💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧
(ya dace ya gyara kansa)Bilyn Abdull ce🤙🏻
[9......]
...........Alhamdulillah komai ya kankama Na shirin tafiya taron su Jiddah, Wanda Abba baimasan anayiba, sai Ana gobe tafiyarne Uncle yahaya ya kirashi ya sanar masa.
Masifa yaytayi akan shifa bayason gantali, yagaji da yawon da Jiddah take zuwa Ana fakewa da addini, yarinya balaggiya ce zata tafi har wata uwa duniya Abuja, to bai aminceba.
Banza Uncle yahaya yamasa, daga k'arshema ya yanke wayar, koda yaje gidansu Jiddah da daddare cemusu yay kawai Abban ya amince.
Sosai Jiddah taji dad'i, dan dama gobene tafiyar tasu, duk abinda yadace Uba yayi Uncle yahaya ne yaje makarantarsu yay Mata, (dama idan irin haka ta taso shine ke musu, bama sabi takan Abba).
Tun a Daren ranar suka farajin kewar juna itada su Zarah, kad'an-kad'an saisuce gobe iyanzu kuna Abuja Yaya Jiddah, wlhy zamuyi kewarki”.
Umma da ita kanta takejin babu dad'i tai dariya, “to in banda abinki walida yaune tafara tafiya? Kuma wataranfa gidanma aure duk zaku tafi, baga Nafisa ba kamar bata zaunaba”.
Duk kasa magana sukai, sai hawaye dake zirara a kumatun kowaccensu, duk sanda Umma zatai musu zancen tafiya gidan aure duk saisu shiga damuwa, tunaninsu tayaya xasu rabu da juna? Tayaya zasu barta ita kad'ai?.
Umma ta ta6e baki tana fad'in “Tofa, ta6arar tazo? To kunga bara nayi nan ALLAH ya bamu alkairi”.
Umma ta shige d'aki abunta, tana shiga itama ta share hawayen da suka mak'ale mata cikin ido. (😫aure yak'in Mata).
Suma bayan sun gama shashshare hawayensu suka tashi daga tabarmar suna kaye-kayen tsakar gida kafin su shige d'akinsu. Acan d'inma babu mai magana, jikinsu duk a sanyaye sukai shirin barci, kowacce ta kwanta da tunanin. (🤣zakuyi bayani indai aurene).
Abubuwa da yawa ke saka su Jiddah kuka idan suka tuna zasuyi sure. Na farko rabuwa da juna da kuma Ummansu farin cikinsu. Na biyu wane irin miji zasuci karo dashi? Mai irin halin Abbansu ne kokuwa Wanda yafi nashi muni? Na uku tayaya Ummansu zataji dad'in rayuwa babusu a kusa? Tunda suka tashi sune take gani taji dad'i, k'aunar da take musuce tasakata hak'urin zama da mahaifinsu dukda munin halinsa da rashin k'aunar da yake nuna musu da ita kanta, to ta Yaya bazasu damuba a yayin da suka tuna zasu tafi su barta cikin kad'aici bayan ita ta zauna danta gusar da nasu kad'aicin a lokacin da suke matuk'ar buk'atarta.
Haka kowaccensu taita sak'awa da kwancewa har dare yay nisa, ganin sun kasa barci Jiddah tace su tashi suje suyi alwala suzo suyi salla.
Wannan shawarar sukabi, suka fito domin d'aura alwala, Umma dake sallar itama duk tana jiyo motsinsu. Godiya taima ALLAH daya bata y'ay'a irinsu Jiddah, dama akance Ubangiji baya had'ama bawa zafi biyu, idan ta k'untata wajen mahaifinsu saitaji sauk'i da farinciki a garesu, itako tayaya zata jahilci ni'imar Ubangiji buwayi gagara misali, shima dayake a cikin duhun kai ALLAH ya ganar dashi gaskiya.
★★★★
Washe gari duk sukuku suka tashi, gashi ranar lahadice babu makaranta, haka dai suka taimakawa jiddah ta shirya kayanta kala biyu sai Uniforms d'inta kala buyi suma (tafiyar ta kwana uku ce kacal, ko hud'u).
Bayan sun gama Karin kumallo Uncle yahaya ya iso, dan tare zasu tafi, k'a'idar makarantar su Jiddah ce inhar tafiya irin wannan ta Kama saida muharraminka, basu yarda tafiya iya malamai da d'alibaiba, kowacce zatazo da muharraminta ne aje dashi, sauk'insu ma koda tafiya ta Kama ta k'etare to lallai makwaftan Najeriyane irinsu Cameroon, Niger dadai sauransu, mafi yawanci kuma duk tafiyace ta mota balle ace babu kud'in biyan jirgi.
Har makaranta Zarah da Walida saukai mata rakkiya, sun iske malam mustafa da malam Bilal (kanin M. Aliyu) sai malam mika'il da sauran d'aliban da za'ayi tafiyar suma da y'an rakkiyarsu. Basu wani 6ata lokaciba suka shiga motar da za ayi tafiyar.
Har suka fice su Walida basubar d'agama Jiddah da Uncle yahaya hannuba, itama Jiddah Na d'aga musu, yayinda Uncle yahaya suke k'ara birgeshi da k'arajin k'aunar yaran, dan tarbiyyarsu da zumincinsu Na birgeshi, sosai yayarda da maganar man ta bahaushe dayake cewa mace itace ginshik'in zuminci, dan inhar babu ita saikaga kan y'ay'anka kowanne da inda yayi.
Wannan shine zuwan Jiddah Abuja Na uku, dan haka bata wani damu da 6ata lokaci wajen kallon hanyaba, hasalima ramuwar barci tashigayi, sa6anin abokan tafiyar tata dake hira a hankali, su Uncle yahaya dasu malam mustafa ma hirarsu sukeyi wadda ta danganci rikicin rayuwa da ta'addancin dake faruwa a duniya kullum Ana cewa musulmaine.
YOU ARE READING
MUTUM DA DUNIYARSA......
AdventureWannan labari labarine da ya taɓo rayuwar da mafi yawan mata ke fuskanta a wannan rayuwar, tare da rayuwar kishi na gidajen aurenmu, da nuna jarumtar mazan ƙwarai da ke aiki da hankali da ilimi wajen tafiyar da ragamar rayuwar aurensu. Magida...