6

30 1 0
                                    

*SILAR  HALLACI...*!

*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*

_Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto alto_

        *🅿️6*

"Tafiyar Ahmed Makaranta yasa Gabadaya hankalin Samiha ya tashi ta daina Walwala da cin Abinci Sosai ta fara rama bata da aiki sai tunanin Ahmed kafin wani Lokaci duk ta zama wani iri da ita duk bata da kuzari Hajiya mairo na Lura da ita tun tana Daukan Lamarin na Samiha a yarinta har tafara Tsorata da lamarin Samiha da Ahmed din.

Shima a bangaren Ahmed din hakance ta kasance dashi Shima kewar gida gabadaya ta lullubeshi gefe daya kuma ga kewar Samiha wacce taki barin Zuciyarsa gashi bashi da waya a hannunsa balle ya Kirata domin Tuni Samiha ta mallaki wayar hannu mai kyau da Tsari Dole kishiyar naki ya maida hankalinsa a kan karatunsa ammh ba domin ya iya Cire Tunanin samiha acikin Ranshi ba,Kawu maude ne yake Zuwa Dubashi Lokaci bayan lokaci yana iya bakin kokarinsa akansa Domin baya zuwa hannun Rabbana yar miyan ne da kuli kuli da garin Rogo da Sauransu haka zai riko mishi Babu Abunda ya nema ya Rasa na Makaranta sai Abunda ba'a rasa ba Kudin Handout kuwa yawancin Daliban Ajinsu sun Daukemai nauyin haka saboda yana Taimaka musu bangaren karatunsu yana Kokarin koya musu Fiye da yadda Malaman suka koya musu shiyasa kafin a Rufe wannan Hutun Semester Sunan Ahmed Isma"il Jega yagama Tambari cikin Department dinsu dama Zagayen Makarantan Gabadaya.

Hutun Da su Ahmed suka samu na Farko na Sati uku ne,Gashi bai da kudin mota,Dole ya fara isa gidan kawu maude wanda kuma Shima ba kudi ahannunshi shiyasa sai da Ahmed yaci sati daya a gidan kawu maude kana ya bashi kudin mota ya Taho jega Ranar kaka Ta rasa ina zata saka Ahmed saboda murna ta dinga Taba Wuyansa tana fadin ya Rame Sosai Shima din Rumgumeta yayi yana Dariya mai Cike da Farinciki.

Duk da Farincikin dayake ciki na ganin Kaka bai gama cika Murnansa Saboda baiga sanyin idanuwansa ba Samiha kuma shi ba zuwa gidansu yake ba,in ma yaje toh yaje raka samiha gida ne yana ganin yayi kankanta da zuwa Kofar gidansu Samiha wanda yasani cewa tsakaninsa da ita Abu ne mai tazara,har yayi wanka yaci abinci yana Zullumi Da Tunanin samiha duk hiran da kaka takeyimai baya wani Jinta sosai Ganinshi da jinsa gabadaya suna wajen samiha ne,Ganin bashi da mafita bayan sallar la"asar yazo kofar gida ya tsaya yana Tunanin Tabbas Samiha zata wuce Zuwa islamiya ammh kuma har yagaji da zamansa baiga Motar gidansu ta wuce ba haka yagaji ya koma gida,Sai da Shida na yammah tayi ya dawo ya Tsaya Lokacin ne kuma motar gidansu samiha ta Wuce yakurama Motar ido kamar yana ganin Samihan azahiri wanda kuwa bata ciki maimu ne kadai taje islamiyan yau Samiha na gida batajin dadi,ita Maimu din ta ganshi sai ma tabe baki datayi ta kauda kai domin tasan duk damuwan Samiha harda Rashin Ahmed atare da ita tana mamakin yadda Samiha ta fara son wanda bai dace da ita ba,Sai da ta koma gida take fadama Samihan cewa ga Ahmed chan ya Dawo da Farko Samiha ta Zata karyan Maimu ne sai da ta Rantse mata kana ta yarda,tatashi da gudu mayafi a hannu zuwa gidansu Ahmed,wanda Fitowarsa kenan daga masallaci ya Shigo gida yana Tsaye kofar dakin kaka suna Mgana samiha ta fado gidan tana kiran sunan Ahmed shima jin Siririyar muryanta dayayi kewa yasa ya waigo yana kallonta Fuskarsa cike da Annuri Samiha saboda murna ganin Ahmed batasan sadda ta Fada jikinsa ba tana sakin mai kukan Shagwaba Duk da yaji wani iri sanda Samiha ta fada jikinsa nashi bai sa ya Tureta ba sai ma Rike kanta dayayi yana Sakin Mirmishi Salatin kaka kawai sukaji acikin kansu Da sauri Ahmed ya Rabata da jikinsa yana kallon kaka matse kwalla kawai kaka tafarayi tana Fadin Makarantan da Ahmed yaje ba karatu yaje koyowa ba sai iskanci da lalacewa Duniya tazo karshen yaran zamani sun san Rumgumar Namiji su lokacinsu Ko kallon Idon Namiji bama Basayi saboda iyayensu sunce musu ko hada ido da Namiji mace tayi zata samu ciki mai Samiha da Ahmed zasu yi banda Shekema kaka da Dariya itako Haushin Ahmed ne yakamata tana Tunanin baida Hankali Suna fama da kansu ammh zai kara musu Wahala dama Uban samiha na sakin Hannu ne sai ta yarda ya Aureta ammh haka kurum yadda ta Wahala da uwarshi yanzu ma ta dawo tana Wahala da matar da zai aura bazata sabu ba..Samiha kuwa Taki tafiya gida ga Dare yaayi sai da Ahmed ya nuna bacin Ransa kana ta yarda ya Rakata gida Suna tafe kowannensu na gayama Dan"uwansa yadda yayi kewarsa Wannan Hutun Wata irin Soyayyace mai girma da Tafin Burika ta gudana Tsakanin Samiha da Ahmed,wanda har gidansu ta kaishi ya gaida Hajiya mairo tamai karban Mutumci Sosai ammh bawai domin Tana Tunanin Shirmen Samihan zai iya Tabbata ba Domin Dukkansu yarane kanana akwai Tarin kuruciya tare dasu basu gama Sanin Ciwon kansu ba Shiyasa bata fara kokarin Dakatar da Samihan ba Tun farko.

SILAR HALACCIWhere stories live. Discover now