Kimanin wata ɗaya kenan suna gurza soyayyarsu sai dai har yanzu Abbas soyayyar fatar baki yake mata domin babu abin da ya sauya daga tsana da kyarar da yake mata. Kuma yau sati ɗaya kenan da fara shinshino kamshin rayuwarta ta baya saboda har yanzu Abba bai kirashi ya yi signing contract ɗin ba duk da yasan da tarin mutanen da suke neman wannan damar amma Abba ya ce shi zai bai ma wa, yanzu ma zaune suke cikin kasuwa tare da abokan kasuwancinsa. Ko wanne na tofa albakacin bakinsa kan in Abba ya ba su da irin arzikin da za su samu, hakan take ga Abbas don shi ma ba a barshi baya ba ya ce.
"In har Alhaji ya ba ni wannan conturagin nasa hannu ni fa shikenan domin babu wanda zai tuna da ya taimake ni a baya domin ni ma zan yi kokarin gina rayuwata ce da kuma iyali masu kyau."
Gaba ɗaya suka yi dariya sai ɗaya daga cikin yaran shagon Alhaji Shamsu ya ce."Baba yadda kake rayuwa na birgeni ko ni ne na samu dama damawa zan yi."
Abbas ya ce."Kai bana fatan Allah ya bawa wani nawa aboki ko ɗan'uwa irin damar da na samu mai cike da kuncin rayuwa, Malam ina faɗa maka da kasan waye Alhaji Shamsu a baɗilance da wallahi ko zaman shagonsa ba za ka yi domin mugun mutum ne kuma ai kowa yasan fulani da muganci."
Ɗaya dake gefe da tun da suka fara magana bai sa baki ba kuma yana daga cikin amintattun Alhaji, sa'annan babu rayuwar da bai sani ba game da Abbas sannan yana jin haushin Abbas tun lokacin da ya ce yana muzgunawa Bilkisu abokan suka mara masa baya. Ya kuma san irin muggan addu'oin da yake jefar Alhaji da ya yi saurin danna record a wayarsa sannan ya ce."Wallahi Abbas ka ji tsoron Allah ka sani wannan abin da kake faɗa tamkar butulcewa Alhaji ne. Saboda mutumin nan shi ya mai doka mutum mai daraja da kamala, bai kuma barka hakan nan ba ya ɗauki 'yarsa mafi soyuwa a gurinsa ya ba ka don dai kawai ya cire maka tunanin maraicin uwa da uba amma kuma yanzu kake faɗan irin wannan maganganun marasa daɗi akansa."
Abbas cikin fushi ya ce."Na daɗe ina jin haushin katsalandar ɗin da kake min arayuwa kuma wallahi tallahi Faisal in ba ka daina saka min baki a maganar da ban sakoka ciki ba to wallahi ina gab da rabaka da wannan aikin da kake tutiya da ita."
"Ratsuwa da barazanarka babu abin da za su min Abbas. Sannan ka sani in har kan Alhaji ne ba aiki kaɗai ko rayuwata za ka rabani da ita to fa ba zan daina faɗa maka gaskiya ba, wato har ka manta da irin halaccin Alhaji da iyalansa suka yi maka kenan? Har duniya ta ruɗeka ka manta da lokacin da kake tsangayar Malam Mamman? Ka manta ranar da ya janyoka jikinsa kenan? Shi ne har kiɗa da discon duniya ta sa za ka butulce musu? To in ko ka yi hakan wallahi rayuwa ba za ta yi maka kyau ba Abbas. Ka yi tunanin abin da kake shirin yi shawara ce."
A fusace ya taso abokansa masu zigi da ingiza shi suka yi saurin rikosa ɗaya cikin abokan ne ya ce masa."Gaskiya wannan yawa ne baba kuma abin da Faisal ya faɗa gaskiya ne fa ko ni shaida ne sannan ba fa zamu zuba ido ka butulcewa Ala'saini ba dole mu ma da ya mayar 'ya'ya masu ƙima a idanun duniya mu rama mai."
"Au haka kuka ce ko? To gaba ɗayanku nan ku jira na amsa contract ɗina za ku ga abin da zan yi da ku."
Ya yi maganar cikin fushi. Faisal ne ya kuma cewa."Ko ka amsa mai zai faru? Kodayake ai ɗan halas shi ne bai manta tuwon gobe."
Haka suka ci gaba da misayar yawu mara daɗin ji da saurare kuma duk abin nan da ake yi naɗar maganar da Faisal ke yi bai daina ba har sai da Abbas yabar gurin. Shi ma ya kashe wayar tare da mayar da ita aljihu kuma ya kudiri aniyar kunnawa Abba ya saurara ko da kuwa ba zai yarda da shi.
Abbas na komawa gida a fusace ya nufi Bilkisu da ke zaune a ɗosane a kujera domin kafin fitar Abbas ya ce ta jirayi dawowarsa, Samba ne kwance kusa da ita sai zubar da yawu yake yi a fusace don shi ma ya kudiri kwatarwa uwargijiyar shi 'yan cinta. Belt ɗin wandonsa ya zaro haɗe da zuba mata kan belt ɗin gurin karfe ya buga mata a kai, ihu ta yi tare da rike kanta ta faɗi sumanmiya a ƙasa duk da haka bai bar zuba mata mabugin ba har sai da ya gaji don kansa. Haushi Samba yake yi haɗe da zagaye Bilkisu dake kwance yana lashe mata ƙafa, ruwan sanyi ya ɗauka ya sheƙa mata amma ba ta farfaɗo ba domin ko motsi ɗan yatsarta bai yi, ruwan ya sake sheƙa mata har karo na uku sannan ta sauke ajiyar zuciya cikin kuka ta ce."Me na yi maka da kake dukana? Ni ce na ce Umma da Abba su haifoni ko kuma ni ce na ce su daina sonka? Duk abin da kake min ban taɓa kai kararka ba bare na haɗaka da Abbana! Kullum kyautatawa ce a tsakaninku, yana sonka kuma ya ɗauke ka ɗan cikinsa amma karasa wacce za ka tsana sai ni me na yi maka? Kuma wallahi sai mun tsaya gaban Allah ya yi mana hisabi don ban taɓa yafe maka ba.!"
Buɗe baki ya yi yana kallonta cikin tsana sannan ya ce."Kin san me yasa na tsanaki? Saboda soyayyar da tsinannun iyayenki ke nuna wa miki kuma a gaban idona. Ni kuma na tsani na ga hakan saboda ni ban da iyayen ko tausayin hakan ba sa yi don haka dole na yanke alakata da ku."
"Na yarda ka sake ni amma kar ka yi musu komai don Allah na rokeka Ya Abbas.!"
Kuka take yi sosai kamar ranta zai fita. Samba ya nufe shi a fusace ya kama kafarsa ya danna hakorarsa masu kaifi bai cire ba sai da ya cire naman gurin. Ihu yake yi na neman taimako amma babu mai kawo masa agaji domin ko tsawatar da shi Bilkisu ba ta yi ba wannan ne ya ƙara ɓata masa rai ya nufi kitchen da sauri yana jan kafarsa, ganin haka yasa Bilkisu saurin mikewa ta nufi ɗakinta tana kuka."Ya Allah kasan ban taɓa kuntatawa bawanka ba Allah karka ba shi ikon cin nasara a kaina. Allah karka ba shi nasara kan iyayena da 'yan'uwana! Rabbi ka kawo min hanyar da zan kwaci kaina a gurinsa! Allah ka kawo min mafita don tsarkin mulkinka.!"
Kuka har yanzu take yi Samba na tsaye kofar ɗakinta yana haushi da kururuwa. Dambe yake da Samba sosai har ya samu damar yin nasara kansa ya faɗi ƙasa sumamme, kofar ɗakin ya nufa yana jijjigawa da iya karfinsa amma kofar taki buɗuwa. Keyn kofarsa ya ɗauko tare da buɗe kofar tana ganin kofar ta buɗuwa ta yi wani ihu tare da zubewa a kasan gurin tana kiran Allah! Nufarta ya yi yana jan kafarsa ya damko gashin kanta zuwa falo, har yanzu bakinta bai daina furta sunan Allah ba."Allahna! Allahna! Wayyo Allah ka ɗauki rayuwata Allah! Karka ba shi ikon yin nasara a kaina Allah! Allahna ka ɗauki rayuwata Allah! Ummata ki yafe min don Allah. Abbana ku yafe min kasheni zai yi, Allah ka ɗauki rayuwata Allahna. Wayyo Allahna! La'ilaha Ilallahu Muhammadu Rasulillahi Sallallahu Alaihi Wasallam! Annabina. Annabin Allah ka cece ni kar ka bari ya kasheni!"
Haka ta ci gaba da kururuwar neman taimako amma idanun Abbas sun rufe a falo ya wurgar da ita haɗe da taka mata ciki iya karfinsa. Ihunta ne ya far kar da Samba daga sumar da ya yi, belt ɗin ya ɗauka ya cigaba da dukanta da shi aka da jiki ihun kanta take yi da tuni jini ya wanke mata fuska. Amma duk da hakan bai sa Abbas tausayin barinta ba, wukar da ya jefar tun lokacin da yake dambe da Samba ya ɗauko da sauri. Samba ma gurinta ya nufa da gudu yana lashe jinin fuskarta ita dai tana kwance kwakkwarar motsi ba ta iya yi har ya dawo da wukar a hannunsa, tsuguno ya yi daidai kanta tare da ɗago kanta da kyar ta buɗe idanuwanta dake mata nauyi ta kalle shi, wukar ya nuna mata sannan ya ce."Ai na faɗa miki na tsani ganin yadda suke sonki kuma na faɗawa Faisal ku jira za ku ga abin da zan yi muku. To ga shi yanzu zan fara ta kanki kashe ki zan yi kuma na kashe banza, sa'annan na kashe matsiyacin ubanki a tsaye bayan na gama kwashe dukiyar da ya yi shekara da shekaru yana tarawa."
Cikin dauriya da muryar da ta galabaita ta ce."Allah ba zai baka iko ba kuma Abbana ba matsiyaci ba ne iyayen da suka yi zinark....."
Wukar da ya daɓa mata ne yasa ta kasa karasa maganar ihu ta yi haɗe da salati hawayenta ya gwarwaye da jini tana kuka ta ce."Zinarka ku- m-a su-suka yi zin-narka sannan suka wurgar."
Ta tofa mishi yawu a fuska. Wukar ya sake daɓa mata a zuciya haka ya cigaba da caccaka mata wukar har ta cika da salatin Annabi a bakinta idanunta kan Abbas Allah ya zare rayuwarta.!Innalillahi Wa Inna Ilaihir Rajiun! Hasbinallahu Wa Ni'imar Wakil! Allahumma Ajirni fi musibati Ya Rabbi! Lallai Ɗan'Adam Butulu ne. Abbas ya kasheta 'yan'uwa! Abbas ya kashe Bilkisu akan abin da ba ta da iko akansa! Don Allah mu haɗu mu taya iyayen Bilkisu addu'a Allah ya yi mata rahama ya gafarta mata! Amin Ya Rabbi.
DAB...
BSN Ce.