20

2.6K 221 2
                                    

    💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧
             (ya dace ya gyara kansa)

                 Bilyn Abdull ce🤙🏻

                      [25➖26]

   
............Saukar dare su Jiddah sukayi, hakanne yasaka masu tarbarsu suka kasance k'alilan, tana farin cikin dawowa ga ahalinta gefe kuma na  zuciyarta na kewar k'asa mai tsarki, jin hawaye kawai tai suna gangarowa a kumatunta, wanda harga ALLAH batasan yaushene suka fara saukaba. Muryarsa Mai sanyin nan ta daki kunnenta.
         “Yakamata a nad'aki sarauniyar kuka ta k'asarnan”.
     Gabantane ya fad'i, har abadan bazata mance wannan sassanyar muryarba, da sauri ta d'ago idanunta ta saukesu a kansa.
         Janye idonsa yayi daga gareta tareda d'ora Mata handky d'in hannunsa saman trolley d'in gabanta ya wuce.
       Da kallo kawai ta bisa tana sauke wani kasalallen numfashi a hankali, sanye yake cikin shadda ruwan gwaiduwar kwai, yazuba dukkan hanayensa a aljihu, dukda darene hakan bai hanata shaida k'yawun haibarsa ba, mamaki take dama ashe ya dawo Najeriya shiyyasa bata sake ganinsaba a can.........
        “ALLAH ya tabbatar”. ‘Muryar aunty Siyama ta katsema Jiddah tunaninta’.
     Janye idanunta tayi daga kan Sheikh Aliyu daya k'arasa suna gaisawa da Uncle yahya.
       Jiddah ta share hawayenta tana murmushin yak'e, “Aunty addu'ar mi kikeyi?”.
       “Ta abin alkairin danaga yana Neman k'ulluwa mana Jiddah”.
     Jiddah bata fahimci inda Aunty Siyama ta dosaba, dan haka sai tai shiru. Itama Aunty Siyamar bata ja zancenba daga nan, saima haramar tafiya da sukeyi, dan dama sun tsaya jiran Malam ne dake gaisawa da mutane.
         Har gida sukaima su Jiddah rakiya.

         Su Umma suna zaune jiran isowar su Jiddah, dan Uncle yahya ya sanar musu ta waya, dan haka sunajin tsayuwar motoci suka fito cikeda d'oki.
        Tuni farincikin ganin juna yasa sun manta da kowa, murmushi Aliyu yayi yana lumshe idonsa, ba k'aramin birgeshi wannan family sukaiba, hakama Malam sun matuk'ar birgeshi, Aunty Siyama kam tuni taji kewar mahaifiyarsu ta mamayeta.
       Sai Uncle yahaya ne ya tsaya sukayi sallama da mutane, amma su Jiddah tuni sunyi ciki.

★★★★

      Barci dai yau sai 6arawone ya d'auki wannan ahali, washe garima da wannan farin ciki suka tashi, kafin kace mi gida ya d'inke da y'an taya murna, aunty Nafisa kam ai tunda farar safiya ta iso.
         Haka wannan yini Yakuma kasance musu cikin kar6ar bak'i, ita Jiddah ma sai kunya takeji.
      Dangin Umma ma sunata kiran waya, kawu Bunami (yayan Umma) yace Jiddah tafad'i komi take so indai baifi k'arfintaba zai Mata, dan d'ansa Banu da autar su Umman Balu suna nan zuwa Kano.
    Rasama abinda Jiddah zata za6a tayi, dan haka tabashi za6in ya saya Mata komi yaga yamasa. Albarka dai tashata wajen wajen kakarsu.
      Rana ta uku da dawowar su Jiddah saiga Abbah suna tsakar gida suna hira da innarsu Balu ya shigo, duk shiru sukai sai Balu d'ince dake murmushi. Shima saiya Saki fuskarsa yana fad'in “Ah ah yau Balu ce a kanonmu haka?”.
       “Aiko nice yayanmu, ai tunda nazo nake cigiyarka akace kayi tafiyane”.
       Cikin in ina yake  fad'in “E...eh...eh ta..fiya nayi wlhy, jiya na dawo da daddare shiyyasa”.
      Su Zarah dake zaune kawunansu a k'asa duk saida suka d'ago suka d'an kallesa saboda jin k'aryar da ya sharo babba dashi.
      Yayinda shikuma yad'an hararesu yacigaba da gaisawa da Balu.
     Duk abinnan dake faruwa Umma na cikin kicin tana jinsu, amma ko tarima batayiba, saida taji shigarsa d'aki sannan ta fito tabi bayansa da ruwa d'auke a hannunta.
       Kallo d'aya taimasa ta d'auke kanta gefe tana gaisheshi, jin a yanda ya amsa saita kuma kallonsa, harma ta kasa hak'uri saida tace, “Lafiya kuwa?”.
        “Lafiya lau, mi kika gani ne?”.
      “Babu komai”. ‘Umma ta fad'a tana mik'a masa ruwan’.
          Soyake yay Mata murnar nasarar da Jiddah ta samu amma ya kasa, sai mulmula maganar yake a zuciyarsa. Tsaf Umma na lura dashi, amma sai tayi tamkar bata ganshiba. Daga k'arshe daya rasa ta inda zai kamo zance saiya maida akalar maganar kan zuwan Balu. Itadai Umma eh a'a shine amsarta dashi, harya k'araci zamansa yay mata sallama ya tafi.
        Sosai hakan yayma Umma da Jiddah ciwo a zuciya, koba komai yakamata ya nuna murnarsa ga nasarar data samo, kodan ma darajar Addininta data samo nasarar a dalilinsa, amma saiyay k'ememe.

MUTUM DA DUNIYARSA......Where stories live. Discover now