chapter 8

51 9 1
                                    

             Wanene Abdul
Asalin Yan katsina ne. Alhaji iro shine kakan Abdul, manomine da yayi fice Sosai a harkar noma. Ibrahim (iro)  ya kasance da daya tilo a gurin mahaifiyarshi amma hakan besa ta lalatashi ba.

    Duk da tsangwama ta yan uba amma haka yake nuna masu so bashi Da Wanda yafisu.  Komai yasamu su yake nema Ahaka har yayi aure ya auri cousin dinshi.

     Bayan wani Dan Lokaci Sadiya (matar iro)  Ta haife yarinyar ta son kowa kin Wanda yarasa,  Murna gurin iro ba'a magana haka rayuwa ta dinga tafiya dadi ba dadi Suna tare. Sadiya matace mai hankali da natsuwa ba Wanda zai ce GA aibun ta.

    Tun auren su da iro ba Wanda zai ce ga wani korafi da Sadiya tayi akan mijinta ko da a Fuska ba Wanda zai ce yaga damuwarta.

     Shima kanshi yana yaba Hali Irin Nata Wanda hakan ke kara mashi sonta kullum.

    A kwana a tashi Yau shekara takwas da haihuwar ruma amma Sadiya shiru ba wani cikin ba alamarshi.

  Tun bata damuwa har malam iro ya fara ganin damuwar ta.  Sai dai kullum yana bata baki akan lokacine in yayi zata kara in kuma Shikenan falillahil hamdu.

    Tun dangi na gulma bayanta har aka fara a gabanta wannan Abu ba karamin tayar mata da hankali yakeba.  Saukinta MA mijin ta na sonta Kuma yana kokarin kwantar mata da hankali.

     Shekarar Ruma goma cif Sadiya ta Kuma samun ciki , murna a gurin malam Iro kai kace cikin farine.

    Bayan wata tara, Sadiya ta santalo yaronta sak babanshi Wanda yaci Sunan mahaifin malam Iro wato Hamza.

   Bayan haihuwar Hamza ta wata uku Allah yayi wa malam Iro rasuwa.  Ba karamin Tashin hankali Sadiya ta shigaba haka taci gaba da Kula da yaranta.

     Bayan wani lokaci Yan uwan malam suka sakata gaba akan dukiyar Dan uwansu, dama gonaki sunfi yawa haka ta tattara ta basu Shikenan suka juya masu baya.

    Kullum itace wankau, Surfau, da duk wani abu da zata samu ta rufa MA kanta da yaranta asiri. Ana haka hamza ya fara zuwa makarantar boko cikin rufin asiri da taimakon Yan uwan Sadiya da abokan malam iro har ya gama secondary school. Lokacin ruma tayi aure shikuma karfi ya kawo wasu abubuwan MA shiya dauki nauyin su a gidan Saboda hazaka da kokarin neman na Kai.

    Ana Hakane Allah ya hadashi da wani Mutumin Kano yana zuwa sarin anfanin gona. Allah ya hada jinin su Sosai wata rana ya tambayi ina Sadiya izini ya tafi dashi Kano.

    Haka zaman Hamza ya koma Kano.  Yana taimakama ubangidanshi wurin kasuwancinshi.

   A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah. A haka sai GA hamza da nashi gurin Sana'ar kayan gona ta karbeshi Sosai haka yasa ya dage noma hatsin da kanshi.

   Shekaru suka ja,  Lokaci ya shude  ana haka hamza yayi aure,  ya auri yar wajen ubangidanshi zulaiha.

    Zulaiha mace ce mai hakuri da Sanin Yakamata. Bata da hayaniya koda Yaushe burinta ta farantawa mijinta.

    Bayan shekaru biu da auren su Allah ya azurta su da Yaro Wanda yaci Sunan baban zulaiha  Wato Abdulhamid Wanda Suke cema Abdul Saboda babanta yace kar su boyema yaron sunanshi.

     Bayan Shekaru goma sha biu da haihuwar Abdul zulaiha ta kara haihuwar saudat wadda ba Wanda ya Zaci zulaiha zata kara haihuwa. Tun daga nan haihuwa ta tsaya MA zulaiha.

    Saudat Nada shekaru biyar a duniya Allah yayi ma Hamza da Abdulhamid wato baban zulaiha rasuwa sanadin hadarin mota sunje sayayyar kayan gona.

    A lokacin Abdul nada shekaru sha bakwai kuma ya gama secondary school dinshi ana shirye shiryen sama mashi admission a makarantar gaba.

    Rayuwa tayi masu kunci duk wata walwala tasu sai ta bace. Kullum kowa cikin damuwa balle ma saudat da ta shaku da babanta fiye da Abdul Saboda shi baya zama yana makaranta.

    A haka zulaiha taci gaba da zama da yaran tana kula da yaranta har Abdul yasamu yayi NCE a nan FCE dake Kano.

    Bayan kammala karatunshine aka daukeshi koyarwa a wata makaranta kuntau secondary school dake Kano.

    Ya fara aiki cikin sa'a dan Sosai yasamu karbuwa a gurin manyan makarantar.

    Abdul mutum NE me Gaskiya Da rikon amana, mutum ne mai yawan barkwanci da son mutane ga girmama Na gaba dashi.

    Ana haka ne ya hadu da nabila wata rana ya shiga ajinsu yaganta tana ta zuba surutu Yan aji na dariya. Hakan ba karamin burgeshi yayi ba. To tundaga ranar yake ta bibiyar rayuwarta har Soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu. Sunyi shakuwa mai zurfi har ta kai basa iya kwana basu GA junaba.

    Ansa ranar Bikin su wata biyar kwatsam ranar nabila ta tashi da ciwon ciki.

  Abu Wasa Wasa ciwo yake ta zafi kullum ciwo ba sauki sai a gurin Allah.

    Duk wata natsuwa ta Abdul ta gushe, ba barkwanci ba fara'a kullum kamar Wanda akayima sakon Mutuwa fuskarnan ba annuri.  In ya zauna baya tunanin komai sai nabila ana haka gurin aiki suka bashi hutu dan sunga yana cikin damuwa.

    A haka Abdul ya koma jinyar nabila. Kullum yana gunta bacci kawai ke mayar dashi gida.

    Ranar wata alkhamis, zai tafi gida bayan magrib Dan ganin jikin yayi sauki har Suna ta firarsu da ita.  Yayi Sallama da kowa ta rakashi har kofar gida ya tafi.

     Ya dawo daga masallaci da asuba yaga Hafiz yayanta a kofar gida. Gabanshi NE yayi wani mummunan faduwa da kyar suka gaisa yace mashi Allah yayi ma nabila rasuwa da dare.

    Nan take Abdul ya fadi kasa sumamme.  Hankalin Hafiz ba karamin tashi yayi ba sanadiyar haka ya ruga cikin gidan da gudu ya sanarma mama zulaiha halinda ake ciki.

   Bayan wani lokacin Abdul ya farfado a haka akayi zana'izar nabilar dashi.

   Bayan an dawo zazzabi ne me zafi ya rufeshi Wanda ya kwashe Sati uku yanayinshi.

    Daga nan kuma abun ya koma mashi kamar hauka Wanda saida taimakon addu'a Abdul ya dawo normal.

   Mutane sun tausaya mashi Sosai sanadiyar Hakane yasa iyayen nabila kwashe kayansu suka bar garin baki daya.

    Neman duniya Abdul begansu ba haka ya hakura ya cigaba da sabgoginshi.

Take ce dai

Safara'u sa'ad

Comment
Vote
Like
   &
Share
                  Thanks.

  

NABILAWhere stories live. Discover now