💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧
(ya dace ya gyara kansa)Bilyn Abdull ce🤙🏻
[65➖66]
............Hajia hindu dai shirinta tai tsaf domin tafiya, Sai dai kuma ita kaɗai zata tafi bada yaraba, ƴan kuɗin da ake tarama Abba na dubiya tasaka Kalifa yabi duhun dare ya lalubesu tas, shima saida ya ɗiba rabonsa sanan ya kawo mata sauran.
Kafin ta kwanta kamar wasa ta gwada Number ƙaninta harisu kamar yanda ta saba, yaukam saiga waya ta shiga kamar almara, jikinta har rawa yake ta fara faɗin hello-hello tunkan a ɗaga.
Sai da takusa tsinkewa ne aka ɗaga wayar.
Cikin mamaki tace, ”Wanene? Ina kuma mai wayar?”.
Dariya yaron harisu yayi irinta basawa wadda harta tsorata Hindu, saida yayi mai isarsa sanan yace, “Wanan yakwana biyu a barzahu. Halan kece yayarsa da tai mana hanyar samun ƴan canji”.
Zumbur hindu ta miƙe dan bata fahimci maganar tasa ta farkoba, tace, “Eh wlhy nice, tun washe gari nake nemanku a raba kuɗin amma wayar taƙi shiga, dan ALLAH ina harisun yake?”.
Wani wawan tsaki yayi yace, “ke wai halan kanki baya kawo wuta ne, kajimin mumun mata, nace miki yana barzahu, bara na miki gwari-gwari danna kula ƙwaƙwalwar kifi gareki, dama Oga haris baizo amsar kuɗi danya raba dakeba, yazo amsane ya ware abinsa, shiyyasa ya saka miki Number busy yanda kokin kirashi bazaki samuba. Duk wahalar da mukasha wajen amso kuɗin nan muka wanke ƙafafunmu tundaga legas mukai masa rakkiya amma yay nufin cin amarmu, muko bazamu iya ɗaukaba, sati huɗu kenan muka caccake cikinsa da wuƙa muka aikashi gidan kowane shege da shegiya (lahira kenan), yanzu kema na ɗauki wayarkine danki daina wahalar nemansa ma, kisamu gobe kisa ai masa addu'ar uku data bakwai data arba'in, wainar da za'a bamu kirabama almajirai, muna miki gaisuwar ta'aziyyarsa fa, kuma karki damu sai da mukai masa salla kafin mu jefashi ruwa......”
Ƙitt ya yanke wayar.
Ihu kawai hajia hindu ta dage ta fasa, ta kware baki tana rusar kuka da kiran “Wayyo kuɗina, shikenan na mutu, Harisu ka talautani...”
Wanan ihune yay sanadin tashin su Umma a barci, sukazo suka rufu akan hajia hindu ana tambayar miya faru?.
Batareda tasan mi takeba tashiga sakin surutai akan yanda ta ƙulla makirci da haris aka amshe kuɗin Jiddah, harma da dukan da Abba yaci wanda gashinan ya zame masa sanadin doguwar jiyya.
Wannan lamari yayi masifar girgiza su Umma da Abba dake cikin ɗaki kwance yana saurarensu, jiyay hawaye kawai suna gangaro masa, matar daya fifita fiye da kowace ta aiko masa ɓarayi? Wadda yay burin guduwa da ita suci kuɗin tare, dama abinda ta ƙulla masa kenan shiyyasa ta lallaɓashi subari sai da safe su wuce, tini wutar kan Abba ta ɗauke gaba ɗaya, yaji komai yamasa ɗif, bayajin sautin komai, baya ganin komai sai duhu, daga haka bai sake sanin inda kansa yakeba kuma.************
Washe gari Uncle yahya yasa aka kama hindu, dai bata cancanci cigaba da zama batareda ta fuskanci hukunciba.
Abinda yabata matuƙar tsoro da mamaki shine ko damuwa su kalifa basuyiba, sai Munner ne kawai ke kuka da riƙeta.
Abba kam saida aka kaishi asibiti, dan jininsa yayi ƙololuwar hawa sama.✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Alhamdulillah ALLAH ya sauki Maimuna lafiya gabannin asubahi, sai dai tasha matuƙar wahala abin tausayi, ta haifi babynta Namiji mai kama da Sheikh Aliy masha ALLAH, bayan sun shiga sun dubata tana barci suka fito suka barta.
Rige-rigen ɗaukar jariri akai tsakanin Aliyu da Jiddah, ALLAH yabama Jiddah damar karɓa, shiko ya haɗa da Jiddah n da jaririn duk ya rungume, Jiddah ta ɗago tana kallonsa fuskarta ɗauke da murmushi ta furta,
بَارَكَ اللهُ لَكَ فِي الْمَوْهُوبِ لَكَ، وَشَكَرْتَ الْوَاهِبَ، وَبَلَغَ أَشُدَّهُ، وَرُزِقْتَ بِرَّهُ.
*_Barakal lahu laka fil mawhubi laka, wa shakartal wahiba, wa balagha ashuddahu, wa ruzikta birrahu_*.
_ALLAH Ya yi albarka ga abin da aka azurta ka da shi, kuma Ya sa ka godewa wanda ya baka (shi), kuma Ya sa shi ya rayu har zuwa ga matukar karfinsa, kuma a azurta ka da biyayyarsa._
Aliyu yakuma rungumeta yana amsawa da “Ameen ya rabbi Noorunnisa, nagode sosai, ALLAH ya kawomin kema ta tsatsonki”.
Murmushi kawai tayi tana sumbar goshin yaron, yanda takejin ƙaunar mahaifinsa haka shima takejin tasa ƙaunar.
YOU ARE READING
MUTUM DA DUNIYARSA......
AdventureWannan labari labarine da ya taɓo rayuwar da mafi yawan mata ke fuskanta a wannan rayuwar, tare da rayuwar kishi na gidajen aurenmu, da nuna jarumtar mazan ƙwarai da ke aiki da hankali da ilimi wajen tafiyar da ragamar rayuwar aurensu. Magida...