*SILAR HALLACI...*!
*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*
_Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto alto_
*🅿️3*
Alu venue:Kano
"Da sauri take gudanar da komai Agogon dake manne a bangon Kichen din ta kai Duba karfe Takwas Saura mintina goma kachal cikin Hanzari ta gama juyevSoyayyan Dankalin Turawan da kwai cikin Wata karamar Kula,waje ta fita har tana neman Faduwa Saboda Sauri Cikin kayatattacen Dan madaidaicin Falon Daga gefensa akwai wani Danning din abinci karami wanda iyakarsa Zaman mutane Hudu.
Doguwar mace ce,mai karamin ciki atare da ita tana sanye da Riga da zani na wani Leshi kanta ba Dankwali sai dai wani Vail data Lullube jikinta Dashi da Sauri Take komai har tagama jera Duka kayan Breafsat din saman Dinning din Daidai Lokacin da agogon Falon ya Buga karar Karfe Takwas Daidai.
Kanta ta Dafe Lokaci daya ta kwashi Sauri Sanin Halin Hubby yanzu sai ya shammaceta ta iskeshi yagama Shiryawa kuma yace bazai tsaya ya karyaba Saboda Takwas tayi tana Shirin Nufar hanyar da zata sadata da jerin Dakunan Barcinsu ne Taji Muryan Kaka na Fadin"'Motsin wai waye nake taji ne Tun dazu ana kaf kaf da Abu..waye anan nace..?
Tafada cikin Muryan irin ta Tsufan nan,Ajiyar zuciya Abida ta Sauke kafin ta Dafe kai lokaci Daya tana Juyowa sai da ta kariso Tsakiyar Falon kana tace"Nice kaka..ina kwana ."tafada tana Ramkwafawa Kaka dake Tsaye Taci Riga da zani na Atmafa an guma Daurin nan na yanmatan Jiya sai wani Siririn Glass dake Idanuwanta,Kallo daya zakamata ka Fahimci Jiya ba yau ba,karfinta bai kare ba sai dai shekaru da sukaja domin gabadaya kanta ya cika da Farin Gashi,ammh FatarJikinta akwai Hutu da jin Dadi...
Baki ta washe tana Fadin"A"a Abida ce Ashe...Ina kwana ya shi Lafiyan Ahmadun..? Tafada tana wani kifkifata idanuwa,lokaci daya tana laluban Wajen zama kuma ga idanuwanta tardasu ganin haka sai Abida ta matso kusa ta kamata zuwa kan Daya Daga cikin Kujerun Falon Tana Fadin"Kaka kinga Kujera nan Zauna kada ki Fadi.."Zama kaka tayi tana Fadin"Nagode Abida..Allah shi miki albarka.."Da mirmishi ta amsa da Ameen kafin kaka ta cigaba da Fadin"Ai ni wlh Abida babu Abunda zan ce ma Ahmadu sai Allah ya isar min."tafada harda wani goge Hanci kamar wata yarinya.
Baki Abida ta kama Lokaci daya tana Zaro Ido Duk da ba yau ne na Farko da Kaka tataba Durama Hubby Allah ya isa ba Tun bayan Dawowarsu Daga India inda akayi mata aikin ido Kullum Safe In Ahmed yaje gaisheta sai ta Dankaramai Allah ya isa wai yakaita cikin Nasara jajayen Fata an Hada baki dashi an kwakwule mata idanuwanta masu karfi da kyau irin na bakaken Fata an sakamata na wani Nasaran wanda babu inganci..
Cikin Zolaya Abida ke Fadin"Allah ya isa kuma kaka..? Shi Jikan naki kikema Allah ya isa.."Bata rai kaka tayi kafin tace"Eh Shi jikan nawa yo Ko sama"ila keda rai ya aikata min Abunda maketacin mijin naki ya aikatamin na Mai Allah ya isa ballatana Ahmadu ke bari ma kiji Wani labari da baki taba jinsa ba Ko Tsinema Ahmadu nayi sai ya bi Duniya nice komai nashi ke Abida bari na Takaita miki Labari ko Uwarsa Zaliha bata kaini Wahala da Ahmadu ba,gashi yarintar Kazanta yayi sai fa da girmansa yayi Zaune zaune ya Kirba kashi akwance Lokacin Sama"ila ya Fita kasuwa Nice nan ke wahala dashi kina ganinsa haka nina maidashi ya zama mutum har kika ganshi kika Aura.."Dariya ta kama Abida Sai da tadara ganin Hubby Tsaye Bakin Bedroom dinsu yana Hurgama kaka Harara bai yi mgana ba sai da ya Fito Falon Lokaci daya yana Murza Hula kiran Zanna Bukar Bisa kansa.
Kaka na yar Dariya ta Bude baki tana Fadin"ai in ina baki labarin Tarihin Kuruciyar Ahmadu sai kinsha mamaki.."Cikin Takaichi yace"Don Allah kaka waya tambayeki..? Meyasa wani Lokacin kin cika Fadi ba"a Tambayeki bane .?
yafada yana Saka Hannuwansa cikin Aljihun wandon Farar Shaddan dake jikinsa Kallonsa Abida Tayi cikin Wani Salon ni zaka ma Haka itama Hararan ya jefata dashi yana Tsuke bakinshi.
YOU ARE READING
SILAR HALACCI
FantasyAhmed ka manta Wacece ni...? Nice fa masoyiyarka Samiha..? ka manta alƙawarinmu...? Ka manta yadda muka tashi muna gina yadda rayuwar Aurenmu zata kasance..? amma yau rana ɗaya saboda wani dalilinka mara tushe ballantana makama kakeso kaƙi amfani da...