chapter 14

48 5 4
                                    

      Zaune take a gaban malam ta zayyanamasa duk abunda kefaruwa.

      dama nagayamaku zai dawo, to amma wannan abunda yazo dashi shine bansaniba hajiya.

    to malam yazamuyine Yanzu?

Shiru yayi sannan yafara rubutu a kan wata kasa dayatara a gabansa, yajima yana nazari sannan ya tayardakai yadubi hajiya hauwa.

Yace; hajiya abdul ne yadawo gida sai dai akwai wani abu danakasa ganewa anan wato bayan haske danakeson gani sai duhu yamaye wajen rubutun dan haka akwai katanga data hana infahimci dawace matsala akahadashi da ita dan nasan sarina zata iya haka koma fiye da haka.

      Amma karku damu zanyi iya kokarina Dan ganin nagano kan matsalar.

     To malam mun gode Allah ya kara kaifin basira. Cewar hajiya Hauwau.

    Kinji yadda mukayi dashi hajiya, amma in sha Allah ba wata matsala bace nan da kwana biu zan kara komawa dan jin mekenan.

     Toh hajiya,  Nagode Allah ya bar zumunci yayi ma rayuwa albarka.  Cewar ummah

    
     Azaune suke suna tattauna Matsalar dake damun abdul

    gaskiya mudauki mataki me kyau game da wannan Sarinar kabir saboda bazamusa ido tana abunda taga damabafa.

    gaskiya hakane samir karkadamu akwai inda   zamu dakai gobe in Allah yayarda zamusamu mafita.....

    kamin sukai karshen maganar sai ga wata guguwa tataso ko gabanka baka iya gani tsakaninsu basu ganin junansu wucewarta keda wuya kabir yanemi samir ya rasa sama ko kasa yayi kira amma babu alamarsa.

     Akwance akasameshi a kofar gidansu dagudu sukaje suka sanarda mahaifiyarsu ga yaya kabir can a kwance a kofar gida.

    dagudu taje wajen kansa tana jijjigashi kabir kabir miyasameka kowa nawajen kuka yakeyi dasauri akadaukeshi zuwa asibiti.

    likitane yabasu hoto dazasuyi sukawo danganin abunda kedamunsa.

    hoto har Wanda ba ace suyiba saida sukayi suka kawo masa.

     zaune take a gaban likita tana jiran taji ansar dazaya bata.

Bayan dogon nazari can ya Nisa yace;  hajiya gaskiya babu wani abu dake damun wannan yaron naki dan haka ina baki shawara da kumayar dashi gida ayi maganin hausa ina ganin za'adace.

     A haka aka basu Sallama suka koma gida suka ci gaba da neman magani.

    Abu Wasa Wasa Yau kwana biu ba samir, kabir Kuma ba kanshi. 

    Abubuwa sunbi sunyi MA umman Abdul yawa,  bata gidan su kabir bata gidan su samir duk Dan ta tayasu jaje amma hakan be Hana yan gutsuri tsoma maganganu akai ba.

    Wasuma gani Suke kamar duk laifin ummah NE da take kiransu dan su takmaki yaronta.

      Haka rayuwa taci gaba dayi masu kunci ko ina ba dadi,  Abdul kullum Jiya iyau ba'a gane kanshi.
.
.
.
.
.
.
.

.
.
.
.

       Tasha wahala sosai wajen Neman gidan duk dayake yabata kwatancen gidan kamin su rabu.

    amma haka baihana ta manta da kwatancenba amma daga baya  Allah yasauwake mata wahala dan tagamu da yaron dayasan gidan kuma har kofar gidan yakaita.

    zaune take a gabansa tana rusa kuka kamar idonta zai fita bakomai yasata kukaba sai ganin halin da Abdul yake ciki ya   koma kamar yaro Wanda ake koyama Abu.

     Dakyar ummah wato mahaifiyar Abdul ta shawo kanta sannan ta daina kuka.

    kiyi hakuri haka Allah yaso da bawansa wannan ai jarabawace kuma Allah yabamu ikon cinyewa .

bakomai take tunawaba sai zamanta dashi, sunyi zama Na mutunci tsakanin su

    sun anshi adireshin juna dacewa zasu kaima juna ziyara amma Allah bai nufaba sai yanzu da batayi dacen ganinsa cikin farincikiba.

     kallon juna sukeyi kai dagani kasan akwai aminci a tsakaninsu .

     tabbas yaganeta kallon dayake mata shizai nunamaka cewa yaganeta .

     mahaifiyarsa tayi matukar mamaki dagani yau abdul Ne yake nuna yagane wani......

Hmmm to wacece wannan Kuma?

A ina suka hadu da Abdul?

Mecece alakarta da Abdul?

Menene dalilin zuwanta gurinshi yanzu?

   Taku

Safara'u sa'ad

Karkumanta

Vote
Like
Comment
  &
Share

            Thanks
    

NABILAWhere stories live. Discover now