31

2.7K 234 3
                                    

    💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧
             (ya dace ya gyara kansa)

               Bilyn Abdull

                   [47➖48]

   
..............Muryarta na rawa kanta a k'asa tashiga amsa masa,
        “Sharuddan alwala guda goma ne 1.Musulunci, 2. Hankali, 3.Wayo, 4.Niyya, tare da kyautata hukuncinta tare da niyyar ba zai yanke ta ba har sai ya kammala alwalar, 5.Daukewar abunda ke hana alwala (Jinin al’ada da jinin biki), 6. Istinja’u ko istijmaru, 7.Ruwan ya kasance mai tsarki, Ruwan ya kasance na halasta, 9.Gusar da abunda zai hana shigar ruwan fata, 10.Shigar lokaci ga wanda ke da hadasi a kowani lokaci.   
         Abubuwanda ke wajabta alwala. Abunda ke wajabta shi ne samuwar hadasi.
          Farillan arwala, Farillan alwala shida ne.1. Wanke fuska da baki da hanci wad'anda ke furkar. 2. Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu. 3. Shafar kai tare da kunne 4. Wanke kafafuwa. ALLAH madaukaki yace:
     “Ya ku wad'anda sukayi Imani! Idan kun tashi za ku yi sallah, to sai ku wanke fuskokinku da hannaye zuwa gwiwar hannu, kuma ku shafi kawunanku da kafafuwa zuwa idon sawu” (Ma’idah: aya ta 5).

         5. Jerantawa, domin ALLAH maigirma da d'aukaka ya sanya jerantawar hakan sai ya sanya shafa tsakanin wankewa. 6. Jerantawa kamar yadda ANNABI (S.A.W) ya aikata.

         SUNNONIN ALWALA. Daga cikin sunnonin alwala akwai; 1. Asuwaki
2. Wanke tafin hannu sau uku. 3. Kurkurar baki da shaka ruwa.
4. Tsefe gemu mai yawa da yatsun hannu da kafafuwa. 5. Damantarwa. (fara gabatar da dama). Wanki na biyu da na uku. (idan na farko ya game).
7. Debo ruwa domin wanke kunne. 8. Addu’ah bayan alwala. 9. Sallar nafila raka’a biyu bayan ta.

       Daga cikin makaruhan alwala. 1. Yin alwala a wurin da ba shi da tsarki, domin tsoron abinda ke iya taba jikinsa na najasa. 2. Kari akan wanki uku, domin abinda aka ruwaito lalle ANNABI ya yi alwala sau uku-uku ne, sai ya ce duk wanda ya yi kari hakika ya munana, kuma ya yi zalunci. (Nasa’i ne ya ruwaito).
3. Barna da ruwa wajan alwala, ka tuna lokacin da ANNABI (S.A.W) ya yi alwala da mudin Nabiyy, shi ne kuma kanfatar hannu. Barna abace da aka hana a komai. Barin sunnah daya ko fiye da haka, daga cikin sunnonin alwala, lalle kuma barinta rashin lada ne, kuma bai kamata baya bari lada ya wuce shi.

      Abubuwanda ke warware alwala. Abubuwa masu warware alwala bakwai ne;
1. Abubuwan dake fitowa daga mafita biyu (ta gaba ko ta dubura).
2. Abinda ke fitowa daga sauran jiki.
3. Gushewar hankali ta hauka ko farfadiya ko maye. 4. Shafar azzakarin mutum ko shafar gaban mace ba tare da shamaki ba. 5.Namiji ya shafi mace domin jin sha’awah ko mace ta yi hakan. 6. Cin naman rakumi.
7. Duk abunda ke wajabta wanka yana wajabta alwala, kamar shiga musulunci da
fitowar maniyyi da makamancin haka, saidai mutuwa lalle shi yana wajabta wanka ne banda alwala.

       WANKA: Ma’anar wanka; A yare da kuma wurin mallaman fikhu, Alghuslu ) ( da wasalin dumma ruwan da ake wanka da shi ne, amma da wasalin fataha ) ( aiki ne (wato yin wankan) da wasalin kasra ) ( kuma shi ne darasin mu, watau tsarkakewa. Ma’anar shi a shari’ah: shi ne zuba ruwa a dukkan jiki, daga tsakiyar kai har zuwa kasan diddige da ruwa mai tsarki akan sifa kebantacciya. Mace da namiji wajan siffar wankan su dayane, saidai ga mace a lokacin da take wankan daukewar jinin al’ada ko na biki, to yana kamata a gare ta da ta wanke alamar jinin domin tsarkaketa da kuma kauda warin jinin.
       Abubuwan dake wajabta wanka. Abubuwan dake wajabta wanka guda shida ne:-
1. Fitar maniyyi kai tsaye, ta hanyar jin dadi daga mace ko namiji.
2. 6oyewar kan azzkari a cikin farji. 3. Idan mutum ya mutu ya wajaba ayi masa wanka, sai dai in shahidi ne. 4. Musuluntar kafiri ko wanda ya yi ridda.
5. Jinin al’ada.
6. Jinin biki (wato jinin haihuwa).

       Daga cikin wankan da suke anso ayisu a musulunci.
1. Wankan jumu’ah.
2. Wankan shiga harami (da hajji ko da umarah). 3. Wanka ga wanda ya yi wa mamaci wanka.
4. Wankan idi biyu (na zuwa karamar sallah da babbar sallah) 5. Idan mutum ya farfad'o daga hauka ko farfad'iya 6. Wankan shiga Makkah.7. Wanka domin sallar kisfewar wata ko kuma rok'on ruwa. 8. Wanka na mai istiha a kowacce sallah.9. Ga kowanne jima’i an so a yi wanka.

MUTUM DA DUNIYARSA......Where stories live. Discover now