chapter 10

29 10 7
                                    

    Tundaga ranar Abdul ya tattara duk wani abu game da nabila ya watsar.

    Tun yana tunanin ta wani lokaci har yakai yana kwashe kwanaki be tunata ba saidai duk sanda zebi ta gaban gidan yakanji kamar ya tambaya ko ta dawo

    Kuma tun ranar be kara ganin Maryam ba Kuma be kara tambayar labarin su ba.

    Ko a gida baya maganar nabila balle wani abu daya shafeta.

    Y dukufah kasuwancinshi(saida atampopi a kwari) da koyarwa .

       Yau kusan wata uku kenan da kagansa kasan yana cikin kwanciyar hankali.

     shadda ce a jikinsa fara tas sannan da hula akansa.

    umma ina kwana?

Lfy lau abdul harkafito?  Umma ta tambayeshi

    Eh nafito, kinsan yau za akawo kaya a shago.

gaskiyane natuna. Da fatar dai kaci abinci dan ankaima kana wanka?

   Naci umma.

    To Allah ya kiyaye ya tsareminkai.

      Ameen ameen ummana Nagode Abdul ya fada tareda fita dan Lokaci na wucewa.

      Bayan an sauke kayan, ya shirya su a cikin Shago sai ya wuce masallaci dan lokacin sallar zuhr yayi.

     Zaune yake a shago kansa aduke yana lissafin kayanda akashigo dasu.

   Kamar daga sama sallamarta yaji kawai a kofar shagon, kobe tayardakansaba yasan me wannan muryar.

   dago kansa yayi suka hada ido amma wani abu daya bashi mamaki shine tayi kamar batasanshiba, 
  
     su biyu ne a tsaye bakin kofar shagon, kawartace tace malam dan allah muna neman wata atamface kozamu samu anan?

      Shima dai yiyayi kamar besan taba tunda tanuna batasanshiba se ya mayar da hankalinshi kan kawar yana ansamata tambayar ta

    wace iri ce halan malama?

     Kaganta tasa hannu a jaka ta dauko wani kyalle tanunamasa.

    ai ko kunyi sa'a dan yau aka kawo irin wannan atamfar.

     kai mungodema allah dan munsha yawo wajen nemanta wallahi a kasuwarnan.

    guda nawa kuke bukatane?

     wallahi anko ne na kawata kaganta nan tanuna masa nabila, itace zatayi aure.

dam gabansa yafadi amma bebari sukaganeba, au wannnan ce zatayi auren? Ya tambaya

    Eh wallahi, kagantanan tayi shiru sunanta nabila.

    Yanzu kam alamar tambaya ta fito fili a fuskarsa, nabila ? Ya tambaya

      kanta ta tayar tadubeshi malam ko kasannine? naga kamar kanatunanin kamar kataba ganina ko?

    Tambayar yaji daga sama beyi tsammaniba, a'a kawai dai nafadane. Yabata ansa a taqaice

    munason koda kamar kala ashirin haka ai zamusamu ko?

     Eh zaku samu yanzu za abaku ko sai kundawo?

    Bari mubaka wasu kudi ka Jiye kamin mudawo.

To ba matsala  kawar Tace tana mika masa Kudin.

    bayan tafiyarsu ya dauko wayarsa ya lalubo lambar nabila yasa kira, can aka dauka.

       Dan allah ko nabila tana nan ya tambaya?

NABILAWhere stories live. Discover now