95-100: Season Finale. (YA GUDU)

67 10 4
                                    

Ciki ta koma haɗe da cewa.

"Abba ku fito don Allah mu ga abin da Samba ke nuna mana tun shigowarmu yake kuka tare da nuna mana can gurin tarin ƙasan nan. Abba jikina na ba ni akwai hikima a tattare da Samba don Allah ku fito mu gani."

"Ni'imah rigimarki ta cika yawa. Jiya kin damemu da kuka yanzu kuma mun zo ki zauna 'yar'uwarki ta fito daga wanka mu gaisa kuma kin ce mu fito gurin ƙasa me za mu yi a gurin ƙasar Sadiya? Ni masallaci zan tafi kuma sanin kanki ne huɗuba ta wuce ni."
       Cewar Abba. Hawaye ne ya gangaro mata ta ce.

"Abba don Allah ku taso in ma ta fito ai za ta samemu wajen amma don Girman Zatin Allah Abba ku fito."
       Jan hannun Abba take yi haka dai ya ta so ba don ya so ba. Gurin kabarin suka nufa har yanzu kuma Samba na tsugune gurin yana ganinsu ya fara tona gurin, Abba mamakin lamarin ya fara saboda tun zuwansu yake tsugunne a gurin yana haushi, yanzu kuma da ganin su Abba ya hau tone gurin. Hassan da Hussain ne Abba ya sasu haka gurin, ledar da suka gani kusa da diggar gurin suka ɗauka har Hassan zai buɗe ledar sai ya sa tare da fara tone gurin kayan Bilkisu ne ya fara musu sallama da sauri Ni'imah ta karasa gurin tare da cewa.

"Abba kuna ganin abin da nake gani kuwa? Abba ku duba da kyau wannan atampar da ka yi mana ne da karamar sallah wallahi shi ne Abba.!"
      Kuka take yi Hajiya Rukayya ta yi saurin rikota tare da rungumarta.

"Hassan ku yi hankali gurin tonar nan ko kuma ku yi amfani da hannu kawai ku ajiye digar."
     Cewar Abba. Hannun suka sa suna tonewa sannu a hankali Hussain ne ya taɓo fuskarta da sauri ya janye hannunsa haɗe da cewa.

"Wallahi Abba mutum ne kwance a gurin nan."
      Hannunsa ya duba ya ga jini ya kuma cewa.

"Abba ka gani wallahi mutum ne kwance gurin nan ka ga jini ne a hannuna."
        Daɓas Hajiya Basira ta zauna a ƙasa ta kurawa ramin ido. Hassan ne ya cigaba da haƙon ramin har Bilkisu ta bayyana. Ihu Ni'imah ta yi haɗe da shiɗewa ta bankare a jikin Hajiya Rukayya ɓoyayyun aljanunta ne suka tashi, fisgewa ta yi ta nufi Abbas da gudu dake tsaye a kofar d'aki ta shaƙe wuyarsa iya ƙarfinta idanunta sun yi ja. Kakari yake yi kamar mai shirin barin duniya da kyar Abba da wasu makota da suka ji hayaniyar da ke faruwa suka kwace hannun Ni'imah a wuyar Abbas.

"Wallahi shi ya kasheta Abba."
          Juyawarta ya yi daidai da fito da Bilkisu daga ramin zubewa a ƙasa ta yi tare da makociyarsu da ita ma shigowarta kenan. Nan da nan aljanunta suka ta shi har Ni'imah ma da babu wanda yasan tana da su a ranar sun ta shi, Hajiya Basira zuba mata ido kawai ta yi amma babu hawaye sai ajiyar zuciya take yi. Hajiya Rukayya ya ce ta yi saurin cire mayafinta ta lulluɓeta da shi tana kuka mai ban tausayi, da kyar aka samu aka kwantar da aljanun Ni'imah domin har Hajara makociyarta wanda Samba ke zuwa gurin karyarta sun sauka ta dawo hayyacinta cikin kuka ta take cewa.

"Na ji ihunta ta windon ɗakina tana addu'ar neman taimako amma na gaza taimaka mata! Ku yafe min wallahi shi ya gargaɗe da karna kara shigar masa gida kuma ya yanke zumuncin dake tsakaninmu.!"
           Haka ta ci gaba da faɗar kyawawan halayyar Bilkisu haɗe da munanan halin Abbas. Duk wanda ke gurin tur yake da Abbas da tofa masa yawu mai wari aka, kuma duk abin da ake yi yana zaune a gurin babu ɗar ko tsoro a zuciyarsa sai da ya ji an kira police sa'annan ana kokari yi ma Bilkisu sallah ya lallaɓa ya gudu, babu wanda ya lura da rashin shi gurin sai bayan da police suka zo sannan aka farga da gudunsa. Hotonsa aka ba su sannan aka sallame su amma suka tafiya sai su ka ce za su rakata makwancinta.
      Har zuwa yanzu da aka ɗauki Bilkisu zuwa gidan Alhaji Shamsu don suturtata Ni'imah ba ta farfaɗo ta dawo hayyacinta. Hajiya Basira kuwa babu ɗigo ko surnanowar hawaye a idanunta sai ajiyar zuciya take yi, ita da Hajiya Rukayya su ka mata wanka anan ne suka kara firgita da irin kisan gillar da Abbas ya yi mata. Ba don babu kyau kuka lokacin wankan gawa da ko tabbas Hajiya Rukayya ta rushe da ihu, sakamakon caccakar wukar da Abbas ya yi mata kuma har zuwa yanzu da ake mata wanka jikinta na nan fresh furkarta ɗauke da murmushi, su ka ce ta yi kyau da haske kuma har yanzu ɗin kwayar idanunta a tsaye take baƙin ya shige sai hasken da ya kara haske.
           Sutura suka yi mata kamar yadda addini ya tanadar kuma ya koyar da mu. Iya fuskarta kawai aka bari buɗe 'yan'uwa na ta zuwa yi mata sallama da addu'ar dacewa da rahamar Allah, Ni'imah aka kawo a miƙe kamar matatta haka aka shimfiɗar da ita kusa da Bilkisu. Ganinta ita ma kwancen ne ya sa Hajiya Bilkisu fashewa da kuka amma har yanzu babu hawaye a fuskarta, babu wanda ya hanata saboda kukan ma rahama ce a gareta.
          Abba ne ya shigo yin sallama da ita tare da su Gambo duk suna tsugune gabanta suna addu'a. Abba ne ya kalli Hajiya Rukayya ya ce.

DAN'ADAM (BUTULU)Where stories live. Discover now