*SILAR HALLACI...*!
*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*
_Follow us on Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto alto_
*🅿️12*
Har Ahmed yaje Office bai yarda ya buɗe wayarsa ba saboda bayaso Samiha ta sake damunsa. Yaje Office kenan bai daɗe ba ya gama cin abincin daya taho dashi daga gida ya samu kira daga Baban Iman ta wayar office ɗin saboda ya kira wayarsa ya jita a kashe yace masa ya taho Wambai store an kawo kaya yazo ya duba, ya fito a gurguje ya shiga motarsa ya tafi kasuwar Kwari ya ɗauki Baban Iman ɗin acan suka tafi Wambai store dake layin Ganduje, suka je suka duba an kawo kayayyaki suka dudduba abubuwa. Bayan sun duba basu bar gurin ba sai da sukayi sallar Azhar, kafin su rabu da juna sai da suka biya restaurant suka ci abinci daga nan shi Baban Iman ya tsaya a kasuwar Kwari shi kuma Ahmed ya koma Office ɗinsa.
Bayan ya koma ne ya kunna wayarsa yana kunna wayar da Saƙon Samiha ya fara cin karo inda take cewa.
_Ahmed taurin kai zaka nuna min...? Toh shikenan banason inyi maka abunda zaka dawo ka tsaneni daga baya ne, ina so in bika a hankali amma tunda har ka nuna haka muje zuwa..._
Yana ganin text ɗin ya gama karantawa ya zauna akan kujera yana tunanin Wai me yarinyar nan ta maidashi ne..? Ji yadda take walagigi dashi da rayuwarsa..? Amma yasan yadda zaiyi mata, nan take kawai yaji wata jarumta tazo masa zuciyarsa ta dake yayi making ya fara rubuta mata reply da cewa.
_Samiha inaso in baki shawara ko kuma ince magana dake ta ƙarshe da zanyi karki ƙara kiran numbern wayata kuma karki ƙara turo min saƙo. Idan kuma haka ta ƙara faruwa zan saɓa miki, na gaya miki abunda kike nema bazaki taɓa samu ba, ana dole ne! Karki ƙara kirana kuma karki ƙara nemana, Ni dake bamu da wata alaƙa wanda ya wuce alaƙar zumunci.._
Yana gama tura mata daga nan ya goge numbernta ya goge saƙon da tayi masa da wanda ya tura mata.
Ita kuma a dai-dai lokacin da taga saƙon tana zaune akan kujerar madubi ɗaure da tawul ta fito daga wanka kenan tana kwalliya taga saƙon Ahmed ya shigo cikin wayarta. Data buɗe ta karanta sai da taji ƙwalla sun ciko idonta tace Wai yau itace Ahmed ɗinta yake mata wannan wulaƙancin..? Ahmed ɗinta dai wanda ta gama ƙwallafa rai da zuciyarta da komai nata akansa shine yake mata wannan wulaƙancin...? Toh shikenan mu zuba dani da kai Ahmed. Kasancewar dama Abba ba'a gidanta yake ba ranar a gidan Umma yake kawai tana gama kwalliyarta ta shirya cikin wani rantsattsen leshinta mai kyau da tsada wanda aka yiwa ɗinkin riga da siket tayi kyau sosai kamar ka saceta ka gudu ta fito zata tafi Office gurin Ahmed domin taje ta sameshi, saboda ita maganar gaskiya bazata taɓa iya haƙuri ta fita daga harkarsa ba kamar yadda yakeso ba. Ta gama shiryawa kenan ta fito riƙe da makullin motarta a hannu, sai ta samu waya daga Hajiya Hansa'u inda take sanar mata Hajiya Mero bata da lafiya hawan jininta ya tashi har an kwantar da ita a asibiti. Take hankalinta ya tashi nan da nan ta kira wayar Abba ta gaya mai tace tana so yanzu yanzun nan don Allah zata tafi Jega. Yace toh shikenan bari yasa a nema mata flight sai ta tafi, nan da nan yayi waya da wani abokinsa aka neman mata jirgin da zata samu ta hau yayi waya akace masa akwai jirgin da zai tashi zuwa Birnin Kebbi nan direba ya ɗauketa zuwa airport tana zuwa ba daɗewa jirginsu ya tashi suka ɗaga zuwa Kebbi. Daga Kebbi suna sauka a airport ta ɗauki tashan taxi ya kaita Jega, koda taje ta iske Hajiya Mero a Asibiti an kwantar da ita amma jikin da sauƙi. Wannan dalilin yasa bata samu daman zuwa gurin Ahmed ba a wannan rana kamar yadda ta Ƙudurawa a ranta.
Shi kuma Ahmed tunda ya tura mata saƙon nan yaji ta shiru sai yayi tunanin cewa gargaɗin da yayi mata ya shige ta ne har ya ɗan saki jikinsa ya ga har an kwana an wuni Samiha bata ƙara kiransa ba, kuma bai ji wata magana daga gareta ba, kawai shiyasa ya saki jikinsa yake tunanin cewa barazanan da yayi mata na karta ƙara kiransa ƙila taji, kawai sai bai ƙara wannan tunanin ba, saboda haka ya maida komai ba komai ba ya cigaba da harkar rayuwarsa, har ita Abida ma taga ya ɗan saki tana ta jin daɗi.
YOU ARE READING
SILAR HALACCI
FantasyAhmed ka manta Wacece ni...? Nice fa masoyiyarka Samiha..? ka manta alƙawarinmu...? Ka manta yadda muka tashi muna gina yadda rayuwar Aurenmu zata kasance..? amma yau rana ɗaya saboda wani dalilinka mara tushe ballantana makama kakeso kaƙi amfani da...