💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧
(ya dace ya gyara kansa)Bilyn Abdull ce🤙🏻
[35➖36]
..............Kallo d'aya taimasa ta d'auke kanta tana murmushin k'arfin hali, jikinta duk sai ya kuma sanyi, itadai tasan Aliyu ba mutum bane mai yawan fitina, hasalima sunkan jera kwana hud'u batareda ya nemeta ba, sannan baya d'aukar dogon lokaci tare da ita, wannan dalilin yasakashi dagewa wajen gyara kansa, dan a ganinsa ba mace kawai yakamata taima miji gyaraba, suma mazan yadace suna gyarawa........
“Ko ba'ayi murna da dawowataba Na koma Gimbiya”. Maganarsa ta katsema Maimunatu tunaninta, mik'ewa tayi ta nufosa, sai da ta rungumesa da sumbatar kumatunsa kafin ta sakesa ta amshi kayan hannunsa tana danne kwallar data cika idonta, dan sosai taji k'amshin turaren daba nashiba a jikinsa, tasan kuma bai wuce Na amarya ba, a yandama yadawo mata kad'ai ya isheta amsa.
Bin bayanta yay ya zauna yana sauke numfashi, kallonsa tad'anyi batareda tace komaiba tawuce kicin, babu dad'ewa tadawo d'auke da tire.
Gabansa ta dire, ya d'ago kansa daya jingina a kujera yana kallonta, itama shi take kallo, cikin danne zuciyarta tasaki murmushi tana fad'in “Wai miya sakaka laushi haka Annur?”.
Zamansa ya gyara sosai tareda kamo hannunta ta zauna a gefensa. Muryarsa a matuk'ar sanyaye yace, “Babu komaifa madam, naga kin damu”.
“To ba doleba Yaya, kafita muna farin ciki kadawomin a sanyaye, kaga sainaga ko wani abune yafaru da jiddan ko wani a gidansu ai?”.
“To kwantar da hankalinki, babu abinda yafaru tanama gaisheki. Bani ruwa nasha kedai”.
“ALLAH Sarki, ina amsawa nima, kuma Alhmdllh tunda babu wata damuwa”. Jug dake kan tire ta d'auka tafara tsiyaya abin ciki a k'aramin kofi.
“Minene wannan zaki bani?”.
Da mamaki ta kallesa sannan ta kalli jug d'in, “Yaya had'in kwakwar dakace namakane d'azun ai, to wlhy nama manta, sai bayan fitarnan taka dasuka kawo wuta Na tuna shiyyasa nayi, kajiko harma yayi sanyi”.
Amsar jug d'in da kofin yayi ya ajiye k'asa, “Barshi dan ALLAH Maimoon inba kasheni zakuyiba”.
Cikin waro ido Maimuna tace, “Yaya kashewa kuma?”.
“Eh mana, ba dole nace kashewa ba, ita tabani kunun aya, kekuma zaki bani had'in kwakwa?”.
Babu shiri Maimuna ta kwashe da dariya, haba no wonder tagansa a sanyaye.
Harara ya zuba Mata yana wani shagwa6e fuska da fad'in “Abindama zakimin kenan ko? Maimakon kiji tausayina”.
Baki Maimuna ta toshe da hannu tana had'iye dariyarta da k'yar, “ALLAH Yaya kaid'inne kaban dariya, ni duk kasakani a tsorone da farko”.
“Humm bazaki ganeba wlhy, tsautsayi kawai ya sakani shan kunun ayarnan da yawafa, gashi kuma yasha had'i kamar yanda kikemin, Nidai Ahmad ai yagama dani daya bani wannan sirrin”.
“Haba dai Yaya godiya yakamata Kai masa ai”.
Hannu yasa ya jawota jikinsa, murya k'asa-k'asa yace, “Wayace ban gode masaba, badan iyakancewar Mahaliccina da taimakon Ahmad ba da yanzu ban mallaki koda mace d'aya ba balle Mata biyu ma ai Sarauniyata, amma wad'annan had'in ba k'aramar harmutsani sukeba”.
Hanu Maimuna tasaka ta rufe fuskarta tana Y'ar dariya. Shima saiyay murmushi yana kuma sakata a jikinsa.
Tarigada tasan muhimmmanci duk irin wad'annan abubuwan ga mijinta, hakanne yasakata kar6arsa d'ari bisa d'ari tun a falo aka fara canja hanya.🙆🏻⛹♀.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Jiddah dai gaba d'aya tama rasa yanda zata fassara abinda sheikh Aliy yay Mata, wani iri duk takeji a jikinta, duk hirar dasu Zarah keyi hankalinta baya tare dasu, har aka maido wuta suka saka cajin wayar.
“Wai Yaya Jiddah mike matsalarkine? Tunda muka dawo kinyi sukuku”.
Kallon Zarah tayi mai maganar, kamar bazata tankaba saikuma ta sauke numfashi tana cewa, “Babu komai, kaina ked'anmin ciwo kawai”.
Sannu suka shiga jero Mata cikin tausayawa, Walida harda zuwa ta samo Mata magani. Bata musaba ta kar6a tasha sannan tayi shirin barci suka kwanta.
Barcinma k'in d'aukarta yayi, sai tunane-tunane takeyi, tunda take bata ta6a soyayyaba, hasalima baifi sau uku zuwa hud'uba ta ta6a tsayawa da saurayi, dan dawahala tana tafiya samari su tareta a hanya ko yimata magana (Muhimmancin nagartacciyar sutura ga d'iya mace, yakan saka mutanen banza shakkar zuwa gareka, abinda y'anmatan yanzu dama matan auren muka gaza fahimta kenan), wannan yasaka komai Na Aliyu take masa kallon *Sabon al'amari* a gareta, ganin barcin yama gagareta saita mik'e tafito domin d'aura alwala.
Nafilfili taita gabatarwa, kafin tayi zaman karatun littafi mai tsarki, a wannan time d'inne suma su Zarah suka farka, sai suma sukayo alwala.
YOU ARE READING
MUTUM DA DUNIYARSA......
AdventureWannan labari labarine da ya taɓo rayuwar da mafi yawan mata ke fuskanta a wannan rayuwar, tare da rayuwar kishi na gidajen aurenmu, da nuna jarumtar mazan ƙwarai da ke aiki da hankali da ilimi wajen tafiyar da ragamar rayuwar aurensu. Magida...