakar ledar da ko ranar aurensu bai shigo da ita ba, murmushi a fuskarshi ya nuna gareta da sassarfa ya rungumeta haɗe da manna mata kiss a forehead sannan ya manneta a jikin shi wani nutsuwa ke saukar masa wanda bai taba fuskartar irinta ba. Haka ita ma Bilkisu wani shork ta ji a lokacin da ya rungumeta nutsuwa da daidaituwar bugun zuciyarta ne suka tabbatar mata da lallai Abbas ya shiryu. Godiya ta yi wa Allah ta kuma roƙi Allah ya dauwamar da su a wannan yanayi mai daɗi da wuyar gogewa a littafin zuciya. Janye jikinsa ya yi yana kallonta tun daga kai har ƙafa kuma tun da yake da ita sai yau ya kalleta da kyau shi kan shi zuciyarsa ta amince masa da lallai ilallah Bilkisu kyakkyawa ce kuma matar nunawa sa'a ne.
Zaunar da ita ya yi ya nufi kitchen plate ya dauko guda ɗaya da tamblan ɗaya, tana tsaye a inda ya barta jikinta a sake saboda soyayyarsa mai kashe jiki da kunna ilahirin igiyoyin wutar lantarkin da ke assasa zuciya, zaunar da ita ya yi sannan ya juye musu gasasshiyar kazar hausa da yoghurt na Rufaida. Ba ta yake yi tun tana kin karɓa har ta saki jiki da shi, bayan sun yi nak ya ce ta shirya su je gida, murnarta ya gaza ɓoyuwa sai take ji kamar yau ne zuwan su na farko gidan tare.
Gyara fuskarta ta yi sannan suka fito gwanin sha'awa. Murnar fuskarta ya gaza ɓoye kyawawan hakwararta sa'annan zinarin haƙorin dake jerin haƙorarta sai haske yake yi, ajere suka shiga gidan lokacin Abba na ƙasa da sauran yaran gidan duk suka zubo musu ido ban da Ni'imah da ta yi musu kallon farko ta watsar. Bayan gaishe-gaishe ne Umman Ni'imah ta ce."Yau kuma wani sabon abu nake gani Yaya sai na ga kamar idanuna na nuna min murmushin 'yata Bilkisu suke yi?"
Hassan ya yi saurin cewa.
