chapter 7

55 10 2
                                    

     A daddafe yasamu ya Isa gida ya bude dakinsa kawai ya kwanta. tunani dama yazama abokinsa tun ranar daya fara ganinta a bauci Kuma ya ganta a kano. to wai ta ina zanfarane lallai saina gano wacece nabila ta asali, Kuma wacece ta mutu, lallai kanada aiki a gabanka wani gefe na zuciyarshi kegayamashi haka. Kai jeka kabincika tabbas zakagane minene gaskiyar wannan lamari inji Kuma wata zuciyar.

      ringin din wayarshi yasa yadawo daga duniyar tunanin da yatafi kirana akeyi Amma abun mamaki anboye suna baya iya gane kowanene kekiransa Dan haka yaki dauka yake ganin kowaye toya bude lambar tasa Mana.

     said da akayi Kira sau uku sannan yadaga cikin bacin Rai ,Wai waye haka Dan Allah yake Kira da lamba a boye ?

     Muryar dayaji ita tasa gaba daya ya manta a ina yake,haba my dear Kai dawa Kuma dagani akwai abunda kedamunka? sai dai da farko ina baka hakuri akan rashin haduwarmu a lokacin danacema Abdul ,nasan kaso kaji minene zangayama saigashi bamu haduba to Amma yau ka saurareni zankiraka.

     sai yanzu yayi magana yace yaushe Zaki kirani?

    Uku na dare zankiraka

  kamin yace wani Abu takashe wayarta.

    Besan sanda barci ya daukeshiba daga cikin barcinne yayi mafarki takirashi tanasanar dashi zata dawo gareshi bada jimawaba.

    karar wayarsa tasa ya tashi yakai hannu ya dauka haryanzu dai ba lamba anboyeta.

    Dauka yayi amman yaki magana can ma dayan bangaren ba ace komaiba.

    daga baya yaga shirun yayi yawa yace Wai waye kan layine Kuma yaki magana?

      Hhhh hhhh shine kawai yaji daganan sai wayar tayanke.

    dazaka ganshi da kayi tsammanin duka yaci saboda tayar da hankalinsa   da akayi.

    kayan jikinsa kamar Wanda aka watsama ruwa duk yajike da zufa.

    To wanene wannan mekirana Kuma Yana dariya to Amma nabila tace zatakirani adaidai wannan lokaci to Kuma ai wannan muryar namiji ce bata mace ba.

      kir kir kir alamar Kira yasake shigowa a wayar tasa ,kallon wayar yakeyi Amma yakasa dauka Dan gudun kada yasake Jin muryar data hargitsashi akaci gaba da Kira ba saurarawa daga baya dai yayanke shawarar bari ya dauka yaji koma waye.

     salamu alaikum, yace.

     daga dayan bangaren aka ansa haba Abdul tundazu naketa. Kiranka Amma kaki dagawa Kuma ai kasan nace zankiraka.

    yanzu yafahimci nabila ce takira yanzu, kiyi hakuri barcine ya daukeni shiyasa.

    toshikenan bakomai yawuce.

   Ashe bakiyi bacci ba ?

   Eh banyiba saboda kai.

    saboda ni kikacefa ?

  Ko kana mamakine Abdul ? Kai kahanani barci nakasa runtsawa saboda kai najima inasonka araina ,Amma wata tanason  tashiga tsakaninmu.

   wacece ita Kuma.... kamin yagama tambayarta wayar ta tsinke.

  Da sauri yabi Kiran Amma sai yayi rashin sa'a wayar akashe ,wacece ita ?wacece ke son shiga tsakaninmu? Kai Ina bukatar ansar wannan tambaya to Kuma wazan tambaya?

    a gaskiya kaina ya daure narasa minene gaskiyar magana Wai nabila tace ko wacece wannan shine abunda yakamata in sani.

   Daga nan bacci gagarar shi yayi,  sai ya yanke shawarar raya daren da nafilfili.

     Yana a zaune har aka Kira sallah. Ya tashi yaje masallaci bai dawo gida ba har gari yayi haske.

    Bayan ya dawo ne yasamu ya kwanta bacci yana daukar shi kadan kadan. Da haka har baccin yayi Nisa.

     Sau biyu saudat kanwarshi na zuwa dubashi amma sai taga bacci yake.

   Hankalin mama yaso tashi Saboda Abdul ba kasafai yake baccin safe ba ko yayi ma ba wani me nisa bane.

     Ita kanta ta hango damuwa da tashin hankali tattare dashi amma ba yadda zatayi sai dai ta tayashi da addu'a.

   Tasani zurfin ciki Irin nasa bazai taba bari yafadi mata damuwar Shina.

    A Karshe tace ma saudat ta kyale shi Kar a tashe shi. Ko kila bai jin dadin jikinsane.

     
    Kir kir kir wayarsa tayi Kara da sauri yakai hannu ya dauka dacewa hello.

   Dan Allah kayi hakuri Abdul jiya nace zankiraka Amma bansamu damaba sai yanzu.

     gabanshine yayi wata muguwar faduwa yanzu yagane, jiya ba itace takirashiba🙄?to Amma wacece Kuma takira kanta da nabila? Kai yahakane Wai?

    kayi shiru Abdul bakace komaiba ko dai haryanzu fushi kakeyi Dani?

   a'a wallahi bakomai ya kike ya gida?

    kowa yayi tafiya kaga nikadaice a gida.

    ina sukajene? Ya tambaya

    garimmu da Nisa. Tace mai a takaice.

     Nabila zan iya zuwa in ganki anji....  Kit yaji wayar ta tsinke kafin ya gama maganar shi.

   Kuyi hakuri da wannan kunsan Yan koyo, beside that rubutun kanshi wahala yake yimun Wallahi.  But I will try my possible best Inga nayi improving.

    Duk da nasan wasu har yanzu basu gano kan labarin ba amma Inajin dadin yadda ake kokarin karantawa. Nagode. 🙏🙏

     Kuyi hakuri yanda Zakuga ina dade wa ba update yanayin hidindimu ne Kuma da rashin son rubutu ku rinka bani kwarin gwiwa Saboda shi zaisa in kara dage wa dan ganin na rubuta ko ba yawa

    Kafin in manta,  nasan mafi yawancin mu muna azumi, wasu sunyi Jiya da Yau,  wasu Yau da gobe. Allah ya anshi ibadojinmu ya biya mana bukatun mu na alkhairi.

    Mu rinka sa kasarmu cikin addu'a Saboda rashin tsaro a wasu jihohi Irin su zamfara, katsina da sokoto Allah ya kara mana zaman lafiya me dore wa. Amn

    Anty corona Na nan a rinka wanke hannu. Mind you bada ko wace Irin sanitizer ba dan anyi wata me cutar da mutane.  Sabulu ma idan kasa ya wadatar 😀.

    Allah ya karemu baki daya, yayi mana Nesa da wannan annoba. Amn

  Kar Kumanta

Vote,
Like
Comment
&
Share
       Nagode.
   

NABILAWhere stories live. Discover now