Washe gari tun da asuba ta shiga kitchen domin yin morning duty ɗinta kamar yadda a kullum yake faɗa mata ne. Ko da kuwa ba zai ci abincin da za ta dafa a safiyar ba yana son ta shiga kitchen ta yi girki, yanzu ma zaune take ta zubawa abincin ido saboda yasan ɗan wake ba abin cinta ba ne amma don bakar mugunta ya ce ta dafa kuma karamin aikinsa ne ya ce ta cinye. Samba ne ya shigo kitchen ɗin ya na haushi da sauri ta sauko daga kujerar da take zaune ta nufi falon da sauri domin in an yi bako hakan shike nuna mata ta yi baƙi, Ni'imah ce zaune a ɗaya daga cikin kukerun falon tana ganin Bilkisu ta mike da haɗe da cewa.
"Surprise!!!"
Murmushi Bilkisu ta yi sannan ta ce."I don't like surprises."
"Ni wallahi Aunty Bill ban san yaushe za ki waye ba ga mijinki dan gayu amma ke kullum kanki a tukunya."
"Na gode Ni'imah in kin gama zagina sai ki faɗa min."
Kama kunnuwanta ta yi fuskarta ya canza ta ce."Am sorry big sis.!"
Sai da ta yi kamar ba za ta amsa mata ba tana komawa hanyar kitchen ta ce."Apology accepted ba don halinki ba."
Ihun murna ta yi haɗe da godiya. Bayan shiganta kitchen ɗinne ta manna 'yar karamar camerar da Ummata ta bata a daidai saman TV in da aka yi kwalliya da flower, babu mai gane da abu a gurin sai in kana gurin aka ajiye. Sannan ta yi saurin shiga ɗakin Abbas ma ta liƙa da ma ɗakin Bilkisu, tana fitowa ta ga Bilkisu rike da kunkumi ta ce."Binciken me ake min a ɗaki.?"
bA tunaninta ta ga sa'in da ta shiga ɗakunan biyu ne ta fara rawar baki. Bilkisu ta ɗaga mata hannu da cewa."Ya isa ki zo ki wuce ga mutumin naki can a dining na gama ki ci kuma wallahi ko kwara ɗaya ban son gani a plate."
Da murna ta rungumi Bilkisu ta ce.
"Aunty Allah ya ja tsawan rai na ga 'ya'yana."
Da gudu ta nufi gurin cin abincin ta yi saurin dakatar da ita."Babu ruwanki da Samba."
"Na ji kuma na yarda."
Ta karasa gurin ɗan waken. Maganar Ni'imah ne ya dawo kwakwalwarta ita da yara har abada domin Abbas da kanshi ya dinga mata pills masu ƙarfi, tausayin kanta da kanta take yi saboda Abbas ya gama da rayuwarta. Hawaye ne ya zurnano a kumcinta ta yi hanzarin sharcewa saboda ba ta bukatar Ni'imah ta gani.
Kamar yadda ya saba shigowa hakan ya faɗo cikin gidan babu ko sallama bai yi tsammanin Ni'imah tana gidan ba domin bai yi tunanin za ta zo a wannan lokacin, sannan ta saba zuwa sai bayan ya tafi aiki take zuwa domin jininsu bai gamu a guri ɗaya ba. Kamar kullum a tsawace da gadarance ya ce."Ke 'yar gidan tsinannu don wulakanci da iskanci kina jin zuwata amma kika yi banza da ni saboda kin ga uwarki ta na yi wa ubanki kuma yana shanyewa to ni ba sakaran ubanki ba n...."
Nuni da hannu Bilkisu take yi masa don ya ankara da Ni'imah amma idanunsa sun rufe."Ba dai ubanta ba sai dai sakaran ubanka da ya yar da kai tun yaranta har yanzu bai waiwayeka ba! Ai ubanta ya yi maka rana tunda har ya mai da sakaran ɗan sakarkarun iyaye kamarka. Hausawa ba su yi karya ba da suka ce gwano bai jin warin jikinsa, wawa mai manta halarc....."
Ni'imah ta cafke maganar saboda zuciyarta ya gaza ɗauka. Marin da ya kai mata ne ta yi saurin rike hannunsa tare da nuna shi da yatsa ta ce."Farka daga mummunar barcin da kake Malam Halima ce gabanka ba Bilkisun da kamayar ganga abar dukarka. Kuma wallahi inhar ka sake buɗe ɗan iskan bakinka mai warin zina ka zagi iyayena, to ni ma bakina ba kurji bane ciki kuma ashirye nake da na mayar maka da kwatankwacin zagin da ka yi."
Sai huci yake yi idanunsa sun yi ja. Ya nuna Bilkisu haɗe da cewa.
