chapter 11

24 6 2
                                    

   Tsayawa fadi maku tashin hankalin da Abdul ya shiga bata lokacine.

     Da kyar ya iya daga kafarshi dan komawa cikin shagon amma wata Irin zuface ke wanke duk wani gaba na jikinshi

     Kan kace me, sai dai ganin Abdul nayi akasa ya suma.

       Yana cikin wannan yanayin NE wata mata tazo sayayya dan sun dan Saba.

       Ganinshi a kwance yasa ta kwalla ihu dan neman agajin Yan kasuwar.

      Nan fah aka cika shagon ana tunanin wane agajin gaggawa za'a bashi.

      Meshagon kusa dashine ya samo ruwa ya watsa mashi amma shiru Abdul be farfado ba.

        Ana hakane wani yace a kaishi asibiti.

    Nan fah suka daukeshi zuwa wani asibiti dake kusa da kasuwar sannan aka samu wani yaje yasanar da ummanshi abunda ke faruwa.

       Ba karamin tashi hankalin umma yayiba. Ba shiri haka tabi bayan Wanda Yazo sanar da ita.

      Hankalinta be kara tashiba sai da taga Abdul a kwance kamar gawa.

     Kuka kam Tasha shi har ta godema Allah.

      Haka Wasa Wasa suka kwashe Sati biyu a asibiti amma Abdul shiru badan lokitoci na cewa yana da raiba da tuni sun fara rage jimamin rashin shi.

       Ranar umma Na zaune saudat ta dawo daga gida dan ita ke masu girki wani Likita ya shigo duba Abdul.

     Bayan yan gwaje gwajen su na likitoci yasamu guri ya zauna.

     Umma ta kalleshi cikin tashin hankali tace Likita ya mutu ko?

    Ajiyar zuciya Likitan ya sauke sannan yace,  a'a mama be mutuba amma har yanzu bamu samo matsalar Shiba.

    Duk wani gwaji da za'ayi munyi amma gaskiya bamuga wata matsalaba.

    Amma da zaku dauki shawarata da nace ku koma gida ayi na gargajiya ko Allah zesa  a dace.

      Umma taji dadin shawarar likitan dan Itama tayi tunanin hakan amma rashin Wanda ze bata kwarin gwiwa yasa tayi shiru ta zirama sarautar Allah ido.

     Nan take akafara shirye shiryen sallamar su Umma daga asibiti.

      Ba tare da bata Lokaci ba aka sallamesu suka koma gida.

     Nan fah aka shiga fadi Tashin nema masa Magani.

    Kowane me Magani da abunda yake fadi game da ciwon nashi amma har yanzu ba wani sauki saidai duk inda umma taji ance me magani to yanzu fah zataje.

       Yau kusan wata  biyu kenan yana kwance yana fama da firgici da rashin lafiya duk wanda yaganshi zai tausayamasa.

     mahaifiyarsa ma hankalinta a tashe yake tun lokacin da aka kawoshi daga kasuwa gashi ba wanda zaigayama dalilin hakan.

      jin sallamar yasa tadawo da dubanta a kofar gida danganin wanene meshigowa. kawartace hajiya hauwa tsaye tayi tana kallon kawar tata cikin damuwa.

     lafiya naganki tsaye a kofar abdul?  Aminiyar tata ta tambaya dan ta jima bata gari Kuma basu samu sunyi wayaba tunda abun ya faru.

     bata boyemata komaiba harda abunda kabir yagayamata game da nabila.

     karkidamu hajiya akwa wani malamina zankaiki wajensa in allah yayarda zamu samu waraka.

    Haka kuwa akayi, Gari na wayewa suka shirya sai kofar dawanau Dan anan gidan malamin yake.

      malam hashim barde kowa yasanshi a garin kano, yayi suna wajen bayar da Magani kala kala, daga ciki harda na aljanu.

      Duke suke a gabansa bayan sun shigo dashi, sun gaisa da hajiya Hauwau Saboda sun Saba sannan tafadi mashi matsalar dake tafe Dasu.

    malam kaji abunda kefaruwa da wannan yaro.

     shuru yayi sannan yayi yan rubutunsa a wata kasa da yatara a gabansa.

      Bayan nazari na yan Mintuna kansa yatayar ya kallesu daya Bayan daya sannan yadubi abdul inda yake kwance sannan ya gyara zama.

     wato Hajiya hauwa wannan yaro yana tare da wata aljana a jikinsa kuma itace takemasa gizo tana zuwa amatsayin nabila, kuma tasha alwashin kashe duk Wanda yanemi rabata dashi.

      hajiya hauwa in takaice maku labari itace sanadiyar mutuwar tsohuwar budurwarsa nabila, batason ganinsa da kowace mace inba itaba.

     sunanta sarina yar sarkin aljannun kasar masarce, mahaifinta yana ji da ita Sosai bayason abunda ze tabata Shiyasa take abunda taga dama.

        nashiga uku, To malam yazamuyi kenan? inji umman abdul.

    karku damu zansan yadda za ayi, ku koma gida kubani kwana biyu zan nemeku.

    Nan ya hada masu magunguna ya basu kafin kwana biyun kamar yadda yace.

    Ai kuwa washegari sai ga Abdul Jiki ya samu,  yaji sauki ba laifi dan ranar yana iya zama da kanshi murna gurin yan gidan ba'a magana.

      Yau safiya tayi har wajen karfe takwas zuwa tara Amma babu motsin abdul, dasauri mahaifiyar tasa taje dakin danganin halindayake ciki.

    har bandaki taduba amma ba alamarsa hankalinta  a tashe zata fito dakin idonta yakai kan katifarsa wata takarda tagani dasauri taduba tafara karantawa.

     karkusha wahala wajen nemansa dan yana wajena, naji kunce zakuyi maganina kurabani da masoyina banson matsala a tsakaninmu dan kuma mahaifanane, amma zankula dashi karku damu.
                     daga sarina.

Tirkashi!!!
    Ana wata ga wata kenan.
Yanzu dai Sarina ta dauke Abdul, me kuke ganin ze faru?

      Shin zata dawo dashi koko?

Shin da gaske ita ta dauke shinma?

    Shin da gaske nabilar Abdul ta rasu?

  Ku biyoni cikin littafin danjin yadda za'a karke da Sarina.

   Taku
Safara'u sa'ad

Kar manta a rinka following dina Saboda bada shawara ko gyara.

  Nagode

Don't forget to
Vote
Comment
Like
   &
Share.

                Nagode
  

NABILAWhere stories live. Discover now