*SILAR HALLACI...*!
*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*
_Follow us on Wattpad:Janafnancy13 Or Aisha Alto alto_
*🅿️13*
"Ranar Monday tun Safe Abida Tagama Shirinta na zuwa Asibiti,bayan ta gama Taimakama Ahmed ya Shirya cikin Wani Farin yadi shara shara Wanda har farar vest din Jikinsa ana gani Aikin Jikin kayan baki ne Hakama Hulan kansa baka ce Agogon hannunsa baki ne na Fatar damisa haka Rufaffen Takalmin kafansa baki ne kallo Daya zaka ma Ahmed ka Fahimci yana cikin Walwalarsa ayau din sakamakon yana ji ajikinsa ya kawo karshen matsalansa da Samiha Tun Ranar dayayi mata kaca kaca bayan ya Daukota Daga Filin Jirgi bata kara Kiranshi ba,shiyasa sai Hankalinsa ya kwanta har yafara maida dan wuyan dayayi.
Tea da Buredi da Soyayyan Doya da kwai suka karya Dashi,Ahmed ke tsaye atsakiyar falon yana Jiran Fitowar Abida saboda shi zai kaita Asibitin kafin ya wuce office dinsa,Agogon Fatan dake hannunsa yake Kallo har 8 ta gota ammh Abida na ciki taki Fitowa Daga komawa Dauko Waya data manto ta aciki Kaka ta Fito Daga Dakinta tana Kokarin gyara Daurin zanin Atamfar dake Jikinta Ta kalli Ahmed tana Fadin"Kai kuma lafiyanka kuwa kayi tsaye kikam kamar wani Soja ko Dan sanda..?
Tafada tana Kokarin zama Bisa Daya Daga cikin Kujerun Falon,Ahmed ya kalli Kaka yana Fadin"Kaka ina kwana..? Yanzu nake Shirin na shiga mu gaisa kafin na wuce wajen aiki.."Tabe baki Kaka Tayi tana Fadin"Bawani nan Ahmadu nida kake gaba dani acikin Gidanan..!? Ido ya zaro yana kallon Kaka kafin yace"Ni Kaka gaba fa kikace..? Wani irin Gaba kuma ana Zaune kalau Hajiya Kaka..?
Baki ta Mele kafin tace'Eh koma wace iri ce kafini sani karyan Iskanci kakeyi Ahmadu ina gidanan ammh yaushe Rabon da kamin mgana ko Shigowa kayi na maka Mgana banza Dani kake Cikin Raina dai nace Oho dai Bani ka yi ma Banza ba Sama"ila kamawa ko Uwarka Zaliha.."Baki Ahmed ya kama kafin yace"Oh my God Tsakani ga Allah Kaka kina da matsala gagaruma wlh.."Yafada yana kallonta cikin Dan Tsuke Fuska Lokaci Daya kuma yana kara Duba agogonsa kafin ya waiga yana Kiran Sunan Abida.."Sweetheart kina ina ne..? Kiyi Sauri Allah na makara.."Daga cikin Daki Abida ta amsa tana Fitowa"Gani nan Hubby Marata ce ta Daure na Shiga Tiolet.."Tafada Daidai Lokacin data Fito tana gyara zaman mayafin dake kanta Kaka na Zaune tana kallonsu Kafin ta Daga Murya tana Fadin"Nice keda Gagaruman mtsala ko Ahmadu..?
Nunfashi ya sauke kafin ya waigo yana Kallon Kaka cikin Tsukewar Gira yace"Eh wlh Kaka..Haka kurum in ba mtsala ba kiyi ta faman Kiran sunan iyayena Alhalin kina sane sun rigamu gidan gaskiya Abun fa na kona min Rai bana nuna miki ne kawai.."Karamin Tsaki Kaka taja kafin tace"Nice gidan Haya ko Tsohuwar Mota karewar mtsala kenan kaji ko.."Tafada tana wani Gyara baki cikin alamun tana cike da Ahmed din ko kara kallonta baiyi ba ya yi gaba yana Fadin"Muje kawai.."Abida tabi bayanshi tana Fadin"Kaka mun tafi sai na Dawo...".
Galala Kaka tayi tana kallonsu kafin ta yunkura ta mike tana Fadin"Kai kai...Ku tsaya nan nace bangane muku bane..Ina zaku je ne dukkanku haka da Sassafe..?
Abida ce ta tsaya Ahmed Shi Har ya Fice Cikin Haushin kaka,Abida ce ta tsaya tana Fadin"La Kaka kin Manta jiya na gaya miki yau zan Fara zuwa awo..? kaka bata saki Fuska ba tace"Eh anyi haka.."Abida tacigaba da Fadin"Toh Shine Hubby zai kai ni kafin ya wuce wajen aikin Allahbarshi in nagama Abunda zanyi sai na hawo Napep na dawo gida Kaka.."
Wani irin Kallo Kaka ta Wurgama Abida kafin tace"Lalle kun isa daga ke har Mara mutumcin Mijinki Ahmadu..Wato zaku fice Abunku ga Yar aiki ko megadi da kuka bari ta muku gadin gida ko..? Abida ta sanyaya Murya tana Fadin"Ba haka bane Kaka ba Dadewa zanyi ba ina zuwa aka bude Fayel suka bani Ranar da zan Dawo Allah bazan tsaya ko"ina ba zan dawo gida.."Juyawa kawai Kaka tayi tana Fadin"Ku kuka sani koma Yaushe zaki dawo bai Shafe ne ba ,Nidai Abunda na sani Wlh kafata kafarku ban yarda ku Fice ku barni gadin gida ba Atoh.."Tafada tana Shigewa Dakinta kai kawai Abida ta Dafe Lokacin Daya kuma ga Hon din Ahmed ya isheta da Sauri ta Bude Kofar Falon ta Fice Zuwa Haraban Gidan.
YOU ARE READING
SILAR HALACCI
FantasyAhmed ka manta Wacece ni...? Nice fa masoyiyarka Samiha..? ka manta alƙawarinmu...? Ka manta yadda muka tashi muna gina yadda rayuwar Aurenmu zata kasance..? amma yau rana ɗaya saboda wani dalilinka mara tushe ballantana makama kakeso kaƙi amfani da...