💧MUTUM DA DUNIYARSA....!!💧
(ya dace ya gyara kansa)Bilyn Abdull ce🤙🏻
[31➖32]
............Can na hango muku ango Sheikh Aliy shar cikin d'anyar shadda gizna ruwan toka mai haske, sai zabga k'amshi yake yana gaisuwa da jama'a da suketa masa ALLAH ya sanya alkairi, yau d'imma dai baka isa shaida yanayinsa ba tamkar lokacin aurensa da maimuna.
Yazo ya gaida su Abba da gaba d'aya jinsa ya barsa, sama-sama yakejin hayaniyar mutane, koda Aliyu na gaisheshi saida Kalla ya zunguresa sannan ya amsa cikin alamun baya a hayyacinsa.
Shidai Aliyu ya gaidashi cikin mutuntawa tareda masa godiya ya mik'e
Aliyu Na barin wajen Abba ya fisgi hannun Uncle yahya sukai baya inda babu jama'a.
“Yaya wai miya farune kaketa jana? ina zaka kainine?”.
Banza Abba yay masa bai tankaba, kuma bai Saki hannunsaba. Sai da suka Isa can bayan k'aramin d'akin da Gen......take Na masallacin, Sannan ya sakeshi tare hankad'a Uncle yahya jikin bango ya shak'eshi. Da farko Uncle yahya ya tsayane yaga iya gudun ruwan Abba, amma ganinfa da gaske yake saiya shiga k'ok'arin rik'e hannunsa domin kare kansa, amma Sam Abba yak'i sakinsa, sai kuma k'ok'arin shak'arsama yakeyi, tuni kiciniya ta 6arke a tsakaninsu.
Kawu Surajo dayaga fisgar da Abba yayma Uncle yahya ne yaji zuciyarsa takasa nutsuwa, dan haka yabiyo bayansu...
“Subahanallahi, Zakariyya! Kanada hankali kuwa? 'Dan uwan naka zaka kashe? Miyaymaka?”. ‘Kawu Surajo yay maganar yana kiciniyar kwace Uncle yahya daga hannun Abba’.
Uncle yahya ya k'yale Abbane kawai amma badan yafi k'arfinsaba, Abba dai bai Saki Uncle yahya ba saida Kawu Surajo ya maresa, saurin sakin Uncle yahya yay yana kalon Kawu Surajo dake huci (dan shima akwai zuciya dam) hannunsa dafe da kuncinsa yace,
“Kawu shine zaka mareni?”.
“An mareka d'in kozaka Rama? Waishin Zakariyya mikakeson zama kaikam a rayuwarka? A ina ka gado wannan halinne? Wlhy mahaifinka bashida wannan bak'ar halayyar taka, hakama Mahaifiyarku, girma kake kullum amma halin yara da rashin sanin yakamata yakasa barinka, kanason gamawa da duniya lafiya kuwa?”.
Cikin harzuk'owa Abba yace, “Yaza'a dakeni sannan a hanani kuka? Yazaku zauna Ku k'ulla munafuncin aurarmin da yarinya sannan ace bazanyi maganaba?, Jiddah dai nina haifi abata bawani ya haifarminba, wlhy yahya kayi maza ka saka ya sakarmin yarinya, bashi nai niyar bawaba kuma bazan bashiba, inko ba hakaba wlhy saina maka rashin mutuncin dabaka ta6a tunaniba”.
Kawu Surajo zaiyi magana Uncle yahya ya dakatar dashi ta hanyar fad'in kaga “Kawu barshi, nima Zan bashi amsa dai-dai dashi, domin Yaya bai cancsnci kowacce irin girmamawa ba agareni yanzun. Yaya a wannan Karon bazan maka shiruba kamar yanda Na Saba, kaimin dukkan abinda zuciyarka ta fad'a maka dai-dai, sai dai kuma kasani Wannan auren yayi k'ulluwar da insha ALLAHU mutuwace kawai zata rabashi, duk kuma abinda kaga zakamin ga fili gamai doki nan, ko kunyar ALLAH bakaji ka saida yarinya akan kud'i kadawo kana hura hancin y'arkace, dan wannan wlhy saidawane, tunda batasan kaje kaci bashinkaba, k'ilama ko sisi bataci a cikiba.....”
Duka Abba yakaima Uncle yahya amma sai Kawu surajo ya janye Uncle yahyan yana fad'in ”Kaga yahya barsa muje kawai, wannanma kad'ai ta isheshi, yaje ya nemawa masu kud'i kud'insu”.
K'iri-k'iri Abba yashiga mulmulo ashariya yana nakama Uncle yahya da tabbatar masa saiyayi dana sani, kuma aurene saiya rabashi.
Badan wajen babu kowaba kam dasun tara y'an kallo bana wasaba.✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A gida kam Jiddah duk sai tayi wani sukuku, duk tsokanar dasu Aunty Nafisa kemata bata kulaba, dayake ba taro za'ayiba batayi wani kwalliyaba, tadaiyi wanka ta saka sabon d'inkinta. Zaune take a d'akinsu ta zuba tagumi tana tunanin rayuwa, wai itace aka d'aurama Aure sau biyu cikin shekara d'aya, rayuwa kenan, mai tafiya da jarabawa.
Dukda ba taro za'ayiba gidan nasu yad'an cika da makwafta, koda y'an d'aurin aurema suka dawo sai akaita bud'e-bud'e, wad'andama basu shigoma suka shishshigo sunama Umma ALLAH ya sanya alkairi.
YOU ARE READING
MUTUM DA DUNIYARSA......
AdventureWannan labari labarine da ya taɓo rayuwar da mafi yawan mata ke fuskanta a wannan rayuwar, tare da rayuwar kishi na gidajen aurenmu, da nuna jarumtar mazan ƙwarai da ke aiki da hankali da ilimi wajen tafiyar da ragamar rayuwar aurensu. Magida...