chapter 12

23 10 2
                                    

     Sai ganin ummah akayi a kwance bata ko motsi.

     dagudu saudat tayo kanta, tana fadan mama dan allah kitashi karki barni mama ke kadaice dani dan allah ki Tashi.

     shiru kakeji da sauri saudat Taje tadebo ruwa tadinga watsamata tare da girgizarta, firgigit ta tashi.

    kallon yarinyar tata takeyi cikin tausayawa, kuka tafeshe dashi a gabanta.

     mama kidaina kuka dan allah nima sai kisani Kuka.

    bazakigane bane shiyasa,ana cikin haka hajiya hauwa tafado Gidan.

    lafiya mikefaruwa ne? Shine tambayar da fara masu.

   gabadaya umma ta fada mata abun dake faruwa.

  Ba karamin tashi Hankalinta yayiba amma se ta danne ta fara ba ummah baki.

    karki damu bari inje gun malam nasanar dashi abunda kefaruwa.

Nan hajiya Hauwau ta fice Dan zuwa gurin malam.

    Duke take a gabansa shima yayi shiru na tsawon wani lokaci.

Can ya sauke ajiyar zuciya yace,  karkidamu hajiya yaron ku yana hannun wannan shedaniyar wato sarina amma yana cikin koshin lafiya.

     ai malam mudai adawo dashi yafi.

    zai dawo hajiya zan hadatada bakin aljani wato duna ko bataso zai dauko shi.

    nagode, nagode malam allah yasa adace. A haka hajiya  ta baro malam cike da fatan nasarawa.

    Kinji yadda mukayi dashi hajiya kikwantar da hankalinki, hajiya Hauwau take fadima ummah.

    nagode hajiya hauwa.

Ah Haba, ai kinfi karfin haka a wurina.  Allah dai ya bayyana manashi.

    A haka suka rabu hajiya Hauwau ta koma gida.

    Bata dade da komawa gidaba wayar ta tafara ruri.  Da sauri ta dauka ganin Sunan malam Na yawo a fuskar wayar.

   
    hajiya hauwa kiyi hakuri gaskiya saboda abunnan yafi karfina saboda aljani duna yakasa da sarina, yanzuma tasa anemomatashi a cikin duniya, idan akasameshi kuma zata kulleshine a gidan sarka, Kuma in baki manta ba na fadi maki yar gidan Sarkin aljanu ce
Saboda haka shikuma ya gudu yanzu haka ni Kaina bansan inda yakeba.

     yanzu malam ya za a yi  kenan? Hajiya Hauwau ta tambayeshi.

   kubari zanyi tunani akai, da haka suka gama wayar.

   Abunda malamin ya fada taje ta fadi ma ummah.  Kuka kam ummah tasha shi har ta godema Allah.

    Haka suka zira ma sarautar Allah ido amma ansa anata addu'a masallatai Allah ya bayyana Abdul.

       Yau kusan satin abdul uku a hannun sarina kullun gidan cikin damuwa ake. shin wane hali abdul yake ciki wannan shine damuwarsu.

    Umma ce tasa a Kira mata kabir da samir dan sune abokan Abdul.

     kabir da samir a gaban ummah tana basu bayani game da abdul da rashin sanin halin dayake ciki.

    Bakaramin Tashin hankali suka shiga ba Saboda a labari kawai suka taba jin haka ta faru yau sai Gashi ya faru da dan uwansu aboki Kuma amini. 

      Kabir ne yayi karfin hali yace,  umma bakomai zamuje muga yadda yakamata muyi kiyi hakuri umma.

        nagode maku allah yataimakeku.

     Amn thumma amin umma, suka ansa.

     A haka suka tafi cike da tunanin wannan Al'amarin

    Kabir ne ya fara magana.  Yanzu yakake ganin Zamu bullo MA wannan lamarin.

   Hmmm ai ni tsoron Allah ya kamani kabir, Cewar samir. Wallahi badan ummahce ta fadi mana da bakinta ba da sai ince karyane Saboda a film ko tatsuniya kawai nakejin haka na faruwa.

      Nan dai kabir ya bada shawarar suje makarantar malam musa me almajirai su bada sadaka a dinga yi mashi addu'a har zuwa sanda Allah ze bayyana shi.

    Wannan shawara ita Sukayi anfani da ita kuwa basu tafi gidaba sai da suka dangana da makarantar malam musa.

    Ai kuwa malam ya masu Alkawarin yi mashi addu'a a koda Yaushe.

    A Haka suka koma gida cike da al'ajabin halinda dan uwansu yake ciki.

     Kwance kabir yake a dakinsa jiyakeyi kamar ana kwankwasa kofar dakin nasa  amma daga baya yafahimci ba wasa bane da gaskene, tashi yayi yace waye?

      Jin shiru yasa ya bude kofar da karfi cike da masifa yake cewa wai waye da bazai yi magana... ai be Kai karshen maganaba wata iska me karfi ya daukeshi tayi jifa dashi kan katifarsa daga nan kuma besakejin motsin komaiba.

   Hmmmmm me Kuma ke shirin faruwa da kabir?

    Da gaske NE iskar ce ko Kuma tsabar firgici ne yasa yake imagining Abubuwa?

   Taku
Safara'u sa'ad

   Kar ku manta

Share
Vote
Like
   &
Comment

                       Thanks




NABILAWhere stories live. Discover now