1-10: KAWALWAINIYA!

110 10 0
                                    

Kuka take yi kamar ranta zai fita amma babu halin kai kara gida domin Abbanta ya dauki so da yardar duniyar nan ya mikawa Abbas, kuma yarda da shi ne ya sa ya bata shi a matsayin mijin aure. Karenta dake gefenta ne ke ta kuka kamar yadda uwargijiyarsa ke yi, shafa kanshi ta yi cikin raunanniyar murya ta ce.

"Ka yi hakuri Samba watarana zai zama labar domin jikina na bani watarana Abbas zai daina abin da yake yi."
Kamar karen ya ji abin da take faɗa ya yi shuru haɗe da kara shigewa cikin jikinta.

"Samba ka ga takalmina can yi maza ka dauko min."
Da gudu ya tashi zuwa kofar falon dakin ya dauki takalmin da baki ya zo ya ajiye a gabanta ya kuma komawa ya dauko ɗayan sawun takalmin ya ajiye mata, kwanciya ya yi agefenta ya fitar da harshe waje yawu na zubowa, da ganin hakan ta gane yunwa ce ke damun Samba. Da tsamun jiki ta nufi kitchen don daura sanwar abincin safiya kafin Abbas ya dawo daga jogging, source ɗin miyar hanta da cabbage ta yi sannan ta soya dankalin turawa daidai cikin Abbas saboda ita a yanzu ba ta jin yunwa. Sa'annan ta daurawa Samba abinci ta juye mai a plate dinsa sannan ta tsiyaya masa tashashshiyar madara, nan da nan Samba ya shanye saboda jiya da yunwa ya kwana sakamakon dukan da Abbas ya yi wa Bilkisu akan kuskuren da bai taka kara ya karya ba, gefen kafarta ya je yana shafa mata kafa da kanshi tare da lashe mata kafar dama. Wannan ɗabi'ar Samba ne duk lokacin da ta ba shi abinci sai ya nuna godiyarsa ga duk wanda ya kyautata masa. Cikin muryar da tasha kuka ta koshi ta ce.

"Ka yi hakuri Samba jiya ka kwana da yunwa saboda jikina na min ciwo ban iya ɗaura maka sanwa ba, iya cikin Abbas kawai na dafa ina fatan zaka yafe min ka ji Samba.?"
Haushi ya yi sannan ta ci gaba da cewa.

"Samba nasan kana jin abin da nake faɗa kuma kana ganin azabar da Abbas yake min a gidan. Amma zuciyata ba za ta iya kai kararsa gida ba saboda ko na faɗa babu mai yarda da ni! Kai shaida ne a kaina Samba! Ban taɓa yin abinda zai muzguna rayuwar Abbas ba, komai nake yi don gudun bacin ransa! Samba ina kiyaye lokacin cin abincinsa da muhallinsa! Ban taɓa barin Abbas da yunwa ba amma ya zabi ya muzguna min don kawai sanadiyar haihuwata Umma da Abba suka rage soyayyar da suke masa! Samba don Allah laifina ne? Laifina ne da aka haifeni? Ko ni ce na ce Umma su daina sonsa? Samba ka faɗa min me na yi masa wanda in na daina Abbas zai daina dukana da hantarata? Don Allah ka faɗa min Samba!"
Ta fashe da kuka mai cin ran mai saurarenta, Samba ma kukan yake yi ta hanyar haushi da karfi yana karkaɗa jelarsa. Rungumarsa ta yi tana shafa bayansa cikin kuka ta ce.

"Mu yi hakuri Samba nasan Allah yana kallon duk wanda aka zalinta kuma shi ne zai saka min. Kuma ko a mafarki ban yarda ka rama abinda yake min ba domin in ka cije shi kaina komai zai dawo, ka yi hakuri Samba ni ma hakurin nake yi."

"Gara ki gargaɗe shi domin daga ke har shi ba fin karfina kuka yi ba kuma wallahi a shirye nake dana kashe tsinannan karen nan a duk ranar da ya yi kokarin ɗaukar miki fansar abinda nake miki shegiya mai shegen halin uwarta."
Jin maganarshi ta yi daga bayanta da sauri ta waiwaya cikin firgici haɗe da ƙanƙame Samba hawaye masu ɗumi na gangarowa a fuskarta ta yi saurin sharcewa kafin Abbas ya gani ya kara nakaɗa mata na jaki. Cikin kakkausar murya ya ce.

"Kuma ina mai umurtarki da ki tashi ki shirya don zamu je gaisuwa a gida sannan ina kara gargaɗinki da wallahi ko da wasa kika ce ga abin da nake miki a gidan nan. Na rantse da Allah na lahira sai ya fiki jindaɗin rayuwa, ke sai kin gwammace mutuwarki da rayuwa da ni. Shegiya matsiyaciya mai mugun zuciyar uwarta."
Rumtse ido ta yi da sauri saboda a duniyar azabar Abbas da yake gasa mata aya a hannu babu kalmar da ta tsana kamar zagar mata uwa, uwar da ta ɗauke shi kamar ɗan da ta haifa a cikinta amma shi a gurin shi babu wacce ya raina irinta. Da sanyin jiki ta tashi zuwa ɗakinta ta gasa jikinta da ruwan zafi sannan ta yi wanka haɗe da ɗauro alwala, bata da gurin kai kuka daga Allah mahaliccinta sai Samba da Ni'imah duk da bakomai take faɗa mata ba kamar yadda take faɗawa Allah kullum dare da rana, haka shi ma Samba bata gajiyawa dai da faɗa mai damuwarta. Wata rana su haɗu su yi ta kuka babu mai rarrashin wani haka zasu yi kukan har sai sun gaji dan kansu. Hannunsa ɗauke da kular da na zuba masa miyar source ɗin da ta yi masa ya shigo ɗakin kirjinta sai bugawa yake yi, ajiyewa yai sannan ya koma ya dauko ɗayar kular dankalin ya dawo zama ya yi tare da juye duka dankalin a plate, haka miyar ma ya juyata duka asaman dankalin ya cakuɗa haɗe da tura mata gabanta. Ya tamke fuskarsa ya yi kamar wanda bai taba dariya ba, da ma ita ba ganin dariyarsa take yi ba amma wannan fuskar da ya ɗaura ya firgita ta sosai ya ce.

"Bilkisu zauna ki cinye wannan abincin duka domin ban gaji asara ba kuma ba za a min asarar abin da sai na fita na sha wahala nake nemowa. Ban taɓa barinki da yunwa ko kishir-ruwar da zaki sha ba, haka ban ce dole sai kin dafa abin da nake so ba tunda ba haka na tashi gidan ubanki uwarki ke yi ba don haka ki zauna ki cinye wannan kazamin abincin da kika yi na ci."
Cikin rawar murya ta fara ba shi hakuri.

"Don Allah ka yi hakuri Ya Abbas wallahi na koshi in na ce zan ci wannan abincin mutuwa zan yi! Ka yi min rai Ya Abbas karka tursasani na ci wannan abincin.!"

"Wallahi Allah Bilkisu sai kin cinye abincin nan don tsabar bakin mugunta ki rasa abin da zaki min da safe sai wannan kazantar, saboda kin rainani kuma kin tashi kin ga yadda uwarki ke raina ubanki shi ne ni ma za ki min a nan gidan ko? To wallahi kin ji na rantse sai kin cinye kazantarki."
Mikewa ya yi haɗe da fita bai dauki lokaci ba ya dawo hannunsa ɗauke da belt, tana ganin haka ta yi saurin tsugunawa gaban abincin tana cusawa a cikinta yayinda da hawaye kuma ke tsiyayowa daga idanunta. Bai bar ɗakin ba sai da ta cinye abincin tana yunkurin amai, yana fita kuwa ta amayar da duk abin da ta ci kela aman take yi kamar za ta amayar da 'yan hanjinta.

DAB....

BSN Ce.

DAN'ADAM (BUTULU)Where stories live. Discover now