8

30 1 0
                                    

*SILAR  HALLACI...*!

*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*

_Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto alto_

        *🅿️8*

"Suna Fita ta nufi Hanyar Kichen Cikin Takun ta na Takama Jinsa yana Biye abayanta yasa take wani Taku tamkar wata Wahainiya,Shi kuma yana Biye da ita yana kallonta cikin wani Shauki da Soyayyah sai da suka Shiga Kichen din kana ya Coge daga Bakin Kofar kichen din yana Kallonta,Tasha mur tana ta Faman Hada mai abinci Bisa wani katon Faranti.

Mirmishi ya saki kafin ya karisa Gareta Sai ji kawai tayi ya Rumgumota ta baya Lokaci daya yana Sakarmata Kiss agefen Wuyanta,Ajiyar Zuciya ta Sauke Tana Doramai Kofuna Bisa Farantin bayan ta jeramai Kololin Abincin da kuma Filet da Cokali,Cikin Muryan Shagwaba ya Fara cewa"Nace ayi hakuri ko..? Ko baza"a hakura bane sai angama Horani.."?

Kwace Jikinta tayi ta waigo tana makamai Harara baki ya kama yana Fadin"Mijin kuma yau ake Harara..Babban Mgana.."yafada yana yar Dariya Duka ta d'agamai a Gefen Cinya tana Fadin"Ba cewa kayi na Fita na baka waje kana Bukatar kadaichi ba..? Ko ba Haka kace ba..?tafada tana Zaro mai ido Lokaci daya tana karamai kai mai Duka baya yaja yana Dariya Lokaci daya yana kara Rikota ya Cukwikwiyeta yana Fadin"Afuwa....Bazan kara ba Kinji Abidan Ahmadun kaka.."Dariya ta kwace mata ganin yadda yawani Narkemata kansa ta Dungura tana Fadin"Be carefully.."Tafada a Shagwabe da Sauri yace"I carefully Madam.."Dariya suka Sheke Dashi kafin ta Dauki Tiren Abinci shi kuma ya Bita abaya har Zuwa Cikin Bedroom dinsu,Abincin ma Itake bashi abaki yana Zubamata Shagwaba tana Biyemai Duk domin yaga Abida ta saki Ranta ammh acikin Ransa fargaba damuwa da kuma Tunanin me Haduwarsu da Samiha akaro na Biyu yake Nufi,har zuwa Dare Ahmed bai kara bari Abida takara Fahimtar yana cikin Damuwa ba,Yayi kokarin Boye Fargabansa bai sake Fita ba sai Washegari ta waya kawai yayi ta bada Umarni Sai Baban Iman dayazo gida ya sameshi suka karishe Mgana Duk da Shima yaso yamasa Tambaya kan Samiha ammh ganin bai bashi Fuska bane yasa ya kyaleshi

Shima Ahmed din yaso yayi ma Baban Iman Zencen ammh sai wata Zuciya ta kwabeshi,Domin dai bashi da wani abokin Shawara Tun Tasowarshi daga Kaka sai Kawu maude sai kuma Bayan Aurensa Abida toh ammh yanzu inma zaije musu da mgana yace musu mene..? Yaga samiha amatsayin Amaryan Abba..Ganin baida mafita ne yaso yama Nura manaja mgana ammh kuma sai ya Fasa Duk da dashi ne kadai yake good Time Sosai bayan Alaqan kasuwanci,Tunani yayi Ba amfanin gayama wani gwara yayi addu"an Allah sa haduwarsu ta Zamo alheri ba Sharrinta ba kamar yadda yake Tunani ba.

Ganin har Washegari yaje Office ba wata mgana yasa ya saki Ranshi kuma Sunyi waya da Abba kan kaya da zasu zo Daga Lagos,shiyasa bai kara saka Damuwa ba duk da kasan Ranshi yana Cike da Fargaba idanuwansa Samiha na yanzu Sunfi haka wayewa da Girma da Tasawa kalamanta Suna kokarin Sakashi Fargaba,tattara komai yayi watsar ya Cigaba da Harkan Gabansa...

*****
Tunda ta koma gida ta Kule kanta Cikin Bedroom dinta tana Gunjin kuka mai Cinrai kukan Soyayyah da kauna ta gaskiya wacce Ta  Ahmed Tun tana Cikin Kuruciya,Tayi kuka kamar Ranta zai Fita Daganan sai kanta ya Fara sara mata ta Dauki paracetamol tasha ta koma ta kwanta Har Abba ya Shigo tana kwance tana Barci yayi mamakin ganin yanayin kwanciyarta kamar ba cikin Son Ranta  barcin ya kwasheta ba,gyaramata kwanciya yayi ya Fita Zuwa Falo itakuwa sai bayan La"asar tatashi,Sai da tayi Sallar Azahar kana ta Hada da La"asar,Tunda tatashi ya kasa gane kanta Domin yayi mganan Duniyanan tayi mai banza Sai yayi Tunanin ko Ahmed din ne bai Bata Hakuri ba ya Daga waya zai Kirashi ta Dagamai Hannu tana Fadin"Karka kira kowa a kaina plz...Kaina ne ke Ciwo bana son Hayaniya.."Jin haka yasa Ya Fice ya barta bayan ya gama magiyan tazo suje asibiti tamai banza karshenta ma baya ta juyamai yana Fita taje ta kulle Kofar Bedroom dinta ta Cigaba da kuka Ranar kwana tayi batasama Cikinta komai ba,gashi dama Tana da Ulcer da gari ya waye Taji yunwa ta Fita Zuwa Falo ta kwalama yar aikinta kira tace ta Hadomata Tea,ta hadomata ta kawo mata Kurba Daya Biyu uku ta Shiga Kelaya amai,gashi Abba bashi gidanta gidan Hajiya Rabi yake yan aikin natane Suka Taimakamata ta mike ta koma Dakinta Su kuma Suka Tsabtace wajen,Toilet ta Fada tayi wanka ko Abban bata Kiraba ta Shirya ta Fito Direba yajata zuwa Wani private Hopital Mai suna primiere Hopl,suna zuwa aka bata gado aka Sanyamata Drip da alluran barci saboda ta Galabaita Sai da Ruwan ya kare ne,bayan tatashi ta nemi wayarta ta kira Abba ta Sanar Dashi iya Rudewa ya Rude haka ya bazamo zuwa Asibitin Hankalinsa tashe yana faman Jera mata sannu ita batashi take ba Tunanin yadda zata neman ma kanta mafita kawai take da yarda zata mallaki Mafarkinta.

SILAR HALACCIWhere stories live. Discover now