chapter four

82 13 2
                                    

     Duk Wanda ke wajen yasan ko ba afadaba abdul nacikin tashin hankali,musammam idan kaga yadda idanunsa suka fito hili
Kamar zasu zubo.

    wannan tashin hankali wane irine haka yake tambayar kansa.

    Ta lura da bayacikin haiyacinsa a wannan lokaci kujerar dakin ta matso da ita kusa dashi, tana fuskantarsa.

   Tace ,abdul naga katayar da hankalinka kamar kaga wani tashin hankali, ko wannan maganar dana gayama itace matsala abdul? ai tambaya kayimin kuma nabaka ansa daidai da tambayarka, to minene illa a ciki, ko baka fahimceni bane abdul?

    Mikewa tsaye tayi taje wajen tagar dake dakin, hannu tasa ta yaye labulen dakin nan take haske yabaiyana a dakin sannan tajuyo gareshi da murmushi tana kallonsa  ,abdul in tambayeka?

     Eh tambayarni, yace

   kasan fatalwa? tace mashi

       eh nasanta, ya fada

   a'a kadaisan labarinta Dan baka taba ganintaba, Tace dashi

    eh hakane kuma, abdul yace

  idan fatalwa tana tsaye ba aganin inuwarta kasan da haka?ta sake tambaya

   eh nasani, ya fada

    Tai murmushi Tace; inason abdul kadubeni Dakyau kaga zakaga inuwata ko babu daganan zaka fahimci ni fatalwace ko mutun ce sai kayanke hukunci.

    daga sama har kasa yadubeta.     tabbas ga inuwarta nan kowama zai iya gani lallai nabila mutumce ba aljanabace kamar yadda nake tunani.

     kiyi hakuri dama nima ban yarda da maganar mutaneba yace cikin sanyin murya.

    bakomi abdul nizan wuce sai nadawo kakula da kanka. Tace tare dakama hannun yarinyar suka fice daga dakin.

      Kwanansa kusan biyar a asibiti akasallameshi.

    nabila tagayamashi zataje har gida ta karaganinsa sannan zata gaida mahaifiyarsa.

   yayi farin ciki da haka dan yanzune za a fahimci abunda yake fada akancewa yaga nabila yau suma idan taje zasuga abunda yake gani

    Sun aje da ita ranar assabar ranar daba makaranta zataje gidan ,hakan akayi kuwa Dan kuwa nabila tacika alkawari yau gata kofar gidansu abdul har yau dai tare take da yarinyar nan wadda kusan itace abokiyar tafiyarta,da waya tayi kiransa ringing dinner farko ya dauka

   gani a kofargida abdul, Tace masa.

   
     Gaba yake tana biye dashi zuwa cikin gidan. dakin mahaifiyar tasa suka shiga wuri yanunamata ta zauna ,kowa na gida yau kasancewar ba karatu yau.

  mahaifiyar tasace tashigo dakin da fara'arta.

   Abdul ashe har ta iso? Ta tambayeshi

   har kasa nabila tazube tagaida mahaifiyar abdul.

   a'a diyata tashi zauna ya gida ya mahaifiyar taki ?tana lafiya? Unman Abdul ta Jero mata tambayoyin

    tace nagaishe dake, ta bata ansa
 
  ina ansawa kuwa, Ummar ta fadi da dai fara'ar ta.

     Kanwarsa tasa baki a zancen nasu dacewa Yaya abdul itace kakecewa tayi kama da nabila ai ni banga kama anan ba.

    hakane daga dayan bangaren, inji mahaifiyar tasace, nima dai tundazu naso nace haka. Abdul kowa datasa kamar tacigaba da manana.  Amman ai ga hotonta nan a bango ina kama anan?

   kawai dai gizo takemaka a idonka ta karashe maganar da murmushinta Mai sauti

    ita dai murmushi kawai takeyi

     amma a bangarensa mamaki da tashin hankali yakeso ya bayyana garesa ,koda kaine me karatu dole ka girgiza idan kaga abunda abdul ya gani sam bata kama da nabila maganarma tacanza ba irin wadda ya sabajiba.

    amma Yaya abdul muna sonta Dan Allah ka aureta koya kukace mama? Kanwarsa ta Katse masa tunanin.

    ai Dana itace matar yakawo dan kusan juna mudai fatanmu  Allah yasa ayi muna raye.

   kowa ya ansa da amin.

Mama zankoma dama nace zanzo ingaidaku sannan inga yaya jikinsa. Ta fada Tana kokarin tashi

    bakomai diyata ai nagode. Cewar umman Abdul.

    tare sukafito waje dan ya rakata amma yana cikin wasiwasi a zuciyarsa kiranda mahaifiyarsa taimishi shiyamayar dashi cikin gidan.

     gashi kabata wannan kyautace daga gareni. Inji umma

   tagode mama, Yace.

sauri sauri yakeyi dan ya cimmata dan tawuce kofar gidan kiran sunanta da yayi yasa ta juyo wajensa

nashiga uku ya fada tare da dafe kirji, wallahi nabila ce ya fada da karfinshi.

    Dan Dan Dan lallai Abdul na cikin jarabawa.

  Ni kaina Nafara tunanin wai wacece wannan NABILAR?

    Anya kuwa mutum ce?

Kudai ku biyoni Dan jin yadda za'a warware wannan sarkakiyar.

Taku har kullum
  💝💞💞💟safara'u sa'ad 💟💞💞💝

Kardai ku manta da

Like
Comment
    &
Vote
         Nagode🙏🙏

    

NABILAWhere stories live. Discover now