11

30 3 2
                                    

*SILAR  HALLACI...*!

*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*

_Follow us on Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto alto_

        *🅿️11*

   Ahmed kwana yayi bai yi barci ba,a wannan daren yana ta juye juyen neman mafita, domin tsakani har ga Allah yana tsoron kaidin Samiha saboda ya lura kuma yaga take takenta akansa babu alamar zata ji tsoron aiwatar da duk kuɗirin da tayi niyya akansa, kuma shi ya kasance mai rauni ne ta wani ɓarayin Saboda dai na farko auren Abida yake kuma Abba tamkar mahaifi yake agurinshi, ta ina ne zai fara aikata irin waɗannan abubuwan da Samiha take nema..? har abada tun yana saurayi bai kusanci zina ba sai yanzu daya zama magidanci..? Tsakani har ga Allah Samiha ta kasance first love ɗinsa wacce yaso tun farko, kuma ta kasance mace da take da wani matsugunni mai daraja a cikin zuciyarsa, sannan kuma ita Abida ita matar rufin asirinsa ce saboda dalilinta yayi arzikin da bai san iyaka ba, saboda haka dukkansu suna da wani babban matsayi a zuciyarsa da ba zai iya kwatantawa ba. Samiha dai tuntuni ya cireta a ranshi ganin cewa ta riga tayi masa nisa, bai taɓa tsammanin zai ƙara yin karo da ita a karo na biyu ba. Haka yayi ta juye juye bai yi barci ba, daga ƙarshe ma tashi yayi yaje ya ɗauro alwala yazo yana ta sallah har sai da aka kira sallar Asuba sannan ya tashi Abida ya fita yaje ɗakin Kaka ya tasheta sannan ya fita daga gidan zuwa masallaci. Da safe ma haka ya tashi sukuku duk jikinsa a sanyaye Abida dai tana ta kallonsa cikin damuwa har ta kasa daurewa ta tambayesa tace "Wai Hubby meke damunka ne.?. Ni kwata kwata bana gane kanka a cikin 'ƴan kwanakin nan sai kayi ta abu kamar ba kai ba...? Ni gaskiya bana jin daɗin wannan yanayin da nake ganinka a ciki..." Cikin dauriya da ƙarfin hali ya ɗago yana faɗin "Karki damu kanki babu komai.." Cike da damuwa tace "Toh in baka jin daɗin jikinka ne Hubby ka riƙa kwanciya a gida ka huta mana..? Ai Abba ba zai matsa maka ba tunda dai ma'aikatan nan suna da yawa ba kai kaɗai bane..." Ya ƙaƙaro murmushin ƙarfin hali yana faɗin "Sweetheart ya za'ayi mutum ya zauna a gida...? Sai fa an fita ake nemo abincin karki damu babu komai.." Tace "Toh shikenan.." Ta ɗauki jakarsa ta rakashi har gurin motarsa ya shiga sukayi sallama ya fita ita dai zuciyarta duk bata yarda ba tana ta tunanin toh meke damun Hubby ne haka yayi wani sukuku kamar bashi ba..? Alhalin ta sanshi tsayayyen namiji ne jajirtacce mai dauriya. Haka ya tafi gurin aiki yana fama da wannan tunanin na halin da yake ciki tsakaninsa da Samiha duk da azatonshi ta bar maganar. Nan ko ashe Samiha bata bar maganar ba. Haka yaje Office ya zauna sukuku jkinsa duk a sanyaye har sai zuwa ƙarfe 6pm sannan ya tashi ya cewa masinjanaa ya rufe Office ɗin sai gobe, ba tare da ya shiga wajen ma'aikatan ba ya fice daga wajen ya nufi gida. Koda ya koma gida ma haka yayi ta zama sukuku har Kaka tayi masa magana "Wai Ahmadu meke damunka ne kaketa wani sukuku kamar wanda yayi ƙarya..?" Saboda baya cikin mood mai daɗi yasa bai biyewa Kaka sunyi sa'insan da suka saba ba.

Haka har aka sallami Samiha daga asibiti ta koma gida basu sake Haɗuwa da Abba ba sai dai suyi waya idan wata matsala ta taso, kuma shima bai ƙara gigin cewa zai je gidan ba saboda bayaso su haɗu da ita.

Ita kuma Samiha acan nata ɓangaren sai take tunanin toh wace hanya zata bi saboda ita fa tayi alƙawarin sai ta mallaki Ahmed a karo na biyu, da wannan tunanin ta ɗauki wayar Abba ta kwashe numbern Ahmed ta saka a wayarta.

Ranar Monday Ahmed yana zaune a office ɗinsa shida Baban Iman Nura manager yazo suna lissafi akan wasu kuɗin da za'a ba accounter zai saka a account ɗin Alhaji sanna kuma da magana akan wasu kaya da babu za'a yiwa waɗanda zasu kawo kayan daga Lagos waya zasu kawo sababbin lesuna da atamfofi da babu, sai ga kiran Samiha kasancewar bai da numbernta bai san ko wacece ba kawai baƙuwar number ya gani har sai data kusa yankewa sannan ya ɗauka cikin muryarsa mai cike da izza ya furta "Hello don Allah wake magana...?" Daga can ɓangaren tace "Har zaka iya mantawa da wannan muryar kace dawa kake magana Ahmed...? Toh Samiharka ce.." Ya miƙe a kiɗime jiki na rawa yace "Samiha...?" Shima Baban Iman ya ɗago fuskarsa cike da mamaki yana kallonsa. Ta ƙara maƙale wayar a kunnenta cike da shauki tace "Ƙwarai da gaske. Ka zata na manta da Alƙawarinmu ne..? Ahmed bazaka iya gujemin ba, bazaka taɓa iya gujemin ba na gaya maka, saboda haka ka shiga taitayinka ka fara tunanin mafita, akan taya za'ayi dani da kai za muyi aure kamar yadda muke da buri, saboda yanzu haka ina shirye shiryen nan da kwana uku zan sanar da Alhaji ya bani takardar sakina kona makashi a kotu, kuma ka tabbatar da cewa idan ya sakeni ina gama idda zaka fito a nema maka aurena idan ba haka ba Ahmed zan saka a cikin matsala, wlh Ahmed zan jefaka a cikin matsalar da baka isa ka cire kanka ba..." Jikinsa na rawa yace "Haba Samiha me kike nema dani ne..? Ban taɓa zaton haka kika koma ba meyasa bakya jin magana wane irin banzan tunani ne wannan..? Ai ana barin halas ko don kunya haba don Allah..! A harzuƙe tace "Don Allah Ahmed ni ka rufe min baki... Wane halas ɗin zan bari..? Kasan shekara nawa na kwashe acikin ƙunci..? Kasan shekara nawa na kwashe acikin baƙin ciki da damuwa..? Toh in baka sani ba yau zan sanar da kai tunda nayi aure ban taɓa sanin daɗin aure ba, bansan daɗin namiji ba... Ahmed na kwana na wuni na shekara da tunanin son kasancewa da kai... Ahmed kai na ajiyewa kaina daman nayi maka alƙawarin cewa zanbi umarnin mahaifina amma tabbas dama ina nan ina jiranka kuma zaka dawo gareni in mallaka maka abunda yake mallakinka... Haba Ahmed! Nima inaso in kasance a matsayina ta ƴa mace cikakkiya amma har yanzu ban kasance ba, wannan tsohon yazo ya aureni ya cuci rayuwata yana zaune dani shi ba sonshi nakeyi ba amma kasan kai nakeso saboda haka dole ne kazo mu mallaki juna, idan ba haka ba kamar yadda nake sonka zan iya yin komai ciki har da kashe rai. Idan kuma kana ganin wasa nake toh ka zuba ido ka gani..." Cike da matsanancin tashin hankali ya dafe kai yana faɗin "Innalillahi wa'inna illaihirraji'un..." Kafin yayi wata magana tace "Ya kamata nan da kwana uku ka kirani ka gaya min a matsayar da kake, idan ba haka ba zan aiwatar da abun da naga ya min dai-dai..." Tana faɗin haka kawai ta kashe waya. Ahmed ya faɗa kan kujera ragaf nan nan idanunsa suka kaɗa sukayi jajir a hankali yake furta "Hasbunallahu waniimal wakil..." Baban Iman ya kallesa da mamaki yace "Mijin Abida meke faruwa ne Ahmed...?" Ya ɗago yana kallonsa yace "B..a komai.." Yace "Wane irin ba komai..? Wacece ta kiraka wace Samihan ce ta kiraka...?" Ya ɗan sauke numfashi yace "Baban Iman ba komai... Am Abunda nake so da kai kawai kaje gurin accounter ku ƙarashe maganan. Kaina yana ɗan ciwo zanje gida in kwanta..." Ya faɗa lokaci ɗaya yana miƙewa ya ɗauki makullin motarsa ya cewa masinjansa idan Baban Iman ya fito ya rufe masa office din, jiki a sanyaye Baban Iman yabi Ahmed da kallo a ransa yana tunanin idan fa bai manta ba Ahmed kwana biyun nan gaba ɗaya duk ya canza yayi wani iri kamar bashi ba, shi ko Ahmed yana fita ya shiga motarsa ya fice daga gurin yana tafiya ya rasa inda zaije sai yawata titunan Kano kawai yake yi ya rasa ina zai nufa, zufa sai keto mai take kamar yayi ƙwalla haka yake ji saboda baƙin ciki. Ya Samiha takeso yayi da ransa..? Wane irin rayuwa ne Samiha takeso ta jefasa aciki..? Ya za'ayi ace Samiha tasa Abba ya saketa sannan kuma shi ya fito yace zai aureta...? Da wane ido zai kalli Abida..? Da wane ido zai kalli ƴan uwanta..? Da wane ido zai kalli Umma da Abba...? Haba don Allah! Wannan wane irin wulaƙanci ne da ƙasƙanci taya za'ayi ya tabka wannan abun kunyan, duk hallacin da Abba yayi masa a gidan duniya ya rasa da abunda zai saka masa sai da wannan abun kunyan. Haka yayi ta shawagi akan titi har akayi sallar Magriba sai daya biya masallaci yayi sallah,amma ya kasa komawa gida saboda tambayoyin Abida kawai ya nufi gidan Kawu Maude, shi kansa Kawu Mauden daya gansa sukuku sai daya tambayesa yace "Ahmed ko baka jin daɗi ne..?" Yace "Ni dai lafiyana lau Kawu kawai yanayin aiki ne.." Yace "Toh ka dinga samun hutu..." Ya amsa da "Toh.." Sai da yayi sallar Isha'i a nan gidan Aunty Naja'atu ma tayi tayi ya tsaya yaci abinci yaƙi sannan ya dawo gida.

SILAR HALACCIWhere stories live. Discover now