85-90: SAMBA

47 7 5
                                    

Bayan ya tabbatar da mutuwarta ne ya yi dariya haɗe da cewa.

"Ki je can ki jira iyayenki domin na tabbata nan kusa ubanki Shamsu zai biyo bayanki sannan uwarki Basira ta biyo baya da sannu kuma zan turo miki mara kunyar ƙanwarki da uwarta Rukayya, 'yan tagwaye da Gambo kaɗai zan bari su ma ɗin don kawai na ga yadda rayuwarsu za ta tagayyara ne zan kyale su."
          Kuka Samba yake yi kamar zai shiɗe haka yana ganin gawar Bilkisu kwance gaban Abbas ba motsi komawa gefe ya yi yana kallonta, fita Abbas ya yi zuwa waje ya ɗauki lokaci mai tsawo kafin ya dawo yana dawowa ya cicciɓeta zuwa waje. Da sauri Samba ya bi shi zuwa wajen rami ya haƙa ya turata ciki ya yi sannan ya mai da kasar ya rufe, gurin kabarin ya koma ya kwanta yana zubar da yawu da farko ya so kashe Sambar ban san tunanin da ya yi ba ya kyale shi. Falon ya koma ya gyara gurin tare da goggoge bangon ɗakin da yake irin bangon man nan ne yasa bai sha wahala gurin goge jinin ba, nan da nan komai ya dawo fes turaren tsinke da na wuta ya jona gidan ya ɗauki kamshi. Kayansa da ya ɓaci da jini ne ya cire ya tura a leda ya jefar a bayan gidan gurin kabarin Bilkisu.

       Acan gidansu Bilkisu kuwa Umma ce bugun zuciyarta ya tsananta sannan lokaci zuwa lokaci Bilkisu tana faɗo mata a rai. Yau kimanin sati ɗaya kenan tana fama da faɗuwar gaba da mugayen mafarkai akan Bilkisu, ɗakin Abba ta je bayan ya dawo daga kasuwa cikin damuwa sakamakon recoding ɗin da Faisal ya kunna masa ya ji. Kuma ba yau ya saba kunna masa makamanciyar wannan recording ɗin ba shi yasa hankalinsa ya kasa kwanciya, sa'annan ga faɗuwar gaba da yake fama da ita tun safe a duk lokacin da ya tuna da Bilkisun. Zaune ta same shi ya yi tagumi ya rasa dalilin da duk bayan mintuna da sakwanni sai ta faɗo masa a rai, zama kusa da shi ta yi sannan ta ce.

"Alhaji lafiya?"
            Janye tagumin ya yi tare da cewa.

"Lafiya lau Hajiya me kika ga ni.?"
             Ta ce cikin damuwa.

"Na ga kana cikin damuwa ne."
            Murmushin karfin hali ya yi sannan ya ce.

"Bakomai Hajiyata sai dai ke ce ɗin fuskarki ta nuna min kina cikin damuwa a 'yan kwanakin nan har rama kika yi fa."
            Hawayen da take ɓoyewa ne suka surnano ta ce.

"Alhaji Bilkisu.!"
      Sai ta yi shuru ta cigaba da kuka, jikinsa ya janyota sannan ya ce.

"Me ya samu Maman tawa.?"
       Sai da kukan ya tsagaita ta ce.

"Na rasa dalilin faɗuwar gabana da yawan tunaninta da nake yawan yi a yau ɗin nan saboda na yau yafi na kullum Alhaji.!"
         Sauke ajiyar zuciya ya yi tare da cewa.

"Ni kaina da wannan matsalar nake kwana na tashi amma ki bari tun da gobe Juma'a sai mu je mu kai mata ziyara."

"Har sai gobe Alhaji.?"
                     Ya ce.

"Hakuri zaki yi Hajiya saboda akwai ganawar da zan yi da yaran shagona amma In Shaa Allahu goben sai mu je mu gaisheta da duba lafiyarta kin ga sai hankalinmu ya kwanta."
             Ba don taso ba ta amsa da to. Da sauri Hajiya Rukayya ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama ta ce.

DAN'ADAM (BUTULU)Where stories live. Discover now