chapter three

75 13 2
                                    

     Slm, barkan mu da wannan lokacin.  Yan uwa dan Allah ina so idan anga wani gyara ko nafadi wani abu ba dadai ba a jawo hankalina a yimun gyara kusan tara muke bamu cika goma ba. Nagode.

      Nabila in tambayeki mana?abdul ya fada

   inaji abdul, Tace dashi

  wai dama ku yannan gari ne? Ya tambaya

    eh nan muke mana. Tace a takaice

     to anan gidan kuke dazama ko daga baya kuka dawo nan? Ya kara wata tambayar

   Anan muke babammu da kansa ya gina wannan gidan Tace dashi.  amma miyasa katambayeni ? Ta tambayeshi

    Kawai dai naga ina shigowa nan layin amma bantaba ganinkiba. Ya bata Ansa
Hmm tayi murmushi sannan Tace,  hakane bancika fitowA waje bane.

    ok toni zan wuce, ya fada tare da mikewa.

    tunyanzu abdul? ta ce

    Eh inason zuwa wani wajene shiyasa. Inji Abdul

   to badamuwa, sai kuma yaushe kenan?

    Sai dai nadawo.

     to bani lambarka

   haka yadauki lambarsa ya bata itama tabashi tata lambar. Sukayi bankwana ya tafi

    bezame ko inaba sai gida ya shige dakinsa ya fada kan katifarsa kansa a sama da kaganshi kasan tunani yakeyi ,nifa nakasa gane wannan lamari gaskiya ina cikin damuwa kuma idan nafadama iyayena bayarda zasuyiba dan sunsan nabila ta mutu idan kuma na matsa sai ace na zauce ,amma bakomi zanbi abun ahankali harna gane matsalar.

    yau kusan sati hudu kenan kullun ita kekiransa amman koshi yakira baya samunta yayi korafi akan haka tana gayamasa batada caji. A haka dai har yau shine wata guda da sati daya itake kiransa. Abun na matukar damunsa amma ba yadda zai yi.

   Yau ma kamar kullum, zaune yake yace yau dai bari yakirata ko zata shiga,bugu na farko wayar ta shiga.

    salamu alaikum akace daga dayan bangaren.

     maganar dayaji bata nabila bace, amma hakan behanashi yin tambayaba,

     dan Allah ina nabila me wannan layin?

      Ansa akabashi da cewa kai bakasan aunty nabila ta jima da rassuwaba yau kimanin shekara daya kenan.
   
   Be sake jin komai ba, nan take numfashinsa ya fara sarkewa, Kan Kace haka tuni Abdul ya suma.

     koda yafarka ganinshi yayi kan gadon asibiti.

    koda ya tashi yaganshi da gorar ruwa a daure a hannunsa mamaki yashigayi yaushe yazo nan mikuma yakawoshi asibiti, bude kofar dakin da akayi yasa yaduba me shigowar doctor hajar ce, ita ke kula dashi a asibitin

    harkatashi ,,?  Ta tambayeshi ta kara da, sannu ya jikin naka?

    haryanzu beda ansa dan bemasan abunda yakawoshi nan ba.

    takula yana cikin dan tunani shiyasa tajawo kujera tazauna kusa dashi kakwantar da hankalinka ni sunana doctor hajara, nice mekula da lafiyarka ,inaso inbaka shawara dacewa karage tunani danzai iyasa karasa rayuwarka baki daya ,mike damunka dahar ya jawoma faduwar gaba irin wannan?

   sai yanzu yatuna abunda yake tsammanin shine sanadiyar kawoshi asibiti.

    ita kanta idan ya fadamata ko minene zata daukeshi ya tabu kuma zata sanar da iyayensa halin dayake ciki, wanda bayason susan minene ke damunsa, dama sunnemi susan ko munene ke damunsa amman yaki fadama kowa.

     Dauke take da kayan abinci irin wanda ake kawoma wanda beda lafiya idan anzo dubashi. haryau tare take da karamar yarinyar da yagansu tare kwanan baya.

     sallama me hade da murmushi takeyi a lokaci guda.

    dr hajara ce ta ansa mata tanemi wuri ta zauna kusa dashi tana kallonsa.

     abdul ashe wani abu yafaru haka, ya jikin naka?

   babu abunda zaisa kace abdul ba kurma bane saboda babu wata alama dazata nunama yana magana.

    Abdul bakaji tana magana ? Doctor hajara ta tambayeshi.

    Inaji likita amman sai dai ina so dan allah in tambayeki? dan allah duk abunda ke dakinnan kina ganinsa? Ya fada yana kallon nabila.

    Eh mana abdul. Doctor ta bashi ansa

    to mutum nawa ke dakin nan ? Ya kara tambayar ta.

    Kaga gani gaka sai kuma wannan baiwar allah datashigo yanzu, doctor ta bashi ansa.

     azuciyarsa yake tunani "idan ko tana ganin nabila to lallai nabila ba aljanabace kamar yadda nake tunani"

     amma miyasa kace haka Abdul? tambaya daga inda beyi tunaniba nabila CE ketambayarsa,

      bakomai, yace ba tare da ya Kalle taba

    kai dai ko idanunka nanunamaka wani abu ne abdul, doctor tace dashi

   a'a bakomai, ya fada

    toni zankoma ofishina anjima zandawo indubaka. Ta fice tabarsu.

    dagashi sai nabila da karamar yarinyar akabari a dakin ,kallon kallo akafarayi wanda kenuna akwai wani abu a zuciyarsu da kowake tunani.

     ita takatse shirun dacewa "naje layinkune nakesamun labarin bakada lafiya har ankawoka nan. to wai miyajawoma wannan matsala cikin dan lokaci abdul,,?

    ko ba agayamakaba kasan wannan tambayar tagirgiza abdul, to ta ina zai fara?

    candai ya daure yace "mata sanadiyarki ne.

    saboda ni abdul? Ta fada hankali a tashe. minaimaka ko anhadani dakai ne?
   

      a'a nabila, yace da ita. sai dai nakiraki a waya akasanar dani kin mutu kusan shekara daya kenan.

    tai murmushi tace ba a gayama karyaba abdul.

     Tashin hankali Wanda ba'asa Masa rana.

  To me nabila take nufi da ba'a fadi Masa karya ba
 
   To Da gaske ta Mutun NE ko Kuwa?

    Kudai biyoni Dan jin ya zasu karke

   Taku Har Kullum

               💗💖💖safara'u sa'ad 💖💖💗

Karku manta da

  Like
Comment
      &
  Vote
                         Nagode😘😘

NABILAWhere stories live. Discover now