8

2.4K 202 2
                                    

   💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧
             (ya dace ya gyara kansa)

                 Bilyn Abdull ce🤙🏻


                 [8......]

   
..............Zancen yarinyarnan data turoma malam Aliyu sak'o yata damunsa a rai da zuciya, dan haka ya buk'aci tabashi address Na inda suke.
     Batayi musuba ta turo masa suna cikin Kaduna ne.
    Washe Gari ya sanarma malam yanda sukayi. Kai tsaye malam yabashi Umarnin shiryawa suje shida Mahmud (kaninsa) da mustafa.
           A washe garin wannan ranar suka shirya domin cika umarnin malam.
      Bayan sun Isa kaduna masauki suka fara samu gidan babban malaminnan Sheirk Haruna bala, sanin zuwansu da yayi yaymusu tarba mai k'yau da mutuntawa, dan malam Abdul-ra'uff amininsane sosai. A ranar kam basu bar malam Aliyu ba, dukda gajiyar daya kwaso da daddare bayan isha'i saida ya gudanar musu da lecture Mai taken *_ILIMI DA RAYUWA ABOKAN TAFIYA_*.
     Washe Gari kusan misalin goma na safe ya nema yarinyar da sukazo dominta, dan yanaso a gobe su juyo Gidane.
         Da taimakonta suka iso gidan nasu, gidane babba badai can sosaiba, amma komai a tsare.
          Afrah yarinyar data turama malam sak'oce ta fito tarbarsu, k'yak'yk'yawace a fuska kam sosai, sannan akwai Fari amma irin na kanti, sanye take da hijjab iya gwiwa dan haka su malam basuda damar tantance shigarta, dukdama kallo d'aya sukai Mata kowa ya d'auke kansa, ita kanta cike take da kunyar ganinsu, dan haka kanta a k'asa tabasu umarnin shiga falon Abbansu da k'ofar take a harabar gidan.
     Bayan duk sun zauna ta fita, shidai malam Aliyu yana mamakin da tsarkake sunan ALLAH akan wannan hargitsatstsen al'amari.
           Kusan mintunanta goma da fita saigata tadawo itada wata dattijuwa d'auke da tirirrika, sudai su malam basuce komaiba, fita ta kumayi kafin mintuna kad'an ta sake dawowa ita kad'ai d'auke da wani tiren, bayan ta ajiye ta gaidasu.
      Duk amsawa sukayi.
Kanta a k'asa tace, “Malam kuyi hak'uri Dady bai dawo aiki baneba, amma yana hanya, dan yasan da zuwanku, dukda dai ban sanar masa ainahin abinda ya kawokuba”.
      “Masha ALLAH”. malam Mustafa ya fad'a.
    Malam Muhmud shima yace, “babu damuwa, ALLAH ya maidoshi lafiya”.
    Malam Aliyu dai baiyi maganaba, dan k'ok'arin amsa kiran da akai masa a waya yakeyi.
      Mik'ewa tayi tana rok'onsu dan ALLAH suci abincin.

     Zaman kusan mintuna talatin saiga Dadynsu Afrah ya shigo falon da sallama, da alama ma yadawo tuni, saida ya kimtsa ma sannan ya fito.
      Daka gansa kaga cikakken d'an boko kam, dan sanye yakema da wando tree quarter da T-shirt Mara nauyi, hannunsa rik'e da wayoyinsa, a hasashe zai iya kaiwa shekaru 60, Afrah Na matuk'ar Kama dashi, kawai dai shi bak'ine, itako tayi fari (amma na kanti😝 ). Tarba ta mutunci yayma su malam Aliyu tankar ya sansu, dan sunkula mutumne Mai yawan fara'a.
      Fuskarsa d'auke da murmushi yake fad'in “Lallai nazama Mai sa'a da farin ciki, yau sheirk Aliyu bin Andul-ra'uff maina ne da kansa a gidan, dukda bansan mike tafe dakuba ina muku lale marhabun, amma tabbas nayi mamaki sosai da wannan zunwan, tun jiya da Afrah ta sanarmin abin yak'i barin raina, harma Na tsareta da tambayar ina ta San babban mutum irinka? Dahar zaizo gidannan?”.
       Murmushi su Aliyu duk sukayi, kafin Aliyu yad'anyi gyaran murya, cikin sanyinsa da nutsuwa irinta masu ilimi yace, “Alhaji inafa manya, har gobe mu d'aliban ilimine, abinda ya kawomu kuwa gaskiya babban al'amarine Dani kaina yahana zuciyata da ayyukana sukuni, ina ganin har saina sauke kayan dake kainane Zan sami nutsuwa. Da farko dai tabbas nayi mamaki da kokwanto akan abindama ya kawonin, saboda ganin karanci da mutuncinka, saidai banida wani hurumi na k'in gaskatawar tunda nasamu zancen ne daga amintacciyarku”.
       Kai Dady ya jinjina, sannan ya gyara zama yana kuma damk'e kofin lemon hannunsa, “malam maganganunka sun sakani a duhu matuk'a, amma Zan kwantar da hankalina domin k'ara fahimtarsu daga gareka”.
         “Masha ALLAH, Alhamdllh Alhaji, mun gode da wannan karamci, da farkodai in babu damuwa ina son ganin dukkan iyalanka anan tare damu, wannan ne zai bamu damar fahimtar abinda ya taramun”.
           “To shikenan babu damuwa, Nawwas ne dama kawai baya gida, amma nasan ya dawo insha ALLAH” duk kiran wayoyinsu yayi d'aya bayan d'aya, acikinsu Afrah ce kawai a tsorace, amma Nawwas da  Namrah duk basusan ma'anar kiranba.
        A yanda Nawwas da Namrah da mahaifiyarsu kawai suka shigo ya isa Fara gaskata zancen Afrah. Gaisuwa ma ta sifirin a kaima su malam🤣.
           Dan Hajia Mansura ma tana taunar cigam ta shigo, dukda dai cin masu aji ake masa bana karuwaiba, Afrah ce kawai a k'asa zaune, amma Nawwas da Namrah duk a kujera suka zauna kusama da juna, hannun Nawwas akan Na Namrah wadda ke sanye da wando da Riga masu bin jiki, sai siririn mayafi data yano, shima saida mamansu Tamata magana, kanta yaci uban kitson gashin doki, daka gantadai kaga wayayyun wannan zamanin. Shiko Nawwas wandone irin Na babansa iya gwiwa, sai singlet ruwan d'orawa, askin kansa abun takaici da kuka ga al'ummar musulmai, dan an saisaye gefe da gefe da k'eya,  anbar gashin iya tsakkiyar kai sannan akai masa k'itso kalba (Dada) daga kasan gashin bak'i, sama kuma k'arshen kitson Brown.
       Duk a cikin mintuna kad'am su Malam Aliyu suka nazarcesu.
      Dady yace, “Malam ga iyalin mawa, d'ayane babu a ciki autansu, yana jami'ar legas yana karatu, kwannan ma yatafi, wannan itace matata mahaifiyar yarana, sai babban Nawwas mai shekaru 27 a duniya, yagama p.h.d d'insa, watansa shidda kenan, yanzu haka yana aikinsa. Sai Afrah, tagama degree d'inta itama kwannan, muna mata shirin zuwa masters, sai Namrah tana jami'a tanan jos L200 yanzu”.
         Masha ALLAH su malam Aliyu suka fad'a a tare, da d'orawa da addu'ar fatan alkairi.
             Daga Nana malam Aliyu ya d'ora da fad'in “Dalilin zuwanmu nan gidan shine yarinyarka Afrah”. Atare suka kalli Afrah da kanta ke a k'asa. Malam Aliyu yacigaba da fad'in “Wani sak'o daya kasa barin zuciyata ta turamin, harma naji nakasa hak'uri saina dangane da wannan family, Afrah indai ban shiga huruminki ba inason ki kuma maimaita abinda kika turamin domin Na tabbatar”.
     Hawayen dake d'iga a kumatunta ta share, kafin tace, “Dady da mah-mah Ku gafarceni, yau Zan bud'e sirrin daku baku saniba, saidai har a yanzu ina tambayar kaina Sakacinku ne kokuwa ak'idar boko ce? Da wautar barin tarbiyyar addinin islama?. Har yanzu zuciyata ta Gaza amsamin tambayar, amma ban saniba ko idan Na fad'a yanzu amsar zata fito”.
     Ba k'aramin fad'uwa gaban Nawwas yayiba, dukda baisan mi Afrah zata fad'aba yaji ya tsargu. Mik'ewa yay niyyar yi amma dad ya tsaidashi da Ido, dole ya koma ya zauna yana wani kumbura baki.
      Afrah takuma fashewa da kuka sannan tafara jawabi dalla-dalla kamar yanda taima malam Aliyu a sak'o, harma ta k'ara da abinda bata sanar masaba.
      Gaba d'aya falon jikin kowa ya mutu murus, Dady da mah-mah ma jikinsu rawa yakeyi, hakama Namrah datayi wani tsalle zuwa k'asa saboda tsorata, bata ta6a zaton wani mahaluki yasan suna tarayya da Nawwas ba, sannan bata ta6a zargin yanayin abinda yakeyi da ita da Afrah ba.
      Gani kawai sukayi Dady ya kifo k'asa, Mah-mah ma data mik'e domin zuwa garesa saita yanke jiki ta fad'i. Nawwas kam dukya rikice, yarasa ina zashi ya 6uya saboda kunya da tsantsar tashin hankali.
        A tsorace su malam Aliyu duk sukayo kan Dady, yayinda Afrah tayi kan mah-mah d'insu.

MUTUM DA DUNIYARSA......Where stories live. Discover now