A hanyarsu ta zuwa gida ne ya tsaya ya yi musu siyayya sosai don duk wanda yake gidan sai da ya yi masa tsaraba. A kofar gida suka yi parking saboda dalilin kansa, tun daga harabar shiga cikin gidan nutsuwa da kamala suka dirar masa, sai nuna mata kulawar wucin gadi yake yi kamar zai maida ta cikinsa don tsabar so da kaunar da yake nuna wa a gaban iyayenta. Ta kasa kaucewa idon Ummanta a kanta domin duk yadda taso karsu haɗa ido amma hakan ya ci tura, shi kuma sarkin yaudarar sai sadda kai kasa yake yi kamar sabon amarya, bakon ladabinsa bai taba damunta ba domin in dai a gaban iyayenta ne musamman gaban Abba kamar ba zaka saka mai ɗan yatsa a baki ya gatsa. Yanzu ma zaune yake a gaban Abba ya dauko ladabin duniyar nan ya daura a kanshi cikin ladabi da biyayya yake yi wa Abba bayanin nasarar da ake samu a harkar kasuwamcinsu, ya ɗaura da roko cikin hikima yake cewa.
"Abbas kasan kai ne babba a gidan nan sannan kana auren ɗaya daga cikin 'ya'yan gidan nan kuma mafi soyuwar 'ya a cikin 'ya'yan da Allah ya ba ni don haka nake rokonka da ka yi hakuri da ita. Saboda har gobe Bilkisu yarinya ce da ba ta wuce in ta yi laifi a yi mata faɗa da nuna mata kuskurenta, nasan Bilkisu sa'annan nasan zurfin ciki irin na ta kuma ka ga ba yarinya ba ce mai hayaniya don haka nake rokonka a kullum da ka kular min da ita, kuma ka wadata da abubuwan bukatuwa don in akabi na Bilkisu to fa sai dai ku shekara bata buɗe bakinta ta ce ga abin da take so ba. Don Allah Abbas ka riketa amana karka bari kunci ya addabi zuciyarta.!"
Ya karashe maganar da rawar murya kamar zai zubar da kwalla. Shi kuwa Abbas tunda Abba ya fara maganar Bilkisu ƙunci da tsanarta ke kara ɗarsuwa a zuciyarsa, ɗaci yake ji a kasar zuciyarsa amma babu yadda zai yi ya nuna. Da kyar ya tattaro nutsuwarsa da yaudararriyar ladabinsa dake ƙara siye zuciyar sirinkansa ya ce."In Shaa Allahu Abba za ka sameni da yin biyayya ga kalamanka. Kuma ko babu komai ai Bilkisu kanwata ce, ni mai iya tsaya mata a rayuwarta ne har sai na tabbatar da ta samu jindaɗin rayuwa."
Gyara zama ya yi haɗe da tankwashe ƙafa har ila yau kanshi a kasa ya cire hular kansa ya ce."Abba Bilkisu kanwata ce kuma ina riketa da gaskiya da amana sai dai kasan mutum tara yake bai cika goma ba. Abba ban san me ke damun Bilkisu da kullum take ramewa, zurfin ciki da rashin maganarta ke damuna Abba. Ga shi ta dauki rashin haihuwar da ba ta samu ba ta saka cikin ranta sai ramewa kawai take yi, na yi mata faɗa, na yi rarrashin, na yi fushi duk a banza. Abba har abincinta na daina ci duk saboda ta gyara amma har yanzu shuru Abba!"
Da rawar murya ya karashe maganar har ya na goge kwalla. Tausayinsa ne ya dirarwa Abba haɗe da wutar soyayyarsa na ƙara ruruwa a ƙasan zuciyar Abba."Ka kara hakuri Abbas don nasan kana hakuri da halayyar Bilkisu saboda ita haka Allah ya yi ta tun tana jaririya kai shaida ne. In ka ji kukanta da hayaniyarta to tabbas hakurinta ne ya kare amma a wannan gaɓar kai ke hakuri da ita Abbas kuma ina ƙara ba ka hakurin dai don Allah."
'Wato su mutanen nan kullum 'yarsu ita ce 'ya ni kuma tunda basu haifeni ba ni ba ɗa ba ne kenan? Wannan abin da suke mata ke ƙara min tsanarta kuma wallahi yanzu nasa ƙafa gurin muzguna mata don ita ba ta isa na yi hakuri da ita ba sai ita 'yar taku ta yi hakuri da ni shegiya 'yar shegu.'
Ya karashe maganar zucin da kwafa. Abba ne ya taba shi haɗe da cewa."Lafiya ina ta magana ka yi shuru ko har ka fara gajiya da halin Bilkisun ne.?"
Yaƙe ya yi ya ce.