*SILAR HALLACI...*!
*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*
_Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto alto_
*🅿️10*
"Har Ahmed ya koma gida bai da Natsuwa,wuni daya har yayi wani Zuru zuru dashi Haka Abida ta Dinga kallonsa yana zaune kan daya daga cikin kujerun Falon dawowarsa kenan daga masallaci sallar Isha"i shine ya zauna anan ya Zabga tagumi Ta kawomai Daya daga cikin Favourite Food dinshi Wato Dambun shinkafa da Zogale,Ammh Ahmed bai iya ci ba yace ta bari zuwa anjuma Tsuru kawai tayi tana kallonsa cikin mamakinsa Domin Ta wahala wajen yimai Dambun bata jin Dadin Jikinta sai da Kaka ta hanata taki ji Saboda kawai ta Farantamai rai ammh kamar ta Lura Ahned din yana cikin Damuwa ba,duk da bashi da yawan Hayaniya da Surutu barkatai ammh Fuskarsa tana bayyana baya cikin Hayyacinsa Lokacin dayake Zaunen.
Har ta kariso gabansa bai sani ba Ta zauna kusa dashi,ma bai sani ba sai da ta saka Hannu ta Ciremai Tagumin Fuskarsa kana ya Dago a Firgice yana kallonta ganinta yasa ya saki Numfashi sama sama yana Fadin"Sweetheart baki kwanta ba.."? Ya fada yana Riko Duka Hannayenta Lokaci daya kuma yana Shafa hannayen nata,Rau rai tayi da ido kafin tace"Hubby wht Wrong wit u ne..? Nakasa gane kanka daga satin daya gabata zuwa yau..?
Saurin Sakin Fuskarsa yayi yana Fadin"Me kika gani..? Ba komai Sweetheart..? Mirmishi ta saki Lokaci daya ta saki Hannunshi ta kai Saman Fuskarsa tana Shafawa cikin Muryan sanyi tace"A"a Hubby kana cikin damuwa wani abu na Damunka sai dai indai baka san ka gayamin kawai.."ya bude baki zai yi Mgana ta dagamai hannu tana Fadin"Shikenan kawai Hubby tunda bakasan gayamin..Ammh plz ka rage damuwa kada ka samu wata mtsalan kodon saboda ni da Abunda ke cikina.."Tafada idanuwanta sun Tara kwallah Suna Shirin Zubowa,Kafadunta ya Dafa Duka biyun yana kallonta Cikin Muryan damuwa yace"Karki damu kanki Matata...Babu Abunda ke Damuna Kinji ko..? Duk da bata yarda ba ta dagamai kai Hannu ya saka yana Share mata kwallar data Zubomata Lokaci daya yajata Bisa Kirjinsa ya Rumguneta Tsam yana Shafa kanta Zuwa bayanta cikin Alamun Lallashi lafewa tayi tana Sakin Ajiyar Zuciya Shi kuma Idanuwansa ya Runtse yana so yayi yaki Da Tunanin Mganar da Samiha ta bijiromai dashi ammh ya kasa Saboda Tsabar Zullumi da Fargaban wani salo kuma zata Fito Dashi nan gaba.
Cak ya Dauketa suka Shige Bedroom dinsu yayi kokari ya Boye Damuwarsa,Ya dinga tarairayan Abida yana nuna mata Soyayyah awannan Daren Abida ta tabattar da tafi kowacce Mace samun Nagartattacen Miji Irin Ahmed bayan sun samu natsuwa tana Kwance Bisa Kirjinsa tana Sharar barcinta Shikuwa barci ma yaki Zuwa Cikin Idanuwansa Ceilling kawai ya Kurama ido yana Tunanin mafita ammh har gab da asuba yakasa samo mafita tashi yayi ya zame Abida daga kirjinsa ya maidata kan Filo ya fada Tiolet ya Dauro alwala yazo ya fara sallah yana kaima Allah kukansa da kuma Allah ya masa Tsari da Kaidin Samiha,sai da akayi kiran Farko ya Tashi Daga kan Darduma ya Tada Abida shi kuma ya Fice zuwa masallaci bayan ya Shiga Dakin Kaka ya tarar da tana Raka"atanul Fijir sai ya kadai kai ya Fita zuwa masallaci Gefe na Zuciyarsa ya samu Natsuwa Sosai.
Saboda ya farantama Abida rai da Safe yasa ta Lumamamai Dambun Datayimai jiya yayi Breafast dashi ta Soyamai Doya da kwai da Ruwan Citta ya Hada dashi bai Fita da Wuri ba sai da ya jira Abida da kaka ya Daukesu ya kaisu gidan Umma gadon kaya yace in sun tashi Direba ya kaisu gidan kawu maude in yatashi aiki zai biya ya Daukosu Kaka sai washe baki take tana Fadin"Allah yayi yau na Fito naga Sararin Waje..Haba ace kullum mutun da kafarsa ammh sai a dinga killacesa a gida kamar yana kurkuku ina Dalili..".
Tafada bayan Sun gaisa da Umma,Kowa dariya yayi Banda Ahmed yadan kalli Kaka a dage yana Fadin"Allah ko..? Toh daga yau sai kinyi Shekara zaki sake Fita domin nan kano ne bakisan ko"ina ba ba garin jega bane balle kice nan aka haifeki.."Kaka ta Daga murya tana Fadin"Kama isa Ahmadu.? Wlh kayi kadan ko Tsohon Mijina Zakariya bai isa yasamin Dokar fita ba balle kai karan kada miya.."Baki kawai ya Rike yana kallon Kaka Abida da Umma na Dariya bai kara mata mgana yasha kunu yana zaune yana danne dannen waya,zaman ma dayakeyi yana jiran saukowan Abba ne zai kaisa Kasuwar kwari ya duba kayan da aka kawo Shine ma Dalilin Zuwan nashi basu dAde da zuwa ba sai ga Abba ya sauko yana gyara zaman babban Rigan Jikinsa da Sauri Ahmed ya Mike alamun girmamawa Abida ma ta Duka tana gaisheshi ya amsa yana Fadin"A"a Abida tare da ku Ahmed yazo kenan..?
YOU ARE READING
SILAR HALACCI
FantasyAhmed ka manta Wacece ni...? Nice fa masoyiyarka Samiha..? ka manta alƙawarinmu...? Ka manta yadda muka tashi muna gina yadda rayuwar Aurenmu zata kasance..? amma yau rana ɗaya saboda wani dalilinka mara tushe ballantana makama kakeso kaƙi amfani da...