*SILAR HALLACI...*!
*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*
_Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai_
*🅿️2*
Shekara ta dubu biyu da goma Shabiyar
2015*KANO..*
Area:gadan kaya.."Kura masa ido kadai tayi tana kallonsa cikin mamaki da al"ajabi gani take kamar ba Alhajin data sani bane, kamar ba Mijinta ba kuma uban ya"yanta ba gani take Tamkar Shigowar SAMIHA rayuwar Uban ya"yanta ta chanzashi wanchan Alhaji mai Tsausayi jin kai Dattako da Sanin Darajan mutane uwa uba mai nuna Tsabar jin kai ga ya"yan daya Haifa ya kuma yayi Shekaru wajen basu Tarbiya da kulawa da Lafiyansa da kuma aljihunsa.
Hawaye suka kawo mata cikin kwarmin idanuwanta Bata da Zarafin Hanasu Zubowa tana ji kuma tana gani suka fara Sauka Bisa Fuskarta cikin mamaki yake Binta da kallo yana Tsaye atsakiyar wani kayataccen Bedroom wanda yaji gadon Alfarma hade da Shimfidun alfarma,sai wani makeken Wardrope mai kama da alkarya guda sai madubi wanda yake Shake da kayan kwalliya na mata.
Akallon Farko in kayima Nagartattacen Namijin dake Tsaye zaka Fahimci ba yaro bane Duba da,yadda Farin Furfura ya cika kanshi har zuwa Gemunsa hade da Sajensa Dogon Namiji ne mai a kallah Shekaru 70 aduniya Alhaji Bashir wanbai mutum ne nagari mai halin Dattako da girma acikiin Idanuwan mutane yana da Tarin Dukiya ammh kuma Allah bai Azurtashi da samun D'a Namiji ba matarsa Hajiya Rabi tun Auran Saurayi da Budurwa ita ta haifamai Zaratan ya"ya har Guda shida duka mata kuma Suna nan da Da ransu kafin Shekara biyar baya Alhaji Bashir bashi da wata mtsala ammh bayan Shekara biyar data wuce komai ya lalace daga Bangaren Gidansa Tun bayan Shigowar Samiha Rayuwarsa wacce inda ace ya"yansa sunyi Aure da Wuri yayi jika da ita ko ayanzu ma sai dai Suzo Tsara da yarsa ta Hudu wato Nazifa.
Ita kanta Hajiya Rabin ba yarinya bace Domin a kallan Farko zaka Fahimci macece hakima mai Jiki da Tsawo akallah zata bama Shekaru 47 baya yanayin data ke ciki ne na jin dadi suka boye Shekarunta ammh daga ganinta zaka Fahimci ansha miya aduniya.
Ganin yadda Hawaye ke Zubomata ne yasa yace"Rabi meye haka..? Yanzu saboda nace miki zan maida Samiha gombe da zama Shine kikemin kuka kamar wata karamar yarinya..?
Yafada cikin mamaki lokaci daya yana kallonta Cikin Takaichi ta dago ido tana kallonsa kafin ta saka Hannu tana Share Hawayenta Lokaci daya tana Fadin"Ba maidata gombe da zakayi bane ya sakani kuka ba Alhaji ina kukan Tsausayin kaina ne da na ya"yana Saboda yadda yarinya karama ta maida Rayuwarka kamar kwallo Tana garawa Haba Alhaji Duk Tarin Gidajenka dake Birnin kano yarinyar nan duk basu mata ba Sai ta Daukemin kai ka bita waata uwa Duniya..? Wakake dashi agarin Gombe Duka kasuwancinka suna garin nan ne,Duk Fifita tan daka dinga yi akaina akan ya"yanka bai mata ba ka Duba Fadin Girman gidan nan Na tabbata ko mata goma ake Aure zaka aurosu kasasu acikin Gidan nan su zauna wasu basu matsa wasu ba,ammh Kiri kiri yarinyar nan ta zauna agidanan tace bazata iya zama da matarka da ya"yanka ba kamar wata yar gold Haka ka biye mata jikinka na Rawa ka Dauketa ka sata Sabon Gidan da ka gina da sunana ammh ka sakata ciki saboda ta zabeshi shine Ra"ayinta anya Alhaji Yarinyar nan da iyayenta Sun barka haka kuwa..? Bata wanke gabanta ta baka kasha ba..,?
Tafada tana kallonsa cikin Tabbatar da Tunaninta wani kallon Banza ya jefata dashi kafin ya saki Tsaki yana Fadin"Mtswww...gaskiya Rabi kidaina Abunda kikeyi wannan Wata irinmganar banza ce..ina Daukanki mai Hankali Ashe kallon Kitse nake ma Rogo bansani ba..? Na tabbata ko Abida Bazata aikata abunda kike aikatawa ba abun gwanin kunya kina kishi da Sa"ar yarki..Mganar zan maidata gombe Ina Ruwanki Inace dai Samiha matatace kuma tana Hakki akaina Ina sonta kuma na mata alkawarin komai take Bukata agidan Duniyan nan indai bai gagareni ba zan mata shi karki manta bata sona Mahaifinta ya Tursasa mata ta yarda ta Aure kuma take zaune dani duk hakan ba hallaci bane ni kuma saboda ke sai na kasa mata Abunda take so..?yafada lokaci daya yana kallonta a harzuke..
YOU ARE READING
SILAR HALACCI
FantasiAhmed ka manta Wacece ni...? Nice fa masoyiyarka Samiha..? ka manta alƙawarinmu...? Ka manta yadda muka tashi muna gina yadda rayuwar Aurenmu zata kasance..? amma yau rana ɗaya saboda wani dalilinka mara tushe ballantana makama kakeso kaƙi amfani da...