💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧
(ya dace ya gyara kansa)Bilyn Abdull ce🤙🏻
[6......]
..............Da k'yar ya iya tashi da asubar farko, dan kansa ciwo yake masa, bayi yashiga ya d'aura alwala kafin ya fito ya canja kayan barcinsa zuwa jallabiya ruwan madara, yad'an fesa turare sannan ya fice.
Tunda ya dawo shike kiran sallar farko a masallacin, yauma kamar kullum zazzak'ar muryarsa mai cikeda sanyi ta karad'e anguwar. Koda ya kammala kiran salla ba zama yayiba, saida ya gabatar da nafila raka'a biyu kafin yay zaman karanta littafi mai tsarki. Ahankali mutane d'ai-d'ai suka fara fitowa, ciki harda malam.
Bayan an idar da sallar Asubahi Aliyu bai fitaba, zaman yin azkar na safe yay, saida ya kammala sannan yafito a massalacin. Shiga yay suka gaisa da Malam.
Kallo d'aya malam yayi masa ya karanci damuwa mai tsanani a fuskar d'an nasa, har zai mik'e ya tsaidashi ta hanyar kiran sunansa,
“Aliyu!”.
“Na'am baba” ya amsa yana waiwayowa ga malam.
“Dawo ka zauna”.
Bai musaba ya dawo ya sake zama kansa a k'asa.
“Mike faruwane? ko bakada lafiya?”. Malam ya tambayeshi cikeda kulawa.
Ajiyar zuciya M. Aliyu ya sauke, cikin sark'ewar murya yace, “Lafiyata k'yalau baba, kawai dai wani abune da ban ya girgiza dukkan kuzarina”. Shiru yad'anyi yana sauke numfashi da ajiyar zuciya, yayinda malam ya kafeshi da Ido amma baice komaiba. M. Aliyu yaci gaba da fad'in “Wani sak'one ya birkita dukkan hankalina wlhy baba...............” tiryan-tiryan ya shiga karantoma baba sak'on yarinyar jiya. Shi kansa baba maganar ta girgizashi, har gumi yad'an tsatstsafo masa a goshi, yanayinsa dukya sauya. Wata ajiyar zuciya ya sauke k'arfi yafara fad'in “Dolene ka girgiza Aliyu, duniyarnan cike take da curkud'ad'd'un abubuwa masu hargitsa tunani, babu abinda ke kusanto duniya sai alamomin tashinta, inaga kamata yay kanemi gidansu ita yarinyar, dan mahaifinta yakamata mu fara gani”.
“To shikenan baba insha ALLAHU zanyi k'ok'arin hakan”.
“ALLAH ya bada nasara, ya maganarmu ka yanke shawaran”.
“Baba kawai nabar maka za6i”.
“To Alhmdllh ALLAH yasa mu dace”.
“Amin” m. Aliyu ya fad'a hannunsa dafe da kansa.A k'ofar fita daga Falon malam yaci Karo da yayansa Abubakar, hannu ya bashi sukai musabaha cikin girmama juna, Aliyu ya tambayi iyalansa da aiki kafin suyi sallama, Abubakar ya shige shikuma Aliyu ya fice.
Cikin gida ya koma ya sake kwanciya, dan kansa ya matsa masa da ciwo ainun.✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Umma ta dad'e zaune zuciyarta Na suya, ta tsurama tea d'in data had'ama Abba ido, wai ko kunya baijiba a gabanta yake fad'in zaije yakai yaransa makaranta saboda motar da ake kaisu babu mai, bayan a gaban idonsa su Walida suka fita amma ko ALLAH ya kiyaye baice musuba? Sai yaushene Alhaji zai fahimci kuskuren da yake tafkawa a rayuwarsa? Kosai guri ya k'ure masane?. Wani lokaci takanji kamar bazata iya jure wannan zamanba, musamman idan ta kalli halin k'unci da yaranta suke a ciki. Sai dai kuma wani 6angaren tana duba wani Abu, yaranta sunkai girman da gidan mahaifinsu shine adonsu, dan burin kowacce y'a a nema aurenta tana gidan mahaifinta gaban iyayenta biyu. Wasu hawayen takaicine suka ziraro mata, tayi murmushin da iyakarsa hak'oranta tareda mik'ewa tahau tattare kayan shayin da Wanda ta had'ama Abban.
Sallamar Dauda ta jiyo a tsakar gida, ta amsa masa tana fad'in, “Ina zuwa Dauda”.
Daga tsakar gida ya amsa da “to”.
Tea d'in data had'ama Abba ta d'auka ta fito, Dauda ya rissina yana gaisheta, cikin sakin fuska ta amsa masa kamar yanda ta Saba. “Yau naga ka makara, ko Baku tashi a makaranta da wuri bane?”.
Dauda yace, “A'a muntashi, Na tsaya yin rubutune a allona”.
“To ALLAH ya taimaka, bara Na kawo maka abincinka ka karya saikai maza ka kaimin 6arzan masarannan dan ALLAH, yau sonake nayi dambu, kowa yagaji da shinkafarnan”.
“To hajia” dauda ya fad'a cikin girmamawa.
Kunu da fanke Umma ta kawo masa, ta had'o da shayin data had'ama Abba duk tabama Dauda.
Wasu y'an aikace-aikacen tafara ragewa kafin Dauda daya fita soro cin abinci yagama yakai mata 6arjin masaran.
Babu dad'ewa ko saigashi, dama ta had'a masa a wani k'aramin boket, dan haka kud'in 6arjin ta bashi dana abinda zai sayo Mata Na cefane. Sannan ta nuna masa masaran.
Bayan tafiyarsa bata zauna ba, ta kunna redio tana saurare da rage wasu ayyukan gudun zama tunani ya addabeta.
YOU ARE READING
MUTUM DA DUNIYARSA......
AdventureWannan labari labarine da ya taɓo rayuwar da mafi yawan mata ke fuskanta a wannan rayuwar, tare da rayuwar kishi na gidajen aurenmu, da nuna jarumtar mazan ƙwarai da ke aiki da hankali da ilimi wajen tafiyar da ragamar rayuwar aurensu. Magida...